Saturday, 11 April 2015

Nazarin Kalmar 'SO'




Na karu matuka a makon da ya gabata yayin da na ke sauraron Farfesa Peter Kreeft, wani farfesan falsafa a kwalejin Boston.
Farfesan hazikin masani ne wanda ya ke bayani dai dai gwargwadon fahimtar daliban Falsafa, har ma da sauran masu neman haske.
Ya yi jawabi ne a Ikhlisiyyar (Coci) wani gari dangane da 'Soyayya wacce Allah ke kimtsawa zukata', daga farko har karshen jawabin Farfesa Kreeft ya yi ta kafa hujjojin hankali ne dangane da 'Soyayya'. Ya kuma bambance tsakanin 'Soyayyar da Allah ya kimtsa a zukata', da 'Soyayyar da mutum ya cusa ma kanshi'. Dalilin wannan nazari na Bafalsafe Kreeft ne na tsunduma tunani mai zurfi dangane da Soyayya.
Abun damuwa shi ne yadda a ke sarrafa kalmar 'SO' a wannan zamani na mu. Idan za ka bi mutane daya bayan daya ka na yi musu tambaya dangane da Soyayya, za a ba ka hadin kai wurin amsa tambayoyin amma fa za ka tarad da amsoshi masu sarkakiya.
Ka natsu da kyau, sai ka yi nazarin kalamai irinsu "Ina sonki", "Ina son matata", "Ina son Mota ta", "Ina son Barcelona", "Ina son Alewa", da kuma "Na tsunduma a cikin soyayya". Dukkanin wadannan kalamai su na iya daidaita wurin furuci amma kuma ba dole ma'ana ta zo daya ba. "Soyayya" wani fanni ne na rayuwar yau da kullum. Wasu na rasa rayuwarsu sanadiyyar So, wasu kuma na yin rayuwar din din din ne a cikinshi.
Gabakidaya kamfanonin wallafa na mawaka da masu hada katin soyayya da gaisuwa, su na cin riba ne sakamakon wanzuwar Soyayya.
Dattijon masanin falsafan nan, Aristotle ya zayyana salon soyayya a cikin falsafarshi ta 'Nicomachean Ethics'. Babban mahangar littafin da alkiblarshi shi ne kokarin fassara ma'anar 'Farin ciki'.
Aristotle ya ce "Idan a na batun soyayya, toh sai mutum ya na son kanshi kafin ya iya son wani." Watakila wasu, su ga ba haka ba ne. {ila ma wani ya ce Son rai Aristotle ke koyar da mutane.
Abun lura a nan shi ne, ba wai son rai fa Aristotle ke magana a kai ba. A'a, mutum ya san darajar kanshi ta hanyar kula da taka tsan-tsan ta haka zai iya kiyaye daraja da matsayin sauran mutane.
            Saboda dai Bafalsafe Aristotle ya wanke kanshi daga zargi, sai ya ci gaba da cewa matukar ‘son kai’ zai sa mutum ya tattara dimbin dukiya ya kuma yi danniyan mulki har ta kai ya cutar da mutane, to ba irin wannan a ke nufi ba.
            A tsakanin masana falsafa ma akwai wata Baturiya mai suna Ayn Rand wacce ta bayyana ra’ayinta dangane da ‘Soyayya’.  Ita dalibar falsafan ‘Individualism’ ce ba fannin makarantar Aristotle ba. a wani tattaunawa da a ka yi da ita a shekarar 1964, ga abun da ta ce dangane da soyayya: ‘Soyayya ba dole sai mutum ya fara da son kanshi ba tukunna, wani abu ne wanda ko hanya bai hada da wannan ba. Idan akwai wani wanda ka ke so, to lallai za ka muhimmanta wannan wanda ka ke so din, sannan kuma soyayyarshi na iya tasirantuwa akanka ka canza’.
            Yanzu misali, ka na tafiya a titi lafiya kalau, sai kawai kwatsam wata budurwa ta fito daga wani shago, kawai sai ka kamu da sonta a ganin farko!, Me ke janyo irin haka?.
            Amsar a bayyane ta ke, ya danganta da yadda zuciyarka ta ke aiki. Idan da ma ka na zaman kadaici ne, to zuciyarka za ta kasance a bude wurin neman wacce za ta cike ma gurbi. Duk kuwa taka tsan-tsan din mutum da dauke kanshi, wajibi ne watan watarana sai zuciyarshi ta yi kicibis.
            Na san da yawan mutane, musamman a kasar hausa sun yi imanin cewa soyayyar da a ka fara ta farad daya ba ta daurewa, alhali kuma ba haka abun ya ke ba. sai dai samun irin hakan ya na da dan wahala.
            Za ka iya haduwa da wani, ka fara sonshi farad daya saboda wannan tanadi na zuciya dangane da irin wanda za ta yi soyayya da shi. Ta ya ya hakan zai yiwu, alhali ba ka taba yin magana da shi ba?. Eh, domin zai yiwu cikin tanadin zuciyarka akwai salon tafiya, fasalin magana, kallo da sarrafa idanu. Dadin dadawa kuma ma wannan na iya faruwa cikin sauki idan wacce ka gani din ta tuna ma ka wata masoyiyarka.
            Ya na da kyau mu fahimci cewa, duk wanda tanadin zuciyarshi ya fi karkata zuwa ga ado da kyawun fuska fiye da sauran muhimmin abubuwa, zai fi kowa saurin fadawa soyayya a ganin farko.  
Kowanne dan Adam ya na da irin tsarin rayuwa, tsarin da ke wanzuwa a cikin zuciya. Yanayin tasowar mutum, yarinta da muhallin da ya taso na iya yin tasiri a kan irin abokin soyayyan da zuciyarshi ke so.
            Zan kawo misalin yadda wani Mukhtar (wanda na tattauna da shi) ke son abokiyar soyayyarshi ta kasance;
1.       Ya zama iliminta ya zo daya da na shi, ko ba ta kai shi ba, ta kusa cimmai a fagen ilmi
2.      Kar ta kasance mai yawan surutu (saboda Mukhtar ya camfa cewa yawancin mata masu surutu, soyayya da su bai haifar da da mai ido).
3.      Ta kasance ta iya mu’amala da mutane (Saboda Mukhtar bai iya mu’amala da mutane ba sosai, kuma ya ji labarin ance abokin soyayya na tasiri akan dan uwanshi).
Duk wannan dogon bayani da na ke ta faman zayyanowa ina so ne na bayyana muhimmancin soyayya da kuma yadda ta ke da tasiri a zukatan ‘yan Adam. Za ka ga na wani ya fi na wani. Wasu ma sai ka yi zaton gabakidaya rayuwarsu babu abun da su ka iya sai soyayya. Wani kuma namiji ne amma da zaran ya ga mata sai ya fara sunkuyar da kai, saboda ya na tsoron ma su hada ido.
            Tuntuni na ke tunanin wai me ya sa a ka damu da soyayya ne?, ba zan fadi ko ‘A’ ba, kai ma ina so ne ka tsunduma cikin tunani ka gano me ya sa?. 
Mu hadu mako mai zuwa.


SHIN AKWAI AL’ADAR DA TA FI TASIRI?



Mai karatu a wannan makon, wannan shafi zai ta¬o al’ada ne, domin ya na daga cikin muhimman abubuwan da su ka bambanta mutum da dabba, shi ne al’ada.
            Idan ka ga wata al’umma wacce a ka ce ba ta da al’ada, babu makawa kawai ka bugi kirji ka ce rayuwar da mutanen da ke wannan al’umma su ke yi ba ta da bambanci da ta dabbobi.
            Kamar yadda ba a samun wata al’umma da ba ta da al’ada, haka kuma al’ada ma ba zai yiwu ta samu ba har sai akwai al’umma. Dalilin haka ne masana ke cewa, al’ada da al’umma kamar wayar salula ce da memori (memory card).
            Al’adar al’umma ita ce ke nuna ya yarensu ya ke, ya su ke mu’amala da junansu, menene kyakkyawa a wurinsu, menene mummuna a wurinsu. Wadannan na daga kadan daga abubuwan da ke bambanta wannan al’ummar da wacccan al’ummar.
            Kowacce al’umma na gane daya daga cikinta ne ta hanyar al’ada. Ba sai ma mutum ya yi Magana ba ne kawai za a gane daga inda ya ke, daga yanayin sanya tufafi ma kadai al’ummuu na iya bambance na su da wadanda ba na su ba.
            Idan ka ga mutumin yankin Neja Delta sanye da tufafi, zabgegiyar hular malfa ta isa ta bambanta shi da Bayaraben Ikko wanda ke sutura da leshi. Haka kuma idan ka ga asalin bahaushen Arewa ya zubo babbar riga da hular kube, shigar ta isa bayani.
            A wasu lokutan kuma mai wata al’adar na iya sa suturar wata, abun da ke bayyana hakikanin inda ya fito shi ne ya yi furuci, da zaran ya yi, tsamin bakinsa ko kuma tasirin yaren al’adar ba zai bar shi ya yi furuci irin na wani ba.
            Kafin zuwan turawan mulkin mallaka Afrika (musamman wannan kasar ta mu ta Nijeriya), akwai wasu al’adu wadanda a ke yi, amma sakamakon karfa karfa, bature ya dushe wadannan al’adun, ya maye gurbinsu da na shi.
            Kamar misali; yanayin auratayya a wancan lokaci (na kafin zuwan Bature) al’ummu da yawa a tsarin aurensu shi ne su na bayar da ‘ya ‘yansu mata tun a lokacin da a ka haife su. Idan yarinya ta balaga ta ce ita ba ta so, sai iyayenta su tsangwame ta, idan kuma namijin ne ya ce ba ya so, sai dai ya tattara komatsenshi ya bar garin. Irin wannan al’ada ta yi kaurin suna a tsakankanin mutanen garin Chawai da ke Zariya.
            Su kuwa mutanen tsibirin Nuba (nuba hills) a al’adarsu bai haramta ba namiji da mace su sadu ba tare da aure ba. Mace ta na iya zuwa ta kwana a gidan saurayin da ta ke soyayya da shi. Irin wannan al’adar ta dace da wacce mutanen Ashanti ta kasar Ghana ke yi, amma su a al’adarsu, namiji kafin ya yi aure, kanwarsa ko wata ‘yar danginsu ce za ta koya mishi yadda a ke saduwa da mace, (wai) don kar ya janyo musu abun kunya.
            Haka kuma mace na iya saduwa da saurayin da ta ke so. Sai dai su al’ummar Ashanti, idan mace ta yi ciki a wajen gidan aure, hukunci kisa ne a kanta. Idan mace ta yi aure a Ashanti na kasar Ghana, ta haifi mata tagwaye, dukkansu sun zama kadarorin sarki, ma’ana za a lissafa su cikin jerin matan Sarki, sai dai idan mahaifiyar tagwayen sun hada jini da sarkin.
            Aure a al’adar Kanuri, wani samfurin aure ne mai cike da al’ada, tun kafin zuwan turawan mulkin mallaka, auren Kanuri aure ne mai tsadan gaske da cin kudi, idan ka san ba ka da dukiya mai tarin yawa, kar ma ka fara tarbo ma kanka auren ‘yar Kanuri.
            A al’adar Kanuri, idan mutum ya auri mace kuma ya gano cewa shi ne na farko da ya fara saduwa da ita, su kan hada gagarumin buki, sannan akwai wani kaso na tukuici da zai kai gidansu amaryar. Idan kuwa ango ya gano akasin haka, shi ne ya ke fasa tukunya a kofar gida. Auren budurwa a al’adar Kanuri shi ne mafi muhimmanci da tsada, fiye da na bazawara.
            Dukkan wadannan al’adu da na kawo sun fuskanci  sauye sauye bayan zuwan Bature ta hanyar gabatar da na shi al’adar wacce ya ke ganin ita tafi dacewa da mutanen da ya zo ya taras a Afrika.
            Wannan abu da turawan mulkin mallaka su ka yi babban kuskure ne, wanda a ilmance ya sa¬a. saboda a ilmin zamantakewar jama’a, duk mutumin da ke ganin cewa al’adarshi ta fi na wani, wannan mutumin a na mishi kallon wanda bai san me a ke nufi da ‘al’ada’ ba. Haka kuma wanda ya ke ¬oye al’adarshi ya na jin kunyan a danganta shi da al’adar, shi ma wannan bai san me a ke nufi da ‘al’ada’ ba.
            Matsayar masana ilmin zamantakewar jama’a ita ce; babu wata al’ada da ta fi wata a duniya. Dukkan al’adu su na da matsayi da tasiri.
            A dai dai lokacin da ka ke ganin al’adarka ita ce mafificiya, a wurin wasu al’ummun kuma yanayin gudanarwar wannan al’ummar taka shi ne mafi kaskanci.
            Abun nufi a nan kawai shi ne al’adu su ne al’umma, don haka al’umma da kansu ne za su tantance tsakanin mai kyau da mummuna a wurinsu, sannan su samar da tsare tsare na yadda rayuwarsu za ta kasance. Hatta dakushe hasken al’adu da bature ya zo ya yi, wauta ne da kuskure babba, cin zali da danniya, kuma ya sa¬a ma tsarin dan adamtaka. Mu hadu mako mai zuwa

NAZARIN KYAUTA DA ROWA



Mai karatu a wannan makon zan ta~o wasu muhimman abubuwa guda biyu, wadanda ke kishiyantar juna. Kuma dukkaninsu na da alaka da rayuwarmu ta yau da kullum.
            A da ban hankali na bai ta~a zuwa kan wadannan abubuwa ba, saboda ko kadan kwakwalwata ba ta salwanta min muhimmancinsu da kuma tasirinsu a rayuwa ba. Wasu lokuta baya mu na darasi, sai malaminmu ya shigo da batun ‘Kyauta da rowa’, ya yi mana dogon bayani (wanda shi a wurinshi ya takaita). Har ma ya sha alwashin in Allah ya yarda zai yi nazarin kyauta da rowa.         
            Kafin na ci gaba da bayani, akwai wani abu mai sarkakiya wanda ya kamata mu warware shi. Shin kyauta ko rowa a na yin gadonsu ne, ko kuwa koyonsu a ke yi?
            Wannan tambayar ba ta da wani bambanci da tsohuwar tattaunawar nan dangane da dabi’ar dan Adam, wanda wasu ke hakikancewa a kan cewa ai dabi’a tana tattare ne a cikin jininmu, daya ~angaren kuma su ka ce, a na koyon dabi’u ne a cikin al’umma.
            Idan mutum na da yawan kyauta, za ka ji hausawa na cewa ya na da jinin kyauta. Sai dai wannan Karin Magana kadai bai isa madogara gare mu ba, mu yanke hukuncin cewa ai in dai mutum ya hada jini da masu kyauta babu makawa shi ma zai zamo mai kyauta.
            Wannan rusasshen zance ne, idan za mu yi la’akari; misali akwai tagwaye (twins) wadanda a ka haifa a garin Kaduna. Sunansu Hasan da Husaini, tun bayan kwana bakwai da haihuwansu, sai mahaifinsu ya yanke shawarar zai raba su wurare daban daban a hannun kannenshi.
            Da a ka tashi sai a ka kai Hasan kasar Ingila, shi kuma Hussaini a ka kai shi garin Gombe. Har zuwa lokacin da su ka girma su ka fara aiki. Abun lura a nan shi ne, idan Hasan da ke kasar ingila ya taso tare da mutane masu ra’ayin turawa na cewa taimakon talaka kuskure ne, saboda idan yau ka taimaki talaka ba zai mike ya nemi na kanshi ba. Shi kuma Husainin ya taso a wurin mutanen Gombe, wadanda za su iya sadaukar da dukkan abun da ke cikin aljihunsu domin yin hidima ga bako, ko kuma mutanen da ke fito da abinci kofar gida a taru a ci.
            Wannan ya nuna mana a fili cewa Hasan zai koyo rowa matsananciya, shi kuma Husaini zai koyo yadda a ke kyautata ma mutane. Wannan dan gajeren misali kadai ya isa mu gane karfin ikon wurin da mutum ya taso ga halayyenshi, musamman halin kyauta ko rowa.
            Tun a rayuwarmu ta yau da kullum mu kan ga alheran da ke tattare da kyauta, haka kuma mu kan ga sharrrukan da ke tattare da rowa. Mutumin da ke da kyauta, ya kan zama mafi soyuwa a tsakanin mutane, sannan mutane ba za su aminta a hada kai da su wurin cutar da shi ba.
            Akasin haka ga marowaci. Idan mai gida (oga) ya kasance marowaci, babu makawa da yaranshi (ma’aikata) za a hada baki a halaka shi ko a gurgunta al’amuranshi. Saboda ai tsaro ba ya na nufin mai gadi da bindiga ba ne kawai, mafi girman tsaro shi ne tsaro wanda mutum ya samarwa kanshi ta hanyar mallakar zukatan wadanda ya ke tare da su. Idan kai mai arziki ne, amma ma’aikatanka ko da yaushe su na cikin matsanancin wahala. Kenan watan wata rana makiya za su iya ba mai dafa mishi abinci (kuku) guba ya zuba mishi don ya ci ya halaka.
            Sirrin cin moriyar rayuwa na tattare da kyauta. A wasu lokutan ma kyautar da mutane ke yi kanana su na ganinsu ba a bakin komi ba, amma wannan abun alheri zai ci gaba da binsu har ‘ya ‘ya da jikoki.
            Idan kuwa halin ka kenan rowan tsiya, wannan tabon na marowaci, ya yi ta binka kenan. Har ma idan a ka ci sa’a cikin ‘ya ‘yanka ko jikoki a ka samu wani mai halin kyauta, sai ka ji jama’a na cewa Allah sarki mahaifinshi ko Kakanshi marowaci, amma shi kuma mai kyauta.
            Abubuwa biyu ne masu karo da juna. Sai dai ya na da kyau mu gane cewa wadannan halaye guda biyu, al’umma na da hakkin koya wa mutum su. Idan mu ka kasance masu halin kyautatawa, ‘ya ‘yanmu da wadanda ke tare da mu za su taso da wannan hali. Shi ya sa masana halayyan jama’a da zamantakewa su ke cewa al’umma ne ke gina dabi’ar mutum. Mu hadu a mako mai zuwa
           
                              

ABUN DA KE HANA MUTANE NASARA A RAYUWA



Idan da a ce za a bani zabi a ce wannan rubutun shine rubutu na karshe da zan yi a rayuwa na a wannan filin, kuma an bani damar yin rubutu akan wani al’amari guda daya kacal, babu makawa akan wannan abun da ke hana da yawan mutane nasara a rayuwa zan yi, kuma ya ke dankwafe su wuri daya.
            Zan zabi yin haka ne kawai saboda la’akari da irin dabi’ar mutanenmu da kuma halayyansu akan fahimtar nasara a rayuwa. Idan ma da za a ce na ba mutane shawara akan wani abu, lallai ba zai wuce wancan batu ba. kodayake, wannan wani abu ne wanda gabakidaya duniya ke fama da shi, amma mu namu ya yi yawa.
            Watakila wani ya shiga mamakin me na ke son bayyanawa, ko kuma ma wani yace me na ke nufi ne?, muhimmin abu na ke nufi, domin kuwa babban abun da ke hana mutane nasara a rayuwa shine rashin sanin DALILI.
            Da yawan mutane su na kuskurewa a abubuwan da su ka sa a gaba sakamakon rashin sanin muhimmancin DALILI. Shin kana iya tuna wani muhimmin al’amari wanda ka sa a gaba a rayuwarka, wanda ka dauki matakai domin ganin wannan al’amari ya tabbata?. Amma kuma sai daga bisani ka fara yiwa kanka tambaya, kana tantamar anya wannan al’amari mai yiwuwa ne kuwa.
            Dukkanin dan adam na da wani abu wanda ya ke son ya cimma a rayuwarshi, wanda zuciyarshi ne ta wanzar mai da kaunar aikata wannan abu. A kullum mutane marasa adadi ne su ke shiga tsaka mai wuyar kudurin aiwatar da wani muhimmin abu, wani lokaci wanda zai kawo canji ga rayuwarsu.
            Irin wadannan abubuwa su kan hada da son daina shan taba (sigari), neman aiki, fara kasuwanci, neman hanyar daina mu’amala da miyagun mutane, tsara hanyoyin wanzajjen rayuwa cikin koshin lafiya, kiyaye gaskiya, rikon amana. Tabbas da yawan mutane burinsu bai zarce kwanaki ko awanni ya rushe, su koma tamkar ba su yi wannan kuduri ba, saboda tunaninsu bai fadada ba, sun tsuke shi a wuri guda.
Mai karatu!, matukar za ka yi amfani da wannan shawara, babu makawa za ka ga canji a dukkanin abun da ka sa a gaba. Kowanne abu a rayuwa ana cin nasara akanshi ne ta hanyar sanin dalilin aikata shi. Duk kuwa abun da aka surfafeshi ba tare da ayyanannen dalili ba, ko ya kafu zai rushe saboda ba a san don me ake yi ba.
Yawancin al’amuran mutane su na bin kyale kyale ne ko kuma abun da zuciyarsu ta bijirar musu na dan wani lokaci, ko kuma sha’awa, ko kuma ganin wasu na aikatawa, sai wannan ya rinjayesu su kuma karfafa kawunansu akai.
Rashin sanin dalilin aikata abu yana saurin ruguza komi da mutum ya shirya aikatawa. Zan bayyana wasu matakai wadanda idan mutum ya yi nazarinsu, zai fahimci inda na dosa.
Matakin farko shine mutum ya kasance ya sanyawa kanshi RA’AYIN yin abun da yake son aikatawa. Idan kasuwanci ne, aure ne, ko kuma karatu ne. misali, a ba dalibi gurbin karatun karatun kimiyya, ba zai taba ganin fa’idar karatun ba idan bai da ra’ayin yi.
Sai mataki na biyu kuma mutum ya san DALILIN da ya sa yake son aikatawa. Ka yiwa kanka wannan tambayar, shin menene dalilin da ya sa ka ke son aikatawa?, me zai biyo baya idan ba ka yi nasara ba?, wannan abu da ka ke son aikatawa zai iya cutar da mutanen da kake tare da su?, idan ka yi nasara, ya rayuwarka zata kasance?. Don haka dole ne sai ka san dalilin da ya sa ka yi ra’ayin aikatawa. Idan har ka kasa samarwa kanka dalilin kowanne mataki da za ka dauka, akwai tsammanin rashin yin nasara.
Ba wai kawai ginuwa akan ra’ayi  da kuma sanin dalilin aikata abu ba. babban abun lura wanda kuma ya ke da muhimmancin gaske, shine mutum ya adana a zuciyarshi ba tare da ya manta ba ko da na dakika guda cewa yana da dalilin matakan da yake dauka a abun da yake aikatawa.
Na san wanda ya fahimci inda na dosa zai gano bakin zaren bayanin, domin kuwa wani abu ne wanda yake a fili kuma mu ke rayuwa a cikinshi yau da kullum, ba zai yiwu mu guje daga gareshi ba, mafi kyautuwa shine mu yi aiki da shi domin samun nasara a al’amuranmu, shine sanin DALILIN da ya sa za mu aikata abu. Ruwan alkalamina ya kare, sai na yi sabon zubi.