Mai
karatu a wannan makon, wannan shafi zai ta¬o al’ada ne, domin ya na daga cikin
muhimman abubuwan da su ka bambanta mutum da dabba, shi ne al’ada.
Idan ka ga wata al’umma wacce a ka ce ba ta da al’ada, babu makawa kawai ka
bugi kirji ka ce rayuwar da mutanen da ke wannan al’umma su ke yi ba ta da
bambanci da ta dabbobi.
Kamar yadda ba a samun wata al’umma da ba ta da al’ada, haka kuma al’ada ma ba
zai yiwu ta samu ba har sai akwai al’umma. Dalilin haka ne masana ke cewa,
al’ada da al’umma kamar wayar salula ce da memori (memory card).
Al’adar al’umma ita ce ke nuna ya yarensu ya ke, ya su ke mu’amala da junansu,
menene kyakkyawa a wurinsu, menene mummuna a wurinsu. Wadannan na daga kadan
daga abubuwan da ke bambanta wannan al’ummar da wacccan al’ummar.
Kowacce al’umma na gane daya daga cikinta ne ta hanyar al’ada. Ba sai ma mutum
ya yi Magana ba ne kawai za a gane daga inda ya ke, daga yanayin sanya tufafi
ma kadai al’ummuu na iya bambance na su da wadanda ba na su ba.
Idan ka ga mutumin yankin Neja Delta sanye da tufafi, zabgegiyar hular malfa ta
isa ta bambanta shi da Bayaraben Ikko wanda ke sutura da leshi. Haka kuma idan
ka ga asalin bahaushen Arewa ya zubo babbar riga da hular kube, shigar ta isa
bayani.
A wasu lokutan kuma mai wata al’adar na iya sa suturar wata, abun da ke bayyana
hakikanin inda ya fito shi ne ya yi furuci, da zaran ya yi, tsamin bakinsa ko
kuma tasirin yaren al’adar ba zai bar shi ya yi furuci irin na wani ba.
Kafin zuwan turawan mulkin mallaka Afrika (musamman wannan kasar ta mu ta
Nijeriya), akwai wasu al’adu wadanda a ke yi, amma sakamakon karfa karfa,
bature ya dushe wadannan al’adun, ya maye gurbinsu da na shi.
Kamar misali; yanayin auratayya a wancan lokaci (na kafin zuwan Bature) al’ummu
da yawa a tsarin aurensu shi ne su na bayar da ‘ya ‘yansu mata tun a lokacin da
a ka haife su. Idan yarinya ta balaga ta ce ita ba ta so, sai iyayenta su
tsangwame ta, idan kuma namijin ne ya ce ba ya so, sai dai ya tattara
komatsenshi ya bar garin. Irin wannan al’ada ta yi kaurin suna a tsakankanin
mutanen garin Chawai da ke Zariya.
Su kuwa mutanen tsibirin Nuba (nuba hills) a al’adarsu bai haramta ba namiji da
mace su sadu ba tare da aure ba. Mace ta na iya zuwa ta kwana a gidan saurayin
da ta ke soyayya da shi. Irin wannan al’adar ta dace da wacce mutanen Ashanti
ta kasar Ghana ke yi, amma su a al’adarsu, namiji kafin ya yi aure, kanwarsa ko
wata ‘yar danginsu ce za ta koya mishi yadda a ke saduwa da mace, (wai) don kar
ya janyo musu abun kunya.
Haka kuma mace na iya saduwa da saurayin da ta ke so. Sai dai su al’ummar
Ashanti, idan mace ta yi ciki a wajen gidan aure, hukunci kisa ne a kanta. Idan
mace ta yi aure a Ashanti na kasar Ghana, ta haifi mata tagwaye, dukkansu sun
zama kadarorin sarki, ma’ana za a lissafa su cikin jerin matan Sarki, sai dai
idan mahaifiyar tagwayen sun hada jini da sarkin.
Aure a al’adar Kanuri, wani samfurin aure ne mai cike da al’ada, tun kafin
zuwan turawan mulkin mallaka, auren Kanuri aure ne mai tsadan gaske da cin kudi,
idan ka san ba ka da dukiya mai tarin yawa, kar ma ka fara tarbo ma kanka auren
‘yar Kanuri.
A al’adar Kanuri, idan mutum ya auri mace kuma ya gano cewa shi ne na farko da
ya fara saduwa da ita, su kan hada gagarumin buki, sannan akwai wani kaso na
tukuici da zai kai gidansu amaryar. Idan kuwa ango ya gano akasin haka, shi ne
ya ke fasa tukunya a kofar gida. Auren budurwa a al’adar Kanuri shi ne mafi muhimmanci
da tsada, fiye da na bazawara.
Dukkan wadannan al’adu da na kawo sun fuskanci sauye sauye bayan zuwan
Bature ta hanyar gabatar da na shi al’adar wacce ya ke ganin ita tafi dacewa da
mutanen da ya zo ya taras a Afrika.
Wannan abu da turawan mulkin mallaka su ka yi babban kuskure ne, wanda a
ilmance ya sa¬a. saboda a ilmin zamantakewar jama’a, duk mutumin da ke ganin
cewa al’adarshi ta fi na wani, wannan mutumin a na mishi kallon wanda bai san
me a ke nufi da ‘al’ada’ ba. Haka kuma wanda ya ke ¬oye al’adarshi ya na jin
kunyan a danganta shi da al’adar, shi ma wannan bai san me a ke nufi da
‘al’ada’ ba.
Matsayar masana ilmin zamantakewar jama’a ita ce; babu wata al’ada da ta fi
wata a duniya. Dukkan al’adu su na da matsayi da tasiri.
A dai dai lokacin da ka ke ganin al’adarka ita ce mafificiya, a wurin wasu
al’ummun kuma yanayin gudanarwar wannan al’ummar taka shi ne mafi kaskanci.
Abun nufi a nan kawai shi ne al’adu su ne al’umma, don haka al’umma da kansu ne
za su tantance tsakanin mai kyau da mummuna a wurinsu, sannan su samar da tsare
tsare na yadda rayuwarsu za ta kasance. Hatta dakushe hasken al’adu da bature
ya zo ya yi, wauta ne da kuskure babba, cin zali da danniya, kuma ya sa¬a ma
tsarin dan adamtaka. Mu hadu mako mai zuwa
No comments:
Post a Comment