Monday, 7 September 2015

SAUYI A CIKIN AL’UMMA: NAZARIN BUKIN ZAGAYOWAR RANAR HAIHUWA (Birthday)

Kowanne mutum a duniya haifo shi a ka yi, babu wani tarihi da ya riske mu a kan cewa ga wani wanda shi fadowa ya yi daga sama, ba a jariri ba, da girmanshi da wayonshi. Wannan dalili na cewa kowanne mutum haihuwarsa a ka yi a duniya ne ya samar da ranar haihuwa.
            A tsohuwar al’adar Malam Bahaushe, a ranar da a ka haifi mutum ba dole ba ne sai ya zama iyayenshi sun kiyaye kwanan wata da shekara, sai dai a kan yi wani abu mai ban sha’awa shi ne yi wa mutum lakabi da sunan ranar da a ka haife shi.
            Wadanda a ka haifa a ranar Juma’a, a kan kirasu da Danjuma ko Danjummai, mace kuma a kira ta da Jummai ko Juma. Macen da a ka haifa ranar Laraba kuwa sunanta Balaraba, shi namijin Balarabe  ko kuma Bala. Ranar litinin shi ne Dan liti, ranar Talata kuma dan tala.
            Nazarin wadannan sunaye su ma abubuwa ne masu tasiri wanda su na da muhallinsu a ilmin sanin halayyar Jama’a.
            Sauyi a cikin al’umma wani al’amari ne da ya zama wajibi, ba a iya kaucewa sauyi. Ko a na so ko ba a so ya na afkuwa. Kuma wani abun ban sha’awa da sauyi shi ne duk inda mutum ya je a fadin duniyar nan zai shaidi sauyin.
            Haka kuma sauyi kan dauki salon faruwa a cikin karamin lokaci ko kuma lokaci mai tsawo. Wani al’ada na sauyi shi ne idan a ka samu sauyi a wani bangare na al’umma yak an shafi sauran bangarori.
            Misali idan a ka samu sauyi a yanayin auratayya tsakanin mutane, wannan sauyi na iya shafar al’ada, idan sauyin da ya afku a yanayin auratayya ya afku ne ta fuskacin samuwar aure tsakanin kabilu mabambanta ba tare da la’akari da bambanci ba. Za a samu sauyi ne ta yanayin cakuduwar al’adu.
            Wani sauyin mutane ne ke tsara shi yadda zai auku, wani kuma ya na aukuwa ne ba tare da sanin mutane ba. Misali, mutane kan sauya yanayin shigarsu (sanya tufafi) a lokacin da yanayin sanyi ya kankama. Sanyin ke takura mutum ya yi shigan da bai saba da it aba. A wuraren da dusar kankara ke sauka, sai ka ga wannan dusar ta tilasta musu yin wani irin shiga, wanda babu yadda wani a yankin da babu dusar ya yi irinta.
            Cikin sauye sauyen da a ka samu a Nijeriya, mafi tasiri shi ne tasirin al’adar Bature a kasashen da ya mamaye a Afrika. Kamar a Nijeriya, an samu sauye sauye a yanayin zamantakewa; auratayya, buki, aiki (sana’o’i), tsarin abinci, sutura da sauransu.
            Cikin kuskuren da Bature ya tafka a kasashen Afrika shi ne karfa karfan da ya yiwa kakanninmu wurin raba su da al’adunsu, ta hanyar shigo musu da nashi, tare da nuna musu al’adunshi a matsayin mafiya fifiko da dacewa ga rayuwar mutum.
            Su ka fara sanyawa mutane dokokin tara iyali, kayyade haihuwa da auren mace guda daya rak, wai duk a sunan kiyaye bunkasar tattalin arzikin kasa. duk wannan bai kawar da mutanenmu 100% bisa 100% daga al’adunsu ba.
            Amma zuwan zamani, musamman bayyanar al’amarin ‘Globalisation’ dunkulewar duniya wuri guda ya haifar da sauye sauye a al’ummu fiye da tsammani. A yanzu abun da ke faruwa a birnin Ingila, wanda ke zaune a kauyen Neja zai iya kallo kaitsaye, ko dai ta wayar salula ko ta yanar gizo a na’urar kwamfuta ko tashar talabijin.
            Wannan ilmin sanin me ke faruwa a sassa daban daban na duniya ya taimaka wurin samun sauyi a yanayin bukin zagayowar ranar haihuwa. Ta yadda an jima a na kiyaye wacce rana a ka haifi mutum, wanne wata, a wacce shekara.
            Don haka idan shekara ta zagayo, dai dai wannan ranar a cikin watan da a ka haifi mutum, akwai buki na musamman da a ke shiryawa na tunawa da wannan rana ta haihuwa, wasu yaran ma iyayensu ke shirya musu, har zuwa su girma su shiryawa kawunansu.
            Al’adar bukin zagayowar ranar haihuwa, ba a kowacce al’ada ba ne akwai shi. Amma yanzu kuma ya zama a bu mafi wahalan gaske a rasa shi a cikin al’umma, komi kankanta akwai.
            Ya zuwa yanzu ma sauyi ya sake bayyana a yanayin wannan murna na zagayowar ranar haihuwa a Nijeriya. Yadda masu dukiya ke wannan murnar ta bambanta da yadda talakawa ke yi, duk da ya ke talakawan na ta kokarin ko ta halin kaka sai sun kwaikwayi masu kudi, su kuma masu kudin hankoronsu sai sun kwaikwayi turawa.
            A farko farkon bayyanar guguwar sauyin bukin zagayowar ranar haihuwa, yadda a ke taron shi ne a yi alkaki ‘cake’, ‘yan uwa da abokan arziki su taru, a yanka a ci, sannan a yi buki, masu bayar da kyauta ‘gift’ su bayar.
            Wannan al’ada ce ta masu kudi, musamman a Nijeriya, idan su na aikata wani aiki talaka ya fara kwaikwayo, sai su yi kokarin yin kari ko sauya na su don a ga bambanci. Tunda talakawa ma na rufe ido su kwaikwaiyi yanka ‘cake’, sai kuma a ka samu sauyin fara yin babban buki, wanda za a ce ga kalan kayan da a ke so mahalarta su sanya, (misali, bakin wando da jar riga), sannan kuma a kama hayan wani babban otal wanda a can za a yi bukin.
            Wannan sauyi a yanayin bukin zagayowar ranar haihuwa ya sa mata da yawa a yanzu na yin karyar ranar haihuwarsu, wata ma saboda kyaututtukan da samari kan kawo mata, ta kan shirya bukin zagayowar ranar haihuwa sau uku a shekara daya.
            Mafi muhimmanci a yanzu ba wai kiyaye ranar haihuwar ba ne ma kawai, a’a bukin da ke cikin ranar a ke yi mawa, kyautar da za a samu a ke yi mawa, wanda a irin kyaututtukan wata har sabuwar mota fil a ke bata, wata kuma kudade. bukin dai ya zama jari. Toh ku taya ni murna da addu’a, nawa na gaske ne, ni ma ranar haihuwata ta zagayo. Mu hadu mako mai zuwa!
                 

No comments:

Post a Comment