Wannan shafi an samar da shi ne domin watsa rubuce rubuce na ilmantarwa da fadakarwa musamman wadanda su ka shafi IIlmin sanin halayyar dan Adam da zamantakewa (Sociology). Alqalamin shafin zai fi karkata ga rayuwa, musamman na matasa. Sunan shafin ya samo asali ne daga jaridar Leadership Hausa. Shafi ne wanda ke kawo rubuce rubucen marubuci Sulaiman Bala Idris (ISB DAURAWA) +2347036666850
Saturday, 17 January 2015
Bankwana da zaman lafiya: Kirkirarrun masifu, da bala'o'i
Nijeriya kasa ce mai muhimmancin gaske, wacce hatta kasashen duniya da a ke ambato da tinkahon duniya 'super powers', su na kiyayewa da mutunta wannan matsayi.
Wannan matsayi da Nijeriyarmu ta samu, ya samo asali ne daga wasu daidaikun abubuwa da su ka hada da yalwataccen tattalin arziki; girman kasa mai albarkatu. Da kuma yawan adadin mutane wadanda alkalumma ke tabbatar da cewa sun kai miliyan 150 (tun muna yara ake wannan hasashe).
Akwai yaduwar mutane a dukkanin kusurwowin kasar, Arewaci sun fi kowa yawa, akwai a kudanci, Yammaci, da Gabashi.
Shekaru kadan baya rigingimu su ka fara yi wa yankin Arewacin Nijeriya zaizaiya ta kasa, a hankali tun ba a ankara ba, har ta kai a yau, an ankare.
Sauyin yanayi ya kawo mu wani zamani na rainin hankali, wanda karfin iko da mulki ba su tafiya dai dai har sai an sirka su da dabarun mallakar kwakwale da tunanin al’umma.
Kuma zamani wanda a ke haifar da bala’i, masifa, tashin hankali, barazana, firgici domin samar da mafita ga wata matsala.
Tun shekaru aru aru wasu kasashen duniya su ke amfani da irin wannan lissafi domin cimma burinsu.
Wannan bahaguwar falsafa ba ta samu wurin zama na musamman a Nijeirya ba, har sai wannan lokaci na mulkin farar hula wanda ke tafiya bisa turbar dimokradiyya. Tun mutane ba su fahimta, har ta kai a na fahimtar sabon salon, kuma kowanne shugaba idan ya zo, ya na zuwa ne da irin na shi rainin hankalin.
Wannan dabara da wasa da hankali ne ya samar da mutane irinsu Alhaji Muhammad Dokubo Asari, wanda a ka kirkire shi a cikin dirkirarrun tsagerun yankin masu gadara da shimfidadden danyen man fetur a karkashin kasa (Neja Delta).
Ga wadanda sunanshi kawai su ke ji, Dokubo Asari mutum ne wanda bai iya furuci ba ko miskala, hotunanshi babu abun da su ke siffantawa face rashin natsuwa da kamala.
Mayaki ne (a ikirari) wanda bai san salo da dabarun fito na fito ba, shugaba ne (na ‘yan tsagera) wanda wakilcin shi ga wadanda ya ke wakilta abun tir ne da Allah wadai.
A wannan makon na sadaukar da wannan shafi ne don wayar da kawunan wadanda a ke son a zurma su cikin rami kuma a rufe.
Samuwar Arewa da rashin samuwarta ya na a hannun al’umman yankin ne, idan sakaci da rashin sanin ya kamata ya sa su ka lankwashe hannuwa, su ka rungumi kaddara (kamar yadda kakanninsu su ka yi a ka yage Nijar daga Arewa), ai kuwa dole ne ta fashe a yi wasosonta.
Barazanar ‘ya ‘yan biyuu-ahu irinsu Dokubo ba shi ne babban matsalar ba, su dai kumfar bakinsu kamar ‘yar nune ce wacce ke shaidawa al’umman yankin cewa sha-zumamu na sunsuno zaki.
Mutum mai iyali, wanda shi ne shugaban gidanshi ba zai kuskura ya fadi wata magana wacce furta ta zai iya tarwatsa zaman lafiyan gidan ba. kai ko da kuwa rashin zaman lafiyan tsakanin gidanshi da gidajen makwabta ne.
Ballantana kuma a ce shugaba, ba abin mamaki ba ne ga shugabannin yankin Neja Delta, tunda ba farau ba inda sakin layi ne a fadi zancen bur. Sai dai kalaman Alhaji Dokubo dole ne a daura a sikili a yi nazarinsu.
Ga kadan daga cikin irin zantukanshi wanda na nakalto kaitsaye daga jaridar Vanguard ta ranar 11 ga watan Mayun 2013. “Ina son jaddada cewa babu fa zaman lafiya da zai wanzu, ba wai a yankin Neja Delta ba, a’a a dukkanin Nijeriya, matukar Goodluck Jonathan bai ci zaben 2015. Sai dai idan kuwa Allah ya dauke rayuwarshi ne, wanda kuma ba mu fatan haka. Kamar yadda tsarin mulki ya zo da shi, Jonathan ya na da shekaru 8 cur wadanda zai yi a kujerarshi.”
A wasu yankunan, idan ka ji mutum na fadin irin wadannan soki – burutsu za ka ji a na cewa ya na yin zancen ‘yan tasha. Domin a tasha ne za ka je ka tarar da zauna gari banza, marasa ta ido. Hatta ‘yan tashan cikin siyasa daidaiku ne za su iya runtse ido su yi ta soko maganganu haka.
Sai dai kash!, mutumin fa da ya ke ta wadannan maganganu ba komin komai ba ne, kuma ba kowa ba ne shi, zaman lafiya kuma da ya keta kurarin zai kare ai mu tuni a yankin Arewacin Nijeriya mu ka yi bankwana da zaman lafiya. Manyan jihohinmu da mu ke takama da su kirkirarrun tsagera takwarorin su Dokubo sun tarwatsa ma na su da bama bamai.
Sai da a ka tarwatsa zaman lafiya a shahararren birnin Jos, wanda kafin rikici a ke wa lakabi da gidan zaman lafiya. Irin wannan kirkirarren rikicin addini da kabilanci ne kuma a ka haifar a jihohin kaduna da sauransu.
Rikicin addinai da kabilanci ya biyawa wadanda su ka kirkiro shi bukata. Haka nan kuma rikicin tsageran Neja Delta ma ya biyawa kirkirarrun tsagera bukata ta samun makudan kudade.
Ga kirkirarriyar gwagwarmayar nan ta Boko Haram wacce a ke amfani da sunanta a na ruguza jihohin Yobe, Maiduguri, Kano, Kaduna, da wasu jihohin Arewa.
An yi amfani da sunan Boko Haram din an jibge sojoji a cikin gari su na ta yiwa mata fyade, su na wulakanta mutanen da ba su ji sun gani ba. An kafa shingen sojoji a kowanne sako da lungu. A irin wannan hali, idan mu ka yi shiru, mun ci amanar alkalami, baiwa da hikimar Allah.
Wannan shi ne yanayi mafi tashin hankali, shi ne yanayi na firgici, shi ne yanayi na zulumi da fargaba.
Masifu sun mamaye mu, sun yi mana kawanya, duk dai don a cimma wata boyayyiyar manufa. Allah ya tseratar da mu daga cikin wannan bala'I wanda mun shaidi farkonsa amma ba mu san karshensa ba.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment