Saturday, 11 April 2015

ABUN DA KE HANA MUTANE NASARA A RAYUWA



Idan da a ce za a bani zabi a ce wannan rubutun shine rubutu na karshe da zan yi a rayuwa na a wannan filin, kuma an bani damar yin rubutu akan wani al’amari guda daya kacal, babu makawa akan wannan abun da ke hana da yawan mutane nasara a rayuwa zan yi, kuma ya ke dankwafe su wuri daya.
            Zan zabi yin haka ne kawai saboda la’akari da irin dabi’ar mutanenmu da kuma halayyansu akan fahimtar nasara a rayuwa. Idan ma da za a ce na ba mutane shawara akan wani abu, lallai ba zai wuce wancan batu ba. kodayake, wannan wani abu ne wanda gabakidaya duniya ke fama da shi, amma mu namu ya yi yawa.
            Watakila wani ya shiga mamakin me na ke son bayyanawa, ko kuma ma wani yace me na ke nufi ne?, muhimmin abu na ke nufi, domin kuwa babban abun da ke hana mutane nasara a rayuwa shine rashin sanin DALILI.
            Da yawan mutane su na kuskurewa a abubuwan da su ka sa a gaba sakamakon rashin sanin muhimmancin DALILI. Shin kana iya tuna wani muhimmin al’amari wanda ka sa a gaba a rayuwarka, wanda ka dauki matakai domin ganin wannan al’amari ya tabbata?. Amma kuma sai daga bisani ka fara yiwa kanka tambaya, kana tantamar anya wannan al’amari mai yiwuwa ne kuwa.
            Dukkanin dan adam na da wani abu wanda ya ke son ya cimma a rayuwarshi, wanda zuciyarshi ne ta wanzar mai da kaunar aikata wannan abu. A kullum mutane marasa adadi ne su ke shiga tsaka mai wuyar kudurin aiwatar da wani muhimmin abu, wani lokaci wanda zai kawo canji ga rayuwarsu.
            Irin wadannan abubuwa su kan hada da son daina shan taba (sigari), neman aiki, fara kasuwanci, neman hanyar daina mu’amala da miyagun mutane, tsara hanyoyin wanzajjen rayuwa cikin koshin lafiya, kiyaye gaskiya, rikon amana. Tabbas da yawan mutane burinsu bai zarce kwanaki ko awanni ya rushe, su koma tamkar ba su yi wannan kuduri ba, saboda tunaninsu bai fadada ba, sun tsuke shi a wuri guda.
Mai karatu!, matukar za ka yi amfani da wannan shawara, babu makawa za ka ga canji a dukkanin abun da ka sa a gaba. Kowanne abu a rayuwa ana cin nasara akanshi ne ta hanyar sanin dalilin aikata shi. Duk kuwa abun da aka surfafeshi ba tare da ayyanannen dalili ba, ko ya kafu zai rushe saboda ba a san don me ake yi ba.
Yawancin al’amuran mutane su na bin kyale kyale ne ko kuma abun da zuciyarsu ta bijirar musu na dan wani lokaci, ko kuma sha’awa, ko kuma ganin wasu na aikatawa, sai wannan ya rinjayesu su kuma karfafa kawunansu akai.
Rashin sanin dalilin aikata abu yana saurin ruguza komi da mutum ya shirya aikatawa. Zan bayyana wasu matakai wadanda idan mutum ya yi nazarinsu, zai fahimci inda na dosa.
Matakin farko shine mutum ya kasance ya sanyawa kanshi RA’AYIN yin abun da yake son aikatawa. Idan kasuwanci ne, aure ne, ko kuma karatu ne. misali, a ba dalibi gurbin karatun karatun kimiyya, ba zai taba ganin fa’idar karatun ba idan bai da ra’ayin yi.
Sai mataki na biyu kuma mutum ya san DALILIN da ya sa yake son aikatawa. Ka yiwa kanka wannan tambayar, shin menene dalilin da ya sa ka ke son aikatawa?, me zai biyo baya idan ba ka yi nasara ba?, wannan abu da ka ke son aikatawa zai iya cutar da mutanen da kake tare da su?, idan ka yi nasara, ya rayuwarka zata kasance?. Don haka dole ne sai ka san dalilin da ya sa ka yi ra’ayin aikatawa. Idan har ka kasa samarwa kanka dalilin kowanne mataki da za ka dauka, akwai tsammanin rashin yin nasara.
Ba wai kawai ginuwa akan ra’ayi  da kuma sanin dalilin aikata abu ba. babban abun lura wanda kuma ya ke da muhimmancin gaske, shine mutum ya adana a zuciyarshi ba tare da ya manta ba ko da na dakika guda cewa yana da dalilin matakan da yake dauka a abun da yake aikatawa.
Na san wanda ya fahimci inda na dosa zai gano bakin zaren bayanin, domin kuwa wani abu ne wanda yake a fili kuma mu ke rayuwa a cikinshi yau da kullum, ba zai yiwu mu guje daga gareshi ba, mafi kyautuwa shine mu yi aiki da shi domin samun nasara a al’amuranmu, shine sanin DALILIN da ya sa za mu aikata abu. Ruwan alkalamina ya kare, sai na yi sabon zubi.

No comments:

Post a Comment