Monday, 7 September 2015

BABBAR MAGANA: Yadda a ke gina dabi’a

Akwai abubuwa da yawan gaske wadanda su ne ke haifar da dabi’a ko su yi tasiri a kan dabi’un jama’a. irin wadannan abubuwa su na da yawan gaske, amma wadanda na ke son na yi tsokaci a kansu, su ne mafiya tasiri kuma wadanda ke kan gaba.
            Ya na da kyau mutane su san cewa babu yadda za a yi a samu wata dabi’a wacce ba za a iya bayanin musabbabinta ba, ko kuma dabi’ar da za a ce babu wasu dalilai da suka tasirantu wurin samuwarta.
            A wurin masana halayyar jama’a da zamantakewa, babu wani abu da ya kai matsugunin al’umma muhimmanci da tasiri. Saboda maganar gaskiya ita ce, duk wanda ya ce shi zai qauracewa zama a cikin al’umma ko qauracewa mu’amala da su, babu makawa zai tsinci kanshi a rayuwar kadaici, wanda daga nan zai fara aikata dabi’un da su ka saba da na mutane.
            Kamar yadda Masani Emile Durkheim (1858 – 1917) ya ke fadi, ‘Society is sui generis’, ma’ana matsugunin al’umma ya na da tasiri da qarfin gaske fiye da qarfin ikon dan Adam.
            Wani qarin haske a nan shi ne; mutum na iya yin tasiri wurin sauya dabi’un wasu mutane, amma a bangare guda kuma wannan mutumin babu yadda za a yi ya iya yin tasiri ga al’umma. Ko da a aikata ayyukan alheri ne, duk dagewarka, sai dai ka iya sauya dabi’ar kaso mai yawa, amma ba zai yiwu ka sauya komi da kowa, tsarin gudanarwa, da kuma cibiyoyi da bangarorin al’umma ba.
            A lokuta da dama mutane na boye haqiqanin dabi’arsu don dai kawai su yi tasiri a zukatan wasu. A iya fahimtar masana halayyar jama’a da zamantakewa, don kawai ka ga mutum ya na yi maka murmushi, hakan ba ya na nufin murmushin qauna ko shauqi ba ne, wannan murmushin na buqatar fassara. Babu kuma yadda za a yi ka samu fassara wannan murmushi har sai ka yi mu’amala da wanda ya ke yi maka murmushin, sannan za ka san haqiqanin dalili.
            Ta na iya yiwuwa me yin murmushin ya na so ne ya assasa wani tubalin abota a tsakaninka da shi, a wata mahangar kuma ta na iya yiwuwa me murmushin ya yi ne saboda ya shaidi fuskarka a wani wuri daban.
            Matakin da za ka dauka bayan baquwar fuska ta yi maka murmushi ne zai samar da mafita ga murmushin. Misali idan bayan ya yi maka murmushi, sai kai ma ka mayar da murmushi, wannan zai isarwa da baqon fuskar saqon cewa ka aminta da murmushin da ya yi maka. Idan kuma mai neman a qulla abota ne, zai samu wata damar da zai gabatar da muradinshi.
            Amma a dai dai lokacin da mutum ya ganka ya yi murmushi, sai ka murtuqe fuska, ko ma da me wannan me murmushin ya zo, zai samu cikas da sacewar gwiwa a yunqurinshi.
            Ya na da kyau mu fahimci cewa a lokuta da dama idan mutum ya yi maka murmushi, ba ya na nufin murmushin farin ciki ba ne, wani murmushin na tashin hankali ne, wani murmushin na masifa ne, wani murmushin na mugunta da qeta ne. don haka fahimtar wanne irin murmushi ne baquwar fuska ta yi mana, dole ne mu natsu, mu fahimci a wanne yanayi ne a ka yi murmushin, shin ya dace da yanayin da za a yi murmushi ko a’a. ya fasalin me murmushin ya ke, shin ya yi kama da masu sakakkiyar fuskar da ta saba yin murmushi?
            Sai na biyu, wurin da mu ke zaune (inda mu ke rayuwa) ya na da muhimmancin gaske ga  dabi’unmu. Akwai wani bincike da wani masani mai suna Anderson ya gudanar a shekarar 1997, wanda bayan ya kammala ne ya fitar da natijar cewa, ‘Yanayin zafi na iya samar da dabi’ar mugunta, fushi, da zafin rai ga mutane’.
            Abin da ya ke nufi shi ne wuraren da ke fama da matsanancin zafi na yanayi, wannan zafin na iya sawa a yi ta samun mutane masu dabi’u masu tsananin gaske.
            Hatta wurin da mu ke zama, muhallinmu ya na taka muhimmiyar rawa a dabi’unmu. Ka kwatanta dabi’ar mutumin da ke kwana a cikin daki, na’urar bayar da iska na sanyaya shi, sannan akwai katifa da matashin kai mai laushi; da kuma mutumin da ke kwana a bakin bola, ruwan kwacami da kwadi na shagalinsu a gefenshi. Za ka samu hatta yanayin yadda wadannan mutane biyu ke tunani ya bambanta, haka kuma za ka ga dabi’unsu sun bambanta sosai. Dole dai shi makusancin bola ya ginu da dabi’ar son doyi, dauda da duk wani nau’insu.
            Na uku, al’adunmu na da muhimmancin gaske a wurin gina dabi’ar dan Adam. Al’adarka a lokuta da dama ke gina ma dabi’ar qin wasu abubuwa, al’ada ke gina ma dabi’ar sanya tufafi nau’I kaza tare da gujewa nau’I kaza. Al’adarka ke gina maka dabi’ar qin aminta da abota da wasu nau’in mutane, tare da aminta da abotar wasu nau’in.
            Daga qarshe, duk da akwai wasu abubuwa da daman gaske wadanda ke gina dabi’ar dan adam, amma zan so na taqaita ga yadda yanayin qirar halitta ke tasiri ga dabi’unmu.
            Allah kan halicci mutane daban daban, wasu a yi su manya da babban jiki, wasu masu fadin qirji, wasu farare, wasu baqaqe. Wasu kyawawa wasu munana. Wasu sirara wasu masu qiba.
            Babban misalin yadda qirar mutum ke tasiri ga dabi’armu shi ne; yadda a wasu yankunan qasar nan a ka samu ginuwar dabi’ar qwallafa rai ga farar mace. Yanayin yadda a ke son farar macen ma har ya baci, wannan ya sanya a ka samu sauyi a dabi’un musamman MATA a yanzu, ta yadda duk baqin mace sai kawai ta gina dabi’ar yin amfani da mai me sauya launin fata.
            Wannan dabi’a ta amfani da me mai sauya launin fata ya ginu ne ya kuma tasirantu a zukatan mata sakamakon mayar da hankali da su ka ga maza su ke yi ga dole sai farar mace. Wannan wauta da rashin tunanin da wasu mazan kan yi dangane da wuce gona da iri wurin son farar mace, ya janyowa al’umma asara me yawan gaske, tare da haifar da wata dabi’ar tir ta sauya launin fata. Haka kuma aure sai ya zama ba a na bin diddigin tarbiyya da asali ba ne, saboda sun ce su na son ‘Fara ko aljana ce’. mu hadu mako mai zuwa.              
                                   

No comments:

Post a Comment