A yanzu a duniya babu wani fanni da ke amsuwa fiye da fannin ilmin sanin halayyan dan Adam da qwaqwalwarsa. Wannan fanni wanda a turance a ke kiranshi da ‘Psychology’ ya na a sahun gaba cikin fannonin da su ke tashe. Haka kuma wadanda su ka karanta fannin sun fi saurin samun ayyuka; wadanda su ka hada da ayyukan wucin gadi, aikin din din din, da sauransu.
Wata qila mutum ya ce ai fannin ilmin akawu ‘Accounting’ shi ne mafi amsuwa da saurin samarwa mutum gurbin aiki. Eh, ba zan yi jayayya ba idan dan Nijeriya ya ce haka (dan Nijeriyan ma wanda bai san me ke tafiya a duniya ba), saboda a Nijeriya hukumomin da su ka gabata ba su dauki qwaqwalwar dan adam da muhimmanci ba. Babbar damuwarsu ita ce a qirga a kwashe, sai kuma a lissafa.
Amma idan mutum ya na bibiyan abubuwan da ke faruwa a qasashen da su ka ci gaba, qasashen da su ka dauki rayuwar mutanensu da muhimmanci, za ka samu cewa sun mayar da hankali sosai ga wadannan fannoni guda biyu; fannin kiwon lafiya da maganguna, da kuma fannin halayyar dan adam da qwaqwalwa.
Da yawan mutane na tsintar kawunansu a cikin matsalar qwaqwalwa wanda a qashin kansu ba za su iya yin cikakken bayanin me ke damunsu ba, haka kuma ba su san daga ina su ka yi gamo da wannan cuta ba. Da yawan ‘yan Nijeriya na fama da irin wannan. Mutum na da cuta a qwaqwalwarsa, amma bai ma san da zamanta ba.
Akwai wani masani da na ji ya na qalubalantar likitoci a kan matuqar su na buqatar aikinsu ya riqa tafiya lafiya qalau, wajibi ne su samu tarbiyya daga masana halayyan dan Adam da qwaqwalwa ko kuma ma ya kasance kowanne asibiti akwai sashen da ke wannan aiki.
Na yarda da zancen masanin, saboda a qasashen da su ka ci gaba, ba kowacce cuta ba ce a ke barin mai ita a hannun likitoci. Saboda a sau da yawa matsalar na da alaqa ne da qwaqwalwa. Aiki ne na masana wadanda su ka qware a sanin yadda matsalolin qwaqwalwar mutum da yadda ya kamata ta kasance. Masana a wannan fanni, su kan yi la’akari da damuwa, fargaba, qunci, da sauransu don bayar da shawara ga mutum.
Hadari ne sosai idan mutum ya na cikin damuwa amma kuma ya kasance ya na hadiye damuwar a cikinshi. Yawanci mutane masu irin dabi’ar nan ta shiru shiru (rashin son yin magana) sun fi fadawa wannan hadari. Saboda haka ne akwai wasu masana halayyar dan Adam da qwaqwalwa wadanda a ke kira da ‘Counseling Psychologist’, babban aikinsu shi ne su koyawa mutum yadda zai iya yin magana cikin mutane, yadda za ka iya fadin ra’ayinka, ka amayar da abin da ke cikin cikinka ba tare da wani boye boye ba.
A lokuta da daman gaske an fi samun wadanda su ka qware a fannin kwakkwafa tunanin mutum don ya iya magana a asibitocin lura da masu cutar qwaqwalwa, manyan asibitoci har ma da makarantu. A qasashen da su ka ci gaba a na samarwa da makarantun Firamare irin wadannan qwararru ne saboda su riqa lura da yanayin dalibai yara. Saboda a sau da yawa akwai yaara haziqai amma ba su iya yin magana ko su fuskanci al’umma domin bayyana hazaqarsu.
Wuce nan ma, ya na daga cikin aikin irin wadancan qwararru shiga tsakani don sansanta ma’aurata a al’amuran da ke buqatar shawarwarin hankali, tunani, qwaqwalwa da sauransu. Idan da a yankin Arewacin Nijeriya ma’aurata za su riqa neman shawarwarin irin wadannan qwararru ba tare da gaggauta yanke hukunci ba, da an samu sauqi a yawaitar mutuwar auren da mu ke fama da ita, da zawarawa sun yi qaranci.
Akwai nau’in mutanen da ke fama da gurbatar qwaqwalwa, ba dole sai al’amarin ya kai su ga bin bola ko titi ba, ba dole sai sun fara buge buge ko zare idanu ba. Wani ya na da irin wannan cutar, amma saboda rashin neman shawarar masana a hankali za ta yi ta girma daga qarama zuwa babba.
Kai da kanka idan ka aikata wani aikin, har cikin zuciyarka ka san ka na buqatar likitan qwaqwalwa. Gurbatar qwalqwalwa ne ke sa mutum ya riqa sawwala cewa abun da ba zai yiwu ba zai iya yiwuwa, kamar mutum ya fara tunanin idan ya sa tafin hannunshi zai iya hana hasken rana bayyana. Ko kuma mutum ya na da ‘ya ‘ya, sai ya riqa nuna fifiko a bayyane a tsakanin ‘ya ‘yan, kuma har ta kai ‘ya ‘yan su fahimci fifikon; wannan ma matsala ce ta qwaqwalwa wacce mutum ke buqatar masana ‘Clinical Psychologist’ su yi mishi bayanin mafita don a magance ta.
Mafi burgewa a wannan fanni shi ne fannin da qwararru ke son sanin yadda mutane ke aikata wata dabi’a, kuma don me su ke aikatawa a cikin al’umma. Wannan sashe shi ne a ke kira da ‘Social Psychology’. ta ya za ka iya tasiri a dabi’ar mutane, haka nan kuma ta wanne siffa dabi’arsu za ta iya tasiri a kanka?
A taqaice dai a nan akwai abubuwa guda biya, su ne; matuqar akwai mutane a tare da kai, tsaf za su iya yin tasiri a dabi’unka. Na biyu a dai dai lokacin da qwaqwalwarka ta iya tantance cewa akwai mutane a wurin da ka ke nan ma kasantuwarsu zai canza dabi’arka.
Kamar misali, idan ka je gidan surukanka (iyayen matarka), yanayin yadda za ka natsu ka riqa bin komi sannu a hankali zai saba da yadda za ka riqa yin abubuwa yayin da ka ke tsakiyar gidan iyayenka.
Wannan misali ya nuna kenan kasantuwar a gidan surukanka ka kawo a qwaqwalwarka cewa akwai iyayen matarka, ‘yan uwanta maza ko mata, wannan zai sa ka tilastawa dabi’arka domin yin komi yadda ya dace. Amma idan da a ce a gidan surukan na ka, sai ka samu tabbacin cewa babu kowa a gidan, duk sun yi tafiya, a irin wannan yanayi z aka saki jiki ne ka aikata duk wata dabi’ar da ita ce asalin dabi’arka. Mu hadu a mako mai zuwa!
No comments:
Post a Comment