Mai karatu wannan makon guzuri na ke dauke da shi gare ka, wanda In Allah ya yarda ka ankare za ka ci ribar zama da duk wani mugu.
Domin shi mugu a kullum zuciyarshi ba ta san komi ba face kanshi, babu ruwanshi da wadanda ke qarqashinsa, bilhasali ma ba ya qaunar ci gabansu don a tsammanin busasshiyar zuciyarsa za su iya yin kafada da kadada da shi, kun ji bahaguwar fikira.
Mutum ne zai ingiza ka wurin aikata wani aiki, wanda har cikin zuciyarshi, tsakaninshi da Allah ya san wannan aikin ba alheri ba ne amma saboda ka cutu zai rintse ido a kan yi maka ingiza mai kantu wuta. Musamman a al’amuran da su ka shafi kasuwanci, cinikayya, miqa amana, qulla aure da sauransu.
Faram-faram cikin fara’a za ka ga mutum ya na tarairayarka, mutumin kirki a fuska amma kuma mamugunci a zuci. A yi ta nan da nan da kai, alhali kuma ba a son duk wani abu da zai alamta nasara ko daukakarka.
Me a ke nufi da mugunta?, za a iya samun fassarori mabambanta dangane da kalmar ‘Mugunta’, amma abin la’akari shi ne ko ta wacce siga ka fassara Kalmar zai kasance ta na alamta wani abu ne mara kyau.
Masana halayyar jama’a su na fassara Kalmar ‘Mugunta’ a matsayin dabi’a wacce ke tattare da rayuwar mutane, dabi’a ce wacce kowanne mutum ya na da ita, sai dai mutum ya na iya magance dabi’ar da wasu dabi’un. Akwai muhawara sosai akan wannan fassarar.
Mugunta ta na farawa ne a hankali sakamakon ‘Son rai’, shi kuwa son rai ya samo asali ne daga fargabar kubucewar iko daga hannu, sannan gazawa ne ga wanda ke aikatawa.
Babban alamin mai son rai shi ne wanda ya ke gabato da buqatunshi gaba-gaba, ko da kuwa akwai wadanda su ka fi shi matsuwa da damuwa.
Sai dai kuma a na iya cewa dabi’ar mugunta na iya samo asali daga yarintar da mutum ya yi. idan a lokacin yarinta, mutum bai samu tarbiyyar da ta dace ba a wurin iyayenshi, lallai dabi’ar mugunta na iya yin tasiri akanshi. Saboda mu’amalolin da zai yi da wasu yaran a waje, za su iya kasancewa masu mugayen dabi’u.
Dadin dadawa kuma, mugunta na iya samo asali daga gidan da a ka samu sabani tsakanin iyaye ‘Broken home’ har ta kai ga aure ya rabu. A irin wannan halin mutum ba zai samu tagomashin tasowa tare da cikakkun Iyaye ba. Idan ya tsammaci mahaifinshi ya cuci mahaifiyarshi ne, shi kenan dabi’ar mugunta ta fara samun muhalli a zuciyarshi.
Wasu mutanen kuma mugaye ne saboda su na so su janyo hankalin al’umma zuwa ga halin da su ke ciki. Irin wadanda a ka yi biris da su ba a nuna musu qauna. Kamar misalin masu shaye shayen kayan maye, idan ba a dauki matakin janyo su a jiki da kwakkwafa su ba, za su yi ta aikata dabi’o’in mugunta don su janyo hankalin al’umma.
Sannan kuma akwai kason wasu mugayen mutane guda biyu; na farko shi ne wanda ke ganin shi ya fi qarfin kowa, akwai kuma wanda ke ganin shi wulaqantacce ne.
Mafi sharrin shi ne mugun da ke ganin ya fi qarfin kowa, kuma mutane duk a qasanshi ya kamata a ce su ke, wannan ya fi zafafawa a mugunta, saboda duk wata hanya da wani zai ci gaba toshe ta ya ke yi, kuma babu abun da ya ke qauna a duniya irin a ce ya danqwafar da wasu a qarqashinsa ya na bautar da su kaman bayi.
Shi kuwa mugun da ke ganin shi wulaqantacce ne ya fi kowa wawanci, saboda shi a ganinshi a komi an barshi baya, zai kasance ya na qasqantar da kanshi kuma ya na jin nauyin yin mu’amala da mutane saboda ya na ganin bai kai ba. Don haka ne sai ya riqa yi wa mutane mugunta, don a tunaninshi sun fi shi.
Sai dai fa babu abun da ya kai maganin mugu sauqi a wannan rayuwa, kawai mutum na buqatar ya san hanyoyin da zai bi ne. Da zaran ka fahimci cewa wani mugu ne, ka yi qoqarin sauya mu’amala da shi, duk abun da za ka aikata kar ka barshi ya yi tsammanin shi ke iko da rayuwarka.
Ba wai ina nufin ka watsar da shi ba ne, a’a, kawai ka yi qoqarin yin mu’amala da shi kamar yadda ka ke yi da sauran mutane, da kanshi za ka ga ya fara canzawa, saboda ya fara fahimtar ka san ciwon kanka, ci gaba da danne ka ba zai yiwu ba.
A kowanne mataki na rayuwa sai ka hadu da mugu. [alibai sun san me na ke nufi da mugu, musamman wadanda su ke haduwa da ‘yan baqin ciki qiri - qiri, wadanda ke bata rai kawai saboda wani ya fi su sakamako mai kyau.
Haka nan ‘yan kasuwa ma sun san mugu, saboda shi ne ke surkule, tsafe tsafe da kauce hanya don kawai ya ga jarin wani ya rushe. Kusan a manyan kasuwanni, sai dai ka yi ta ganin a na ajiyewa mutane Manja da doya a qofar shago, don tsabar mugunta!
A kowacce ma’aikata akwai mugu, a wasu lokutan mugun na nan kwance cikin ma’aikatar wani lokaci kuma ya na bibiyan ayyukan ma’aikatar ne ya na kai tsegumi don a kori wani daga aikin da ya ke cin abinci.
Mugu bai so ya ga a na dariya, bai so ya ga a na walwala, bai so ya ga mutane na zumunci cikin annushuwa. Komi na jin dadin duniya ya fi so su zama na shi. Kuma mugu shi burinshi shi ne kullum mutane su riqa roqonshi da neman taimako a wurinshi. Allah dai wadaran Mugu.
Wani mahaukaci da na sani a unguwarmu, idan ya zo wucewa ka ce ‘Mutum Mugu ne’, caraf za ka ji ya amsa; ‘Ko ya mutu sai an daure shi’. Mu hadu mako mai zuwa
No comments:
Post a Comment