Ina yiwa mai karatu barka da Sallah, da fatan Allah ya maimaita mana ganin na wasu shekarun cikin yalwar arziki da lafiyar jiki da zaman lafiya.
Kusan na jima ina yin rubuce rubuce a kan irin abubuwan da kan faru a lokacin da a ke bukukuwan Sallah, ba zan iya tuna takamaimen lokacin da na fara ba, amma ina iya tuna dalilin da ya sa hankali na ya karkata ga bukukuwan Sallah.
A wadancan shekarun babban dalili shi ne; a duk ranar Sallah karama ko babba matasa kan yi gungu (a wasu garuruwan har su dinka kaya iri daya) su je wuraren da a ke yin wasannin sallah. Wurin wasannin kan hada ‘yan unguwanni daban daban, don haka sabani kalilan ya kan kunna wutar bala’in da zai kai ga kisan rai. An yi haka ya fi a kirga. Kamar a Kaduna wuraren da su ka yi kaurin suna a wancan lokacin kan fadace – fadace har da kisa sun hada da; ‘Gamji Gate’ da ‘Galady’.
Haka kuma a washegarin sallah, gungun matasan na sake ziyartan wadancan wurare, inda da zaran an hadu sai kuma a shiga batun daukar fansa, wanda a nan ma wasu rayukan ne ke salwanta. A hankali, wannan al’adar ta zama babba, a kusan garuruwa da daman gaske da ke Arewacin Nijeriya a na aikata hakan.
Sannan abu na biyu wanda ya biyo baya shi ne; matasa sun fara wayewa daga shiga harkokin daba da kauranci. Wannan kuma ya auku ne har da bunkasar wayewa da kuma yawan mu’amala da kafafen sadarwa. Amma sai na sake fahimtar cewa da a ka daina sare – sare a kungiyance a lokutan bukukuwan sallah, sai kuma wata muguwar al’ada ta bijiro, ita ce ta yin wasa da mota ko mashin a wannan lokaci.
A irin wadannan wasanni da mota ko babur a lokutan bukukuwan sallah a kan samu rahotannin rasuwar rayuka da dama daga jihohi har ma da kauyukan jihohin. Wanda wannan babban abin lura ne da damuwa.
Iyaye su ne ke da kaso mafi tsoka a wurin dakile ire – iren wadannan al’adu a lokutan bukin sallah, babu yadda za a yi gwamnati ta iya magance wannan abu ba tare da iyaye sun fara na su aikin ba.
Idan da a ce kowanne Uba zai tsawatarwa dansa cikin nasiha da lalama tare da yi mishi bayanin irin hadarin da ke cikin shiga zugar masu irin wadannan al’adu da za a samu karancin rahotannin barna. Haka kuma idan iyaye za su rika bibiyan mu’amalolin ‘ya ‘yansu a lokutan wannan shagali na Sallah, shi ma zai bayar da daman su iya dakile yiwuwar afkawar matasa ga irin wannan dabi’a.
Wasu iyayen sun yi kokarin hana ‘ya ‘yansu ga shiga harkokin dabanci da kauranci. Amma yanzu babbar matsalar da ke fuskantar al’umma ta girmi dabanci da kauranci, wanda kuma idan Iyaye ba su dauki matakin gaggawa ba, karshenta su ne za a bari da kukan takaici a kuma haifarwa da al’umma da annoba.
Kamar yadda al’amarin fasadin Luwadi ya zama ruwan dare; a wannan lokutan bukukuwan Sallah masu irin wannan dabi’a ta dabbobi za su fake su yi ta bata kananan yara. Kwanakin baya na ke ce ma wani abokina ya kamata mu yi bincike a kan dalilin da ya sa shaidanu ‘yan luwadi su ke farmakan kananan yara.
Idan a shekarun baya al’amarin luwadi bai shigo kasar hausa sosai ba, toh yanzu kam ya shigo ya mamaye wurare da dama. Kusan kullum sai ka ji labarin an cafke wani dan iskan ya na aikatawa. Abin takaicin shi ne kaso 80 da a ke kamawa, su na aikatawa ne da kananan Yara da kuma Matasa.
Tunda mun fahimci cewa wadanda su ka fi fadawa tarkon ‘yan luwadi su ne ‘yan shekaru 7 zuwa 30. Dole ne iyaye su sa idanu sosai a kan duk wani motsin ‘ya ‘yansu. Ba ko ina ya kamata a kyale Yara su rika zuwa ba. musamman ma ya kamata Iyaye su rage yawan yawace yawacen Yara da sunan ‘Yawon Sallah’.
Wannan zamanin ya zo da masifu da bala’o’i iri iri wadanda dole ne sai kowa ya shiga taitaiyinsa tare da daukar matakan kiyayewa. Ba wai ina nufin kar a bar yara su yi ziyara ba, amma a matsayinka na mahaifi ko mahaifiya ya kamata ne a ce kun san ina ne ‘ya ‘yanku su ka je, idan son samu ne ma, ya zama ku ne za ku kai su wurin ziyarar ta yadda za a samu ladan tare.
Na biyu shi ne, akwai wasu kuma wadanda mutane ne amma dabi’ar tamkar ta dabba. Su kuma wadannan, bata kananan yara mata su ke yi; Kaman ‘yan shekaru 5 zuwa 10. Su kan yi musu dabaru, tare da jan hankalinsu da sunan goron sallah. Saboda haka, a nan ma dole ne Iyaye ya zama sun takaita yawon ‘ya ‘yansu mata, saboda gudun sharrin dabba a rigar mutum.
Na uku shi ne yadda samari da ‘yan mata su ke yin amfani da lokacin sallah a matsayin ranakun da za a aikata zina ce zina ce da masha’a. Iyaye na da karfin ikon hana afkuwar wannan masifa, ta hanyar takaita yawace yawacen su ‘yan matan.
Daga karshe zan so iyaye su fahimci cewa; ko dai su tashi tsaye wurin yiwa ‘ya ‘yansu garkuwa daga wadannan mugaye da shaidanun mutane, ko kuma a yiwa rayukan ‘ya ‘yan nasu katoton tabon da warkewarshi sai an yi zufa. Binciken masana halayyar jama’a da zamantakewa ya tabbatar da cewa, idan a ka fara aikata alfashar luwadi da Yaro ya na wahala ya daina. Idan kuma bai daina ba, dole ne zai bata wasu yaran da ya ke rayuwa da su. Idan Iyaye ba su motsa ba yanzu, sai yaushe? Mu hadu mako mai zuwa!
No comments:
Post a Comment