Haha! Matukar ka na raye za ka yi gane – gane a duniyan
nan, musamman idan ka na mu’amala da mutane barkatai, ko kuma ka na da ikon
samun labarun yanayin yadda mutane daban daban daga sassan duniya su ke gudanar
da rayuwarsu. A nan ne za ka tabbatarwa da kanka karfin halin ‘yan neman suna.
Siyar
da rai kala kala ne, kuma kusan masu irin wannan dabi’a ta siyar da rai sun san
duk wata hanya da za su bi su aikata hakan, a wasu lokutan ta sha rutsawa da
su, a wasu lokutan kuma su tsallake rijiya da baya.
Idan a
ka ce siyar da rai kawai a ka yi shiru. Sai mutum ya dauka a na nufin a wurin
siyar da ran dole sai ya kasance akwai barazana ga rayuwa. Wanda kuma ba haka
ba ne, siyar da rai a nemo suna, ya na iya kumsar aikin da zai zubar da
mutunci, kima, dattako ko ya rage kaifin wayonka a idon jama’a. wannan shi ne
ma babban siyar da rai.
Wasu
misalai na siyar da rai amma a ka samo sunan
da a ke nema, shi ne irin kekyashewa da tsayin dakan da tsohon
mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya yi gab da zaben shekarar
2007. Inda ya fito kaitsaye ya yi fito na fito da muradin mai gidanshi, tsohon
shugaban kasa Olusegun Obasanjo.
Siyar
da ran da Atiku Abubakar ya yi, a na iya cewa ya ci riba, ya kuma yi suna sosai
a wancan lokaci. Musamman yadda ‘yan Nijeriya su ka fara kallonshi a matsayin
wani sabon gwarzo, wanda ya rusa sabuwar akidar ‘Third Term’.
Atiku
Abubakar bai tantance fada wa kasadar siyar da rai ba, har sai da ya samu
tabbatattun hujjoji a kan maigidanshi Obasanjo ba zai tallafa mishi don ya maye
gurbinshi ba. Sannan ya tabbatar da cewa idan har hakar ‘Third Term’’ ta cimma
ruwa, shi kam sai dai kuma tarihi. Zabi
biyu a wancan lokaci Alhaji Atiku Abubakar ke da su; ko dai ya danne zuciyarshi
ya hadiyi hakuri da duk wani wulakanci da zai biyo baya. Ko kuma ya kaddamar da
yaki ba kakkautawa.
A ‘yan
kwanakin baya ma, siyar da ran da Malam Ibrahim Shekarau ya yi babban misali
ne, saboda shi kanshi ya san ya siyar da rai ne a matakai biyu; komawa
jam’iyyar PDP wacce a baya ya la’ance ta iya la’anta da abubuwan da za su biyo
baya na kallon da jama’a za su rika yi mishi. Na biyu shi ne ya zauna a cikin
jam’iyyar adawa ta APC ma siyar da rai ne. bisa dalilin ita uwar jam’iyyar ta kasa
ta shardanta cewa duk jihar da gwamna ko
mataimakin gwamna ya komo jam’iyyar, shi ne zai zama shugabanta na jiha.
A
halin da Malam Shekarau ya tsinci kanshi, ko dai ya zauna a cikin jam’iyyar ta
APC karkashin abokin adawanshi gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso ko kuma ya kama
gabanshi (matakin da ya dauka). Karshenta dai da Malam Ibrahim Shekarau ya duba
da kyau, ya natsu ya ga cikin biyun, wanne siyar da rai ne zai zamar mishi mai
sauki sauki.
Tsoron
yin kasadar siyar da rai ne ya hana mutane irinsu Gwamna Sule Lamido, da Gwamna
Babangida Aliyu su biye ma takwarrorinsu su Gwamna Aliyu Magatakarda Wamakko,
Gwamna Kwankwaso da Gwamna Amaechi. Saboda ba su shirya ba, kar wurin neman
suna su kwan ciki.
Wadannan
su ne kadan daga cikin misalan siyar da rai a siyasance. Haka nan a mu’amalarmu
ta yau da kullum, cike ta ke da siyar da rai. Musamman wadanda babban burinsu
shi ne neman suna da son a ce su ne su ka yi kaza da kaza.
Wasu mutanen dabi’arsu kenan a ce su ne su ka
fara aikata wani al’amari, ko su ne su ka dai daita wani abu, alhali ba za su
yi nazarin me neman sunan nan zai iya janyo musu ba. Shin idan sun siyar da
rai, kima da darajar da su ke kwadayi za su samu ko a’a?
Kowanne
mutum mai hankali a duniyan nan, ya na da lura da kiyaye abubuwan da kan je kan
dawo. Kawai yawancin abun da ke cutar da mutane a wannan zamani shi ne rashin
tunani. Kyau a ce duk abun da ka riska ka tsaya ka yi tunani, ka yi nazari na
musamman dangane da abun, ka tantance ka
cire abubuwan da za su iya shafar mutuncinka ko kima, ko daraja, idan har akwai
wadannan barazana masu yawa, sai ka yi hakuri kawai.
Saboda
mutunci shi ne mutum. Duk lokacin da kaso 40 cikin 100 na jama’an da ke
kallonka da mutunci su ka daina, ina mai tabbatar maka da ka rasa wani babban
abu a rayuwanka wanda zai yi ta janyo maka asarori na daukaka da amintan
jama’a, har zuwa lokacin da za a sake sakankancewa da kai da al’amuranka.
Sau da
yawa, ya fi kyautuwa ka yi shiru a abun da bai shafe ka ba. Wasu kan yi alkawuran
siyar da rai, don kawai su farantawa mutum rai, alhali idan alkawarin bai cika
ba, maimakon su nemo suna, sai dai su zubar da suna.
Daga karshe
ina kira ga masu dabi’ar siyar da rai don neman suna, su taimakawa kansu su
rage, saboda ba kowanne siyar da ran ba ne ke tattare da suna. Wani maimakon
nemo suna, sai dai ya janyo kuka da raunin da tabonshi ba zai taba gushewa ba. Mu hadu
mako mai zuwa!
No comments:
Post a Comment