Akwai wani lokaci da na je qauye a Arewacin Nijeriya, sai na yi niyyan siyan Kankana. Yayin da mai kankana ya zabo wata ‘yar babba, ya na so ya yanka, sai na lura wuqar ta yi datti sosai, na buqaci ya wanke ta tukunna. Ba tare da qyashi ba, ya tsuguna ya sa hannu a wani magudanan ruwa ya fara wanke wuqan, daga can nesa na hango yara da masu wucewa na tsayawa su tsula fitsari abunsu a magudanan ruwan.
Nan da nan na yi gaggawa na ce mishi, Malam ban ma so a yanka, kawai bani Kankanan a haka, ba tare da an yanka ba. Ina ganin wannan, wani zance na masana halayyar Jama’a ne ya fado min, inda su ke cewa, ‘Yayin da mutane su ke kallon abu a matsayin shi ne haqiqa, toh shi ne haqiqan a dukkan mu’amalolinsu.’
A dan wannan misali, mu na iya ganin yadda shi a wurin mai siyar da Kankana na qauye, bai yarda a haqiqa cewa akwai wasu qwayoyin cututtuka ba. Ni kuma da na zo daga birni na yi imanin cewa a haqiqanin gaskiya akwai qwayoyin cuta. Kuma kowanne dayya a cikinmu (tsakanina da mai kankana) mun yi aiki ne da yadda mu ka fahimci haqiqa.
Ba kawai wai ni ina da wayo ba ne ya sa na gaskata samuwar qwayoyin cututtuka, a’a, wannan ya na da alaqa da al’umman da na taso a cikinsu ne.
Wani qarin misali dangane da yadda mu ke kallon haqiqanin abu, shi ne misalin wasu tagawaye, masu suna Jack da Oscar, wadanda a ka yi rainonsu har zuwa girma a wurare daban daban. Jack an yi rainonshi a Trinidad shi kuma Oscar an raine shi a qasar Jamus.
Jack sai ya girma da qiyayyar Hitler a zuciyarshi, saboda a Trinidad ya taso. Yayin da dan uwanshi Oscar kuma ya girma da qaunar Hitler cike da zuciyanshi.
Wannan ya nuna mana cewa ashe ba wai abun da Hitler ya aikata ba ne asalin haqiqa. Haqiqa shi ne yadda mu ke kallon abun da shi Hitler din ya aikata.
Lokacin da a ka sace ‘yan matan makarantar Sakandare sama da 200 a garin Chibok. Yanayin yadda gwamnatin shugaban qasa Goodluck Jonathan ta riqi al’amarin ya na da fassarorida yadda kowanne mutum ko bangare na mutane za su kalle shi.
A garin Chibok da wasu yankunan Arewa, za a kalli wannan a matsayin sakaci daga shugaban qasa, saboda shi ke da ikon kiyaye duk wani dan qasa. Amma idan ka samu wani dan Neja Delta, zai iya ce ma ka babu laifi a banzantar da zancen da Shugaban Goodluck ya yi har na tsawon awanni 48, saboda bai yi imanin an sace su da gaske ba.
Masana halayyar Jama’a da zamantakewa (Sociologist) su na kiran irin wannan da yadda a ke kallo ko fassara haqiqanin al’amari. Al’umman da mu ka taso a cikinta ne ko dasa mana abubuwa da daman gaske, ciki har da yanayin yadda mu ke fahimtar haqiqanin abu. Ko mun sani ko ba mu sani ba, tasirin inda mu ka taso ne ke koyar da mu qin wani al’amari ko mutum, tare da son wani al’amari.
Wannan ba qaramin maudu’i ba ne, duk da wani na iya kallonshi a matsayin Kalmar ‘TSORO’ zalla, alhali al’amarin wuce nan.
Idan ka na so ka san menene haqinanin ma’anar tsoro, sai ka kalli Kalmar ta siffofi daban daban; idan kuwa har ka kalleta ta siffofi, za ka gamsu cewa babu wani ma’ana guda daya da ke daukan gundarin fassaran Kalmar ‘Tsoro’.
Misali, idan a ka ce abinci, ka ga ko ma dai menene, abun da ke fara zuwa a zuciyar duk wanda ya ji Kalmar shi ne, wani abu wanda zai iya yiwuwa ya shiga cikin mutum ya zauna, ko kuma ya shiga cikin a amayo shi.
Amma kawai idan a ka ce ma ka ‘Tsoro’, za ka buqaci a ba ka dama ka yi bayani, saboda shi ba yanayinsu daya da Kalmar ‘abinci’ ba. Sai a tambaye ka a ce ka fassara menene tsoro?. Ina mai tabbatar da cewa idan a ka yiwa mutum biyar wannan taambaya, amsoshinsu za su zama daban daban, amma idan ka tambaye su menene abinci, dole a amsarsu sai sun yi kamanni da juna.
Wani zai ce, tsoro shi ne firgita. Yayin da amsar wani za ta kasance, tsoro shi ne kidimewa. Wani amsan kuma na iya cewa tsoro shi ne fita daga hayyacin dai dai zuwa wani hayyaci na ba dai dai ba.
Toh idan haka ne, irin wadannan kalmomi, ta ya za mu iya fassara su ko kuma mu fahimce su yadda ya dace? Wannan ba wani abu ba ne mai wahala, ya na da sauqin gaske.
A wurin qananan Yara ‘yan qasa da shekaru 10, tsoro shi ne duk wani abu mai muni. Don haka ne ma za ka ga a lokuta da dama, irin Yaran nan masu qiriniya, sai ka ga iyayensu na ce musu ga ‘DODO’ nan. Ba wai Dodon ba ne da gaske, sannan ba wai kawai fadin Kalmar Dodon ba ne a baki, idan iyayen su k ace ga Dodo nan, sai su yi wani irin yamutse fuska ko su ma su yi wani irin firgigi yayin da su ke cewa dodon na zuwa.
Wannan yanayi da iyayen ke yi, shi ne yin tasiri a zukatan Yara, sai su gina tsoron dodo a zukatansu. Ka na iya gane tsoro a yanayin Yaro, yayin da yana yin wani abu, sai mahaifiyarshi ko mahaifinshi ya ce, ‘Ku kawo min Bulala’, a nan ba wai Kalmar bulalar b ace ke da tasiri, ta na iya yiwuwa an taba tsula ma yaron bulala, don haka qwaqwalwarshi ta kiyaye tsoron bulala.
Kaman ka kalli mutum geme – geme ne k ace mishi ga Dodo, kai ma ka san ka na batawa kanka lokaci ne. ko kuma ka kalli matashi wanda yah aura shekaru 20 zuwa sama (yana ganiyar balaga) don ya yi laifi ka ce a kawo bulala.
Tsoro a wurin matasa, shi ne kakkausan kalamai daga bakin iyayensu ko wasu wadanda su ke qimantawa. Za ka ga a lokuta da yawan gaske, idan wani abun firgici ya faru, za ka ji matashi na cewa, ‘Ni wallahi ban tsorata ba’, saboda shi a wurinshi, dar din da ya ji a cikin zuciyarshi ba sunanshi tsoro ba. Amma idan a ka kori matashi daga makarantar sakandare ko Jami’a, za ka ji ya na cewa, “Tsorona shi ne idan mahaifi ko mahaifiyata su ka sani”.
A qarshe ina so mu gane cewa, tsoro shi ne tsoro. Yadda ka fahimce shi a na ka tunanin, ya bambanta da yadda baturen Ingila ya fahimci shi. Mu hadu mako mai zuwa
No comments:
Post a Comment