Monday, 7 September 2015

DAN SANDA ABUN TSORO NE?

Mai karatu a wannan makon zan so in wayar da kawunanmu ne dangane da 'yan sanda da ayyukan su,  za mu ta~o inda ke yiwa duk wani dan qasa na gari qaiqaiyi dangane da aikin dan sanda. Su ma na gari cikin ‘yan sandan za su qaru da fashin baqin.
Kalmar POLICE an samo ta ne daga kalmar POLITIA daga harshen Latin, su ma Latin sun samo POLITIA ne daga harshen GIRKA, domin a asali Girka sun kira Kalmar ne da POLIS.
Kafin a samar da tsarin aikin dan sanda a hukumance a wannan qasar ta mu, da ma can mu na da hanyoyin da kakanninmu su ke bi wurin samar da tsaro, kare rayuka, dukiyoyi da sauransu. Kamar misali a qasar hausa akwai DOGARAI, wadanda su ke aikin masu bayar da kariya ga Sarakuna, kuma su ke gudanar da aikin sintiri a cikin gari. A wancan lokacin SARKIN DOGARAI shi ne ke a matsayin shugaban jami'an tsaro. Cikin ayyukansu sun hada da amsar haraji, lalubowa da kuma horas da mai laifi, hana aukuwar barna da sauransu. 
Haka nan kuma mutanen Masarautar SAYFAWA da su ka rayu KANEM BORNO su ma sun jima da tsarin aikin 'yan sanda a al'adance. TALBA shi ne sunan shugaban 'yan sintiri kuma alqalin alqalai a kotun MAI (sarki). 
A yankin Yarabawa kuwa, yammacin Nijeriya,  sunan jami'an tsaro kafin zuwan turawan mulkin mallaka sun hada da ILARI, EMESE, ko AGUNbEN su ne ke gudanar da duk wasu ayyukan 'yan sanda, ayyukansu sun yi kamanni da na DOGARAI a arewacin Nijeriya. 
Wannan ya nuna mana cewa ashe ba bature mai jan kunne ba ne ya zo ma mutanenmu da aikin dan sanda, ba bature ba ne ya koyar da mu harkar tsaro, da tsaronmu ya zo ya same mu, sai dai ma muguntar gur~ata mana harkar tsaron da ya yi. 
Zan dan ta~o yadda turawan mulkin mallaka su ka qirqiri 'yan sandan zamani, manufofin qirqirarsu da kuma sakamakon da mu ke gani har yau.
Ya na da kyau kowannenmu ya san da cewa jami'an 'yan sanda da mu ke da su a hukumance a Nijeriya, turawan mulkin mallaka ne su ka samar da su. Turawan sun fara ne da gina hukumar mutum 30 a shekarar 1861 a wurin da su ka kira 'LAGOS COLONY' wanda daga bisani wannan tsarin ya kutso yankin hausawa a shekarar 1879. A shekarar 1896 ne a ka qaddamar da jami'an 'yan sandan Legas.
A shekarar 1930 ne a ka samu hadewar jami'an 'yan sanda Arewa da na Kudu a ka samar da hukumar 'yan sanda ta qasa, kuma a ka yi mata hedikwata a Legas. A shekarar 1943 ne kuma  turawan mulkin mallaka na birtaniya su ka rubutawa hukumar kundin tsari.
Na kawo wannan dan taqaitaccen tarihi ne don in yi sharar fagen yadda mai karatu zai fahimci rawar da Turawa su ka taka na samar da 'yan sanda a hukumance, kuma sun yi hakan ne ba wai don kakanninmu su ci moriyar harkar tsaro ba, ba sun yi ba ne don a kare rayuka da dukiyoyin iyayenmu.
Turawan sun kafa hukumar 'yan sanda ne saboda su samarwa kawunansu da tsaro da kariya, haka nan kuma sun kafa su ne don su riqa amfani da qarfinsu wurin danne mutane, ladabtar da wadanda ke yiwa dokokin bature kunnen qashi.
Wannan ya bamu ilmin gano dalilin da ya sa baturen mulkin mallaka ya kafa hukumar 'yan sanda, an kafa su ne su don su kare son rai da muradun mai mulki ko mai iko.
Ko da baturen mulkin mallaka ya ba Nijeriya wani abu wai shi 'yancin kai, sai ya bar wa hukumar da su ka gaje shi gadon hukumar 'yan sanda. 
Shi ya sa masana da dama su na ganin cewa matuqar ana son a ga abun arziki a hukumar 'yan sandan Nijeriya,  to a rushe tsarin da Bature ya assasa. 
dan sanda ya kamata ne ya zama abokin kowa, ya zama mai hankali da natsuwa, ya zama mai sanin ya kamata. A halin yanzu dai akasin haka a ke gani a Nijeriya, a wasu lokutan ma sai ka ji ina ma za a riqa gwajin tabin hankali kafin a dauki mutum aikin tsaro? Saboda yadda ‘yan sanda a Nijeriya su ka dauki  sakar wuta kamar kwankwadan kofin ruwa.
Bai kamata dan sanda ya zama mai girman kai, mugunta, da zafi ga jama'a ba, saboda da kudin al'umma a ke tufatar da su, a ke biyansu albashi, don su zama masu bayar da kariya ta kowacce siffa ga ‘yan qasa, ka ga kenan su hadimai ne ba su zama dodanni ba.
Idan a na son haifar da da mai ido a qoqarin samar da fahimtar juna tsakanin yan sanda da mutanen gari, dole ne a shigo da harkar 'POLICE COMMUNITY RELATIONS', ma'ana gina kyakkyawar alaqa a tsakani. Mu hadu mako mai zuwa
 

No comments:

Post a Comment