Tarihi ya tabbatar da cewa abubuwa uku ne ke tasiri a kan yawan mutane, bayan abubuwa ukun nan babu cikon na hudunsu. Na farko akwai mutuwa, akwai haihuwa sannan kuma hijira.
A wannan makon zan so ne mu shiga cikin mutuwa tare da fahimtar alaqarta da yawan al’umma (Population). Masana tun a farkon wannan fanni na ilmin sanin yawan al’umma ‘Demography’ sun fara yin bayanai ne dangane da mutuwa, bisa dalilin cewa ita mutuwa barazana ce ga yawan al’umma, ba ta qara yawan mutane, sai dai ta rage musu yawa.
Saboda wancan dalili ne masanan su ka ba al’amarin mutuwa muhimmancin gaske, su ka yi ta gudanar da binciken musamman domin a iya fahimtar MUTUWA da irin gudummawar da ta ke bayarwa ga ragewar al’umma.
Mutuwa dai dole ce, babu wata halitta da ta isa ta yi fariyan cewa ita da mutuwa sun raba gaari. Kowanne mutum ya na da alaqa da mutuwa, ko don wannan alaqar ta musamman da ke tsakanin mutane da mutuwa, ya ishi masana halayyar jama’a da zamantakewa su yi bincike a kanta.
Dukkanin mutuwa da kan auku su kan kasance daya daga cikin biyun nan; ko dai sanadiyyan gadon cuta daga Iyaye ko wata larura , na biyu ko kuma mutuwa sanadiyyan abubuwan da ke zagaye da mu na mu’amalar rayuwar yau da kullum.
Wannan ba taqaddama ba ne wanda a ka fara a yau, ko kwanakin nan ko kwanakin baya kadan. An tafka muhawara sosai dangane da wanda su ka fi saurin mutuwa tsakanin maza da mata a shekaru aru aru, wanda saboda a kaucewa zargin bin son rai, gudun kaucewa matakan tabbatar da ilmi ya sa masana su ka yi ta gudanar da bincike.
Ban manta ba, na taba karanta muhawarar wani masani mai suna John Grunt a binciken ilmin da ya gudanar a shekarar 1662 a Landan. Ya gudanar da binciken ne ta hanyar bibiyan dukkanin ofisoshin rijistar mutuwa inda ya tattara bayanai dangane da adadin yawan matattun da a ke da su. Sakamakon binciken John Grunt ya tabbatar da cewa ‘An fi haihuwar Maza fiye da Mata; sannan kuma Maza sun fi mata saurin mutuwa’.
Irin wadannan nazariyya su na nan da yawa wadanda masana su ka gudanar tare da fid da sakamako da dalilansu. A wannan sharhin nawa, kafa misali da binciken John Graunt kadai ya wadatar, saboda idan zan ci gaba da kawo misalai ba zan samu damar dora wasu bayanai masu muhimmanci ba.
A dai dai lokacin da a ka haifi jariri daga shekara 0, a wannan shekarar babban abun da ya fi komi sauqi shi ne ya kwashi qwayoyin cuta wadanda ke kashe garkuwan jikin dan Adam, saboda qwayoyin garkuwan jikin jariri ba su da qwari. Dalilin haka ne jarirai da dama ke kasa tsallake wannan shekara.
Ko a tsakanin shekara ta 0 da a ke tsammanin yawaitar mutuwan jarirai sakamakon iya diban qwayoyin cuta; Maza sun fi mata diban wadannan qwayoyin cuta, kuma sun fi mata mutuwa a lokacin da su ke Jarirai.
Dalilin da ya sa Maza su ka fi Mata fuskantar barazanar mutuwa a shekarar da su ke Jarirai shi ne; Mace Allah ya na halittarta ne da wasu kariya na musamman, wanda Namiji ba shi da su, wanda wadannan kariya na musamman da ke qumshe a jikinsu ne ke yi musu garkuwa da dukkan cututtukan da ke kashe garkuwan jiki.
Daga shekarar haihuwa sifili zuwa hudu, daga shekara hudu sannan garkuwan jikin jarirai ya samu kuzarin da ya kamata, don haka babu fargabar za su iya arba da qwayoyin cutan da ka – iya zama sanadiyyan rasa ransu.
Wani qarin matsalan na tasowa ne a lokacin da a ka cika shekara 15 a duniya, a wannan shekaran yawanci maza sun balaga, sun fara tunanin neman na kansu, saboda haka za su kutsa ga neman ayyukan da za su kafa kawunansu don dogaro da kai.
Saboda haka bayan nazari da binciken masana, lissafi ya tantance cewa daga shekara 15 zuwa sama Maza sun fi mata mutuwa, sannan sun fi Mata kasancewa a cikin hadurran da ka iya cinye rayukansu.
Dalili a nan shi ne, Maza su na fara ayyuka da sana’o’in da za su riqa barazana ga rayukansu, barazana ga garkuwan jikinsu, barazana ga dukkan wani tattali da su ke yi na kiwon lafiya. Irin wadannan ayyyuka sun hada da aiki a masana’antu, ma’adinai, masarrafa da sauransu. Misali, ya za ka kwatanta garkuwar jikin mutumin da ke aiki a ma’aikatar da a ke amfani da sinadarin ‘Chemicals’, wanda shaqarshi babban hadari ne ga rayuwa.
A wani bincike kwanan nan, wani bawan Allah mai sana’ar siyar da tabarma ya sanar da ni cewa; ya gano cewa dukkanin masu aiki a masarrafan tabarmu ba su jimawa su ke mutuwa, sakamakon sinadarin ‘Chemical’ din da su ke shaqa.
A nan akwai taqaddama babba, amma taqaddamar na tasowa ne kadai a Nijeriya da wasu qasashen da a ke kira da ‘qasashe masu habbaka’. Taqaddamar ita ce; a qasashen da su ka ci gaba babu barazanar mutuwa ga Mata masu juna biyu, saboda su na kiyaye duk wata qa’ida ta likitoci, sannan kuma akwai qwararru da asibitocin wadatattu.
Amma idan mutum ya kwatanta da irin qasarmu Nijeriya, zai ga cewa Mata sun fi rasa ransu a lokuta da dama yayin da su ke dauke da juna biyu. Don haka a nan za mu iya kawo cewa a shekara 15 zuwa 49 Mata a qasarmu su na fuskantar yiwuwar haduwa da mutuwa, saboda ba a basu kulawar da ta dace.
Daga shekara 49 zuwa sama, a wannan lokacin kuma garkuwan jiki ya fara yin sako – sako, don haka ko a sannan Maza sun fi mutuwa fiye da Mata, saboda har zuwa wannan lokacin kariyar musamman da su ke da ita daga Allah ba ta rabu da su ba.
Daga qarshe, zan so mai karatu ya san cewa wannan nazari ya ginu ne bisa tabbatattun hujjojin da a ke dasu, wadanda a ka samu bayan an gudanar da binciken ilmi ‘Research’ tare da kiyaye qa’idojin binciken. Mu hadu mako mai zuwa!
No comments:
Post a Comment