Saturday, 11 April 2015

ILLOLIN BANGAR SIYASA DA RIKICIN ZABE GA MATASA

Tabbas matasa na da muhimmancin gaske a kowacce al’umma, tasirinsu ya fi gaban a zura ido kawai ga al’amura ko yanayin yadda su ke gudanar da rayuwa. Wajibi ne da ya hau kan al’umma kan yin tattalin rayuwar matasa, samar da hanyoyin shigar da saqonnin abubuwa masu kyau don su siffantu da su, haka kuma a yi musu bayanin illolin abubuwa marasa kyau don su qaurace musu.
            Duk wata qasa da ta ci gaba a wannan duniya, idan ka waiwaiyi sirrin da ke tattare da samuwar wannan ci gaba, za ka ga a hannun matasansu ya ke. Saboda basu yin sakaci a fannin kulawa da rayuwar matasa.
            Haqqi ne babba wanda ya rataya a wuyan iyaye da su kasance mataki na farko a inda ‘ya ‘yansu za su koyi tarbiyya, mu’amala da mutane, kiyaye dokokin qasa da oda, kaucewa ayyukan barna da sauransu.
            Idan iyaye su ka gaza aikata hakan ga ‘ya ‘yansu, babu tantama a dai dai lokacin da yaron ya kai shekarun girma (Matashi) ya fara mu’amala da wasu abokai a waje za su koya mishi dukkan dabi’un da su ka ga dama. A wasu lokutanma ba sai sun koya mishi ba, yanayin mu’amala a tsakaninshi da su ne zai sa ya riqa kwaikwaiyon yadda su ke tafiyar da rayuwarsu a hankali har ya gina dabi’a.
            Wannan ya nuna cewa haqqin iyaye ne, kuma ikon kiyaye ‘ya ‘ya daga fadawa hadurran kwaikwayon halayen banza a waje na hannun iyayen ne. wanda idan a ka samu kaso 60% cikin 100% su na sauke wannan nauyi, za a ga chanji.
            Qasashen da su ka ci gaba din nan, doka ce mai qarfi wacce ta tilasta iyaye a kan tarbiyyar ‘ya ‘yansu. Har ma idan iyayen ba su iya yi ba, sai hukuma ta dauki wannan babban aiki, saboda fahimtar irin hadarin da ke tattare da barin matasa cikin halin rashin bambance kyakkyawa da mummuna.
            A qasashen Afrika, sai ya kasance kaso mai yawa na iyaye babu ruwansu da halin da ‘ya ‘yansu za su shiga idan har basu dauki nauyin kula da tarbiyyarsu ba. Haka kuma a wannan yanki namu na Afrika, iyaye da dama (sai dai kadan) ba su wani taka  rawar a zo a gani wurin hobbasa kan ‘ya ‘yansu su yi karatu.
            Halayen banza da aikata duk wani aiki da zai cutar da mutum ko ya janyo asarar dukiya ya na da alaqa da jahilci. Saboda shi jahilci babu abun da ya ke umurtar qwaqwalwa ta aikata face son rai da aiki ba tare da tantancewa tsakanin mai kyau da marar kyau ba.
            Wannan shi ne dalilin da ya sa baragurbin ‘yan siyasa, wadanda ba burinsu ganin ci gaban Nijeriya ba, su ke amfani da matasa wurin cimma mummunar manufarsu ta aika aika. Su ne su ke ba matasan makamai da qwayoyi.
            Daya daga cikin abun da ke tashe a tsakankanin matasa a Nijeriya shi ne bangar siyasa da rikici. Wannan al’amari ya na da matuqar hadarin da idan ba an magance shi ba ne, lallai ba zai taba yiwuwa a mori dimokradiyya ko wanzajjen zaman lafiya ba.
            A al’ummun da su ka ci gaba ba qaramin aibu bane a kira mutum da dan bangar siyasa ballantana kuma daya daga cikin masu hura wutar rikicin siyasa, amma a Nijeriya wannan ba komi ba ne. Wannan bangar siyasa ta bambanta da asalin ‘yan sara – suka da mu ke da su, da ‘yan kalare da ‘yan daba.
            Duk inda a ka kira wadancan sunaye, musamman a garuruwan Bauchi, Kano da Gombe, suna ne wanda ya shafi matasa masu ayyukan rashin mutunci, rashin da’a da keta haqqoqin al’umma.
            Zaben shekarar 1999, wanda tsohon janar, Olusegun Obasanjo ya lashe. Sai dai tun a wannan lokaci ne ya kamata gwamnati ta tashi tsaye a kan rikicin zabe da bangar siyasa a tsakankanin matasa. Wannan irin mummunan dabi’a ta ci gaba da faruwa har a zaben shekarar 2003 da a ka yi. Maimakon a samu sauqe sai dai ma a ka yi ta samun qaruwar dabi’ar bangar siyasa da rikicin zabe ga matasa.
            ‘Yan siyasa masu mugun nufi a lokuta da dama su na aiki da matasan ne wurin sace akwatunan zabe, kai farmaki, da qone - qonen da su ka sabawa shari’a.
            Yanayin da ke fuskantarmu,  bisa la’akari da gabatowar babban zaben shekarar 2015, alamu na nuna matasan da ba su da ruwa da tsaki da da kalare, daba ko sara – suka akwai yiwuwar su fada ma irin wannan mummunan aiki na bangar siyasa da rikicin zabe.
            A lokacin da a ka yi zaben fid da gwani na jam’iyyu a Nijeriya, an samu rahotannin yadda wasu ‘yan siyasa a jam’iyyun su ka yi amfani da matasa wurin tayar da hankula domin kawai su yi qaurin suna.
            Ya kamata ne matasanmu su hankalta, su gane cewa bangar siyasa da rikicin zabe babu wani alheri da su ke haifarwa, sai dai sharruka birjik.
            Rahotanni sun adana cewa a rikicin zaben shugaban qasa da ya auku a watan Afrilun 2011 ya yi sanadiyyar rasa rayuka sama da 800, kamar yadda hukumar kare haqqin bil’adama su ka bayyana. Wadanda su ka mutu din an kashe su ne cikin kwanaki uku a jihohin arewa 11, wanda a kasha 90 na kashe – kashen matasa ne su ka aikata, haka ma rikicin zaben matasa ne su ka tayar.
            Zaben shekarar 2011 da ya gabata ya tafi ya bar baya ta qura, bilhasali ma ba a taba yin zabe wanda a ka zubar da jinni kamar shi ba. An tarwatsa mutane daga muhallinsu, wasu sun rasa iyaye da ‘yan uwa. Hukumar bayar da tallafin gaggawa ta shaida cewa sama da mutane dubu 65,000 ne su ka bar gidajensu sakamakon rikicin.
            Idan matasa su ka hankalta ta hanyar qauracewa bangar siyasa da rikicin zabe, tabbas baragurbin ‘yan siyasa da basu son zaman lafiya a Nijeriya ba za su kai ga cimma burinsu ban a zubar jinin mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.
            A matsayinka na matashi, ya kamata ne ‘yan siyasa su taimake ka wurin gina rayuwarka, a samar da ayyukan da matasa za su yi bankwana da zaman banza, a samar musu guraben karatu a makarantun da mu ke da su; wannan shi ne aikin gina rayuwar mutum ba a bashi makami da qwaya ba. Makami da qwaya sai dai rusa rayuwarka, ya zama ba ka da fata nagari ga kanka da al’ummar da ka ke tare da su. Mu hadu mako mai zuwa!
           
             
             

No comments:

Post a Comment