Saturday, 11 April 2015

MAMA DAME PATIENCE: WAHIDI IYA!



Lallai sauyi ya zo; wata rana ina zaune a kofar gida, na jima ban ji almajiri na bara ba (neman taimakon abinci), bayan sallar Isha’i ne. kawai sai na ji wani ya zo, abun da ya bani mamaki shi ne sai da ya yi sallama. Ni a baya ban san almajirai na sallama ba kafin su fara bara.
            Ya ce; “Assalamu Alaikum, wahidi iya, sabida Allah, a taimaki almajiri Iya, domin Allah, don Kur’ani, ko dan kanzo, ko gaya ne ba miya Iya, Iya yunwa ba ta da hankali.”
            Har abada duniya  ba za ta manta da tarihin siyasar Nijeriya ba, musamman a zamanin dimokradiyya wacce ta faro daga shekarar 1999 bayan gushewar mulkin Soja sakamakon faduwar gwamnatin Janar Sani Abacha ta hanyar mutuwa.
            A lokacin sai wadanda a ke gani a matsayin jiga jigai a dukkan fannoni na Nijeriya, su ka kirkiri jam’iyyar PDP, wacce ita ta fara mulkin farar hula na dimokradiyya, bayan zagayowar shekaru hudu cur, a shekarar 2003 jam’iyyar ta ci gaba daga inda ta tsaya, wasu shekaru hudun su ka zo, a shekarar 2007 jam’iyyar PDP din ne dai. Bayan an lashe wasu shekaru hudun, a shekarar 2011 labarin dai shi ne babu wani canji, PDP.
            Wannan tagomashi da nasara, da karfi da izza da jam’iyyar PDP ke ganin ta samu, wanda a hakikanin gaskiya akwai karfin, kuma wannan karfi ya tsole ma ‘yan Nijeriya ido, karfin ya takurawa ‘yan Nijeriya musamman talakawa.
            Hatta jiga jigai, wasu ma da su a ka kafa jam’iyyar PDP idan masu mulki ko uwa a bakin murhu su ka yi wani siddabarun wanda ya saba da hankalinsu, ba su isa su ce uffan ba; ko dai su yi shiru ko kuma su yi magana a tsangwame su, idan ma ba su yi sa’a ba, sai a yi amfani da wannan karfi a toshe su, a kashe kaifin tasirinsu.
            Wannan karfi na jam’iyyar PDP ya sa a yawancin lokuta a ke kiranta da giwar jam’iyya a nahiyar Afrika. Duk wani abu da jam’iyyar PDP ta sa a gaba, zaman lafiya da kwanciyar hankalin kowa shi ne ta kai ga nasara, saboda idan ba haka ba, kowa zai ji a jikinsa.
            Hatta al’amarin da ya auku a shekarar 2011 na kone konen muhallan ‘yan jam’iyyar PDP a Arewa, sakamakon zargin murda murda a wasu jihohi. Maimakon ya nuna karshen kaskanci ga jam’iyyar, sai dai ma ya zama hannun jari ga ‘ya yan jam’iyyar da a ka kone ma gidaje da dukiyoyi. Idan an kona maka gida, uwar jam’iyyar za ta mayar maka da wani sabon gida a unguwar da ta fi na ka, da kayan bukatun rayuwa cike da gidan, sannan ta gyara maka gidanka fiye da baya.
            Idan dukiya a ka lahanta ma, za su mayar ma da ninkinta ba tare da dar dar ko faduwar gaba ba. Irin wannan nuna karfi da isa na jam’iyyar PDP ne ya kwantar da hankalin ‘ya ‘yan jam’iyyar, har su ke ganin shekaru 60 da su ke mafarkin za su yi su na mulkar Nijeriya, babu makawa sai sun kai cur sannan za su takawa tafiyar burki (shi ma idan sun so).
            ‘Ya ‘yan jam’iyyar PDP, musamman manyan jam’iyya sun dau wani irin girman kai da dagawa sun jibgawa kawunansu. Wannan zakin karfin jam’iyyar PDP ne ya yaudari mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo ya ke cewa babu wasu dattawa a Arewa sai shi. Shi a iya ka tunaninsa dattijontaka shi ne karfin ikon taka duk wanda ka so, tare da juya duk abun da ka so.
            Shi bai san cewa dattijo, natsattse ba ne, kammalalle wanda ya san ya kamata, ya ke kiyaye hakkokin wadanda Allah ya ba shi aron karfi a kansu, ba wai ya yi amfani da karfin wurin danne duk wanda ya nuna mishi yatsa ba.
            Wannan zakin karfin jam’iyyar PDP ne ya sa mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo duk ranar da zai shiga Kaduna a karshen mako, mutane da yawan gaske su kan rasa kasuwancinsu, saboda jami’an tsaro na tarwatsa duk wata hidima da ta shafi hanyar da zai bi. Maimakon a matsayinshi na mai ikirarin dattijo ya kiyaye irin wannan.
            Wani babban abun mamaki shi ne irin nuna isa da karfin iko da matar shugaban kasar Nijeriya , Madam Dame Patience Jonathan, wacce a kafafen watsa labaru a ke yi mata lakabi da ‘Mama Peace’ wai maman zaman lafiya.
            Ka na kallon fuskan Mama Dame Patience ba ka bukatar a ce ma ka irin mutanen nan ne da ke sako magana ba dadin ji. Tun bayan da Allah ya dauki rayuwar marigayi Umaru Musa ‘Yar’aduwa, mataimakinshi shugaba Goodluck Ebele Jonathan ya maye kujerar, Mama Patience ta fara zubo maganganu, har ta kai ‘yan kasa na tsokanarta, musamman a fannin gurbataccen turanci da ta kware a kansa.
            Lokacin da babban zabe ya matso a shekarar 2015, Mama Patience ta yi ta sakin layi, sai dai abun bai wuce gona da iri ba, har sai bayan da a ka dage zaben shugaban kasa zuwa 28 ga watan Maris, daga nan ne fa ta karbi ragamar yakin nemawa mijinta dawwama a kujerarsa.
            Duk inda ta je yawon kamfen sai ta kafa tarihi, bakin tarihi ga Nijeriya da bakin fenti ga matsayin uwargidan Shugaban kasa. Wani wurin ta ce ai Janar Buhari kwakwalwarshi ta zama jabu, ta kusa daina aiki. Me za a ci da mutum tsofai – tsofai, zai zo ya na takara da ‘ya ‘yan cikinshi. A jihar Ribas cewa ta yi, duk wanda ya zo ya ce musu chanji, su yi mishi jifan rajamu ba kakkautawa.
            Mafi munin sakin bakin ‘Mama Peace’ shi ne inda ta ke cewa wai mai gidanta bai bukatar kuri’un ‘yan Arewa. Mutanen da ba su da aiki sai haihuwar yara su na zubarwa a titi, karshe su zama Almajirai.
            Lallai fa MAMA kin ga aikin almajirai. Su ne dai su ka yi ruwan miliyoyin kuri’u daga jihohin Kano, Katsina. Mama almajiran jihar Kaduna, Yobe, Sakkwato da Zamfara duk sun ki su zabi mijinki. Almajiran jihar Adamawa, da na jihar Kebbi duk sun ki jefa ma mijinki ne saboda kin ce a kai kuri’unsu kasuwa. Mama almajiran jihar Borno sun jima cikin kuncin kisan gilla, dole ta sa su ka ce, su dai PDP Sam!
            Mama Patience baki shi ke yanka wuya; maimakon ki ja bakinki ki yi shiru, ga shi yanzu kin janyowa mijinki asarar kuri’un dukkan almajiran Arewa, ‘ya ‘yan da kika yiwa kazafin a na banzantar da su a titi.
            Cikin fushi da hasala da irin wadannan kalamai na ki marasa fasali da dadin ji, almajiran nan su ka yi mursisi, su ka yi ta ruwan kuri’u ga babban almajiri, mutumin da ki ka kira da tsofai tsofai, wanda ki ka ce kwakwalwarsa ta mace; shi din dai, da wannan kwakwalwa ya yi tasiri a kan mutanen yankin Yarbawa. Mama ya ki ka ga aikin mutanen Osun, Oyo, Legas? Mama mutanen Binuwai ma sun fusata, watakila su ma almajiran ne, domin babban almajiri Janar Buhari tsaf ya cinye jihar.
            Mama na san sarai kin kasance a gaban akwatun talabijin dinki, a dai dai lokacin da dattijon yankinku na Neja Delta, Orubebe ya tayar da hayaniya a dai dai lokacin da a ke tattara sakamakon alkaluman jihohi. Shi dole tsagera, amma abun mamaki, ko da ya gama kumfar baki da cije cije hade da zare idanu, sai almajiri Jega ya nuna mishi irin dattijontakan almajiran Arewa, ya kwabe shi, ya yi mishi nasihar da duk duniya sai da a ka jinjinawa wannan salo na Farfesa Attahiru Jega. A cikin ruwan sanyi, ya tsula ma mai kiriniya tsumagiya, ya dawo hayyacinshi.
            Mama ya kamata ki sani har abada mutanen yankin Neja Delta da ‘yan uwan shugaba Goodluck Jonathan, da jikoki da tattaba kunne, har ma da ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP ba za su taba mantawa da wannan mummunan kaye da sakakkun kalamanki su ka janyo musu ba. Yanzu lokaci ne da ya dace ki bi gida gida na ‘yan jam’iyyar PDP masu mafarkin shekara 60 su na mulki, ki basu hakurin harzuka almajirai da ki ka yi su ka kifar da jam’iyyar da ruwan kuri’u. WAHIDI IYA! Mu hadu mako mai zuwa


No comments:

Post a Comment