Friday, 18 September 2015

Hadarin Da Ke Cikin Killace Yara

Tabbas rayuwa a tare da mutane wani babban al’amari ne mai muhimmancin gaske ga dan Adam, wannan ba ma ga mutane kadai ba, hatta Birai su na da bukatuwa ga rayuwa tare da ‘yan uwansu a matsayin al’umma.
Binciken ilmi da wasu masana halayyar dan Adam da zamantakewa Harry da Margaret Harlow su ka gudanar a shekarun 1962 da 1977, sun fitar da bayanai masu tasirin gaske dangane tasirin mu’amala a tsakanin dabbobi.
Masanan sun gudanar da binciken ne kamar haka: sun dauki jiriran Birai biyu daga wurin mahaifansu inda su ka kebe su a cikin keji daban daban. A kowanne keji akwai kirkirarrun Birai guda biyu a matsayin iyayen wadannan jarirai, akwai sakago (Biri mara rai) wanda a ka kera shi ta hanyar sanya abun tsotso ‘Feeding bottle’ a jikinshi. Sannan kuma akwai wanda a ka kera shi a ka lullube shi da irin jikin Biri amma babu wannan abin tsotso a jikinsa.
Binciken ya tabbatar da cewa jariran Birai din su kan haye kan kirkirarrun Iyayensu wadanda a ka kirkire su da irin jikin asalin Biri su kwanta har sai yunwa ta ci su, sai su sauko su nufi wurin dayan kirkirarren Birin da ke dauke da abin tsotso su sha idan sun koshi sai su koma saman wancan.
Bayan watanni shida da a ka fitar da wadannan Birai a ka hada su da ‘yan uwansu, sai ya kasance wannan tsawon lokaci da su ka dauka a kebe ya taba su, ta yadda a ko da yaushe sai dai su koma gefe su na kallon yadda sauran Birai ke gudanar da al’amuransu na yau da kullum ba tare da shiga ba. dalili kuwa shi ne wadannan Birai sun yi wayo ne a kebe, ba su samu damar koyon yadda a ke mu’amala da sauran ‘yan uwa Birai ba.
Da wannan dan takaitaccen misali wanda na dora shi a bisa binciken ilmi na ke son tabbatarwa cewa shi Mutum ya fi Biri bukatuwa zuwa ga koyon mu’amalolin yau da gobe.
Al’amarin killace Yara kuwa wani abu ne mai girma, duk da ya ke babu yadda za a yi don kawai a na so a fahimci me zai iya faruwa idan an killace su, sai masana halayyar dan Adam da zamantakewa su debi Jarirai su killace su a matsayin gwaji. Amma daga bincike da a ka gudanar dangane da irin sakacin da iyaye ke yi ko kuma wadanda a ke dauka domin rainon jarirai ke yi, an tattara bayanai sosai dangane da irin hadurrra da ke cikin killace Yaro. Zan yi kokarin kawo misalan binciken da a ka gudanar wadanda a cikinsu akwai darussa da ke nuni da hadurran aikata hakan.
Akwai wata yarinya da a ka haifa a shekarar 1932 mai suna Anna, iyayenta ba aure su ka yi a ka haife ta ba, bilhasali ma mahaifiyarta na da matsalar tabin kwakwalwa, saboda haka tun kafin haihuwarta babu wanda ya damu da ta rayu ko ta mutu. A haka a ka haifi Anna, wacce cikin rashin kulawa da nunawa damuwa a ka killace ta a wani kuryan daki da ke gidan mahaifin uwarta. Mahaifiyarta ta na fita tun da asuba ta tafi gona kuma sai dare ya yi nisa ta ke dawowa. Saboda haka ne Anna ba ta samu kulawa da kauna kamar yadda sauran ‘ya ‘ya ke samu.
Masanin halayyar jama’a da zamantakewa Kingsley Dabis a shekarar 1940 ya yi fashin baki dangane da halin da a ka tsinci Anna a shekarar 1938, kamar haka: (Anna) ba ta iya yin magana kamar yadda dan Adam ke yi, haka nan kuma ba ta iya yin tafiya kamar yadda kowa ke yi, ba ta fahimta don an alamta mata abu da hannu, ba ta iya cin abinci da kanta ko da an ajiye mata abincin a gabanta, sannan ba ta san menene tsafta ko kazanta ba.
Wannan al’amari duk ya faru da Anna ne a cikin shekaru shida a killace. A dai dai wannan lokaci ne a ka sa ka ta a makaranta ta musamman, inda a hankali ta fara koyon yadda a ke tafiya da kafafu biyu, yin magana, da kuma tsaftace kanta. Anna ta na ‘yar shekaru 10 a duniya ta mutu, amma kafin mutuwarta an ruwaito cewa ta koyi yadda a ke bin umurni, yin magana, wanke hannayenta biyu, goge bakinta tare da kokarin taimakon wasu Yaran.
A shekarar 1970 an tsinci wata yarinya ‘yar shekaru 13 mai suna Genie. Ita Genie an tsince ta ne a wani kullallen daki ita kadai tun ta na ‘yar watanni 20 a duniya. Mahaifiyarta ta yi haka ne saboda ba ta son a san ta haihu. Sai ta rika watsawa yarinyar abinci ta tagar dakin. Genie ba ta taba jin sautin dan Adam ba, saboda babu wanda ya taba yi mata magana, haka kuma babu talabijin ko Rediyo a dakin.
Masanan da su ka amshi Genie bayan an tsinto ta sun bayyana ta kaamar haka: a lokacin da a ka kawo ta sam ba ta san wani abu wai shi mu’amala ba. ba ta san ya a ke yin fitsari ko bayan gari ba, ba ta iya cin abinci yadda mutane ke tattaunawa a baki kafin su hadiye ba. ba ta iya rike fitsarinta balle bayan gari. Saboda rashin tauna abincin da ta ke yi a lokacin da a ka tsince ta, girman jikinta da tsawonta bai fi na Yaro mai rabin shekarunta ba.
Da wadannan ‘yan misalai za mu iya fahimtar cewa shi killace Yaro a hana shi mu’amala da mutane babban hadari ne wanda zai jefa yaron cikin sahun wadanda ba su iya mu’amala da mutane ba. kuma wannan rashin iya mu’amala na iya ci gaba da tasiri a rayuwar mutum har zuwa girmanshi, ta yadda za ka ga mutum cikakke amma idan ya kwafso maka wani shirmen sai ka dauka dan firamare ne.
Mu hadu mako mai zuwa

No comments:

Post a Comment