Mai karatu a wannan makon zan ta~o wasu
muhimman abubuwa guda biyu, wadanda ke kishiyantar juna. Kuma dukkaninsu na da
alaka da rayuwarmu ta yau da kullum.
A
da ban hankali na bai ta~a zuwa kan wadannan abubuwa ba, saboda ko kadan kwakwalwata
ba ta salwanta min muhimmancinsu da kuma tasirinsu a rayuwa ba. Wasu lokuta
baya mu na darasi, sai malaminmu ya shigo da batun ‘Kyauta da rowa’, ya yi mana
dogon bayani (wanda shi a wurinshi ya takaita). Har ma ya sha alwashin in Allah
ya yarda zai yi nazarin kyauta da rowa.
Kafin
na ci gaba da bayani, akwai wani abu mai sarkakiya wanda ya kamata mu warware
shi. Shin kyauta ko rowa a na yin gadonsu ne, ko kuwa koyonsu a ke yi?
Wannan
tambayar ba ta da wani bambanci da tsohuwar tattaunawar nan dangane da dabi’ar dan
Adam, wanda wasu ke hakikancewa a kan cewa ai dabi’a tana tattare ne a cikin
jininmu, daya ~angaren kuma su ka ce, a na koyon dabi’u ne a cikin al’umma.
Idan
mutum na da yawan kyauta, za ka ji hausawa na cewa ya na da jinin kyauta. Sai
dai wannan Karin Magana kadai bai isa madogara gare mu ba, mu yanke hukuncin
cewa ai in dai mutum ya hada jini da masu kyauta babu makawa shi ma zai zamo
mai kyauta.
Wannan
rusasshen zance ne, idan za mu yi la’akari; misali akwai tagwaye (twins) wadanda
a ka haifa a garin Kaduna. Sunansu Hasan da Husaini, tun bayan kwana bakwai da
haihuwansu, sai mahaifinsu ya yanke shawarar zai raba su wurare daban daban a
hannun kannenshi.
Da
a ka tashi sai a ka kai Hasan kasar Ingila, shi kuma Hussaini a ka kai shi garin
Gombe. Har zuwa lokacin da su ka girma su ka fara aiki. Abun lura a nan shi ne,
idan Hasan da ke kasar ingila ya taso tare da mutane masu ra’ayin turawa na
cewa taimakon talaka kuskure ne, saboda idan yau ka taimaki talaka ba zai mike
ya nemi na kanshi ba. Shi kuma Husainin ya taso a wurin mutanen Gombe, wadanda
za su iya sadaukar da dukkan abun da ke cikin aljihunsu domin yin hidima ga bako,
ko kuma mutanen da ke fito da abinci kofar gida a taru a ci.
Wannan
ya nuna mana a fili cewa Hasan zai koyo rowa matsananciya, shi kuma Husaini zai
koyo yadda a ke kyautata ma mutane. Wannan dan gajeren misali kadai ya isa mu
gane karfin ikon wurin da mutum ya taso ga halayyenshi, musamman halin kyauta
ko rowa.
Tun
a rayuwarmu ta yau da kullum mu kan ga alheran da ke tattare da kyauta, haka
kuma mu kan ga sharrrukan da ke tattare da rowa. Mutumin da ke da kyauta, ya
kan zama mafi soyuwa a tsakanin mutane, sannan mutane ba za su aminta a hada
kai da su wurin cutar da shi ba.
Akasin
haka ga marowaci. Idan mai gida (oga) ya kasance marowaci, babu makawa da
yaranshi (ma’aikata) za a hada baki a halaka shi ko a gurgunta al’amuranshi.
Saboda ai tsaro ba ya na nufin mai gadi da bindiga ba ne kawai, mafi girman
tsaro shi ne tsaro wanda mutum ya samarwa kanshi ta hanyar mallakar zukatan wadanda
ya ke tare da su. Idan kai mai arziki ne, amma ma’aikatanka ko da yaushe su na
cikin matsanancin wahala. Kenan watan wata rana makiya za su iya ba mai dafa
mishi abinci (kuku) guba ya zuba mishi don ya ci ya halaka.
Sirrin
cin moriyar rayuwa na tattare da kyauta. A wasu lokutan ma kyautar da mutane ke
yi kanana su na ganinsu ba a bakin komi ba, amma wannan abun alheri zai ci gaba
da binsu har ‘ya ‘ya da jikoki.
Idan
kuwa halin ka kenan rowan tsiya, wannan tabon na marowaci, ya yi ta binka
kenan. Har ma idan a ka ci sa’a cikin ‘ya ‘yanka ko jikoki a ka samu wani mai
halin kyauta, sai ka ji jama’a na cewa Allah sarki mahaifinshi ko Kakanshi
marowaci, amma shi kuma mai kyauta.
Abubuwa
biyu ne masu karo da juna. Sai dai ya na da kyau mu gane cewa wadannan halaye
guda biyu, al’umma na da hakkin koya wa mutum su. Idan mu ka kasance masu halin
kyautatawa, ‘ya ‘yanmu da wadanda ke tare da mu za su taso da wannan hali. Shi
ya sa masana halayyan jama’a da zamantakewa su ke cewa al’umma ne ke gina dabi’ar
mutum. Mu hadu a mako mai zuwa
No comments:
Post a Comment