Wannan shafi an samar da shi ne domin watsa rubuce rubuce na ilmantarwa da fadakarwa musamman wadanda su ka shafi IIlmin sanin halayyar dan Adam da zamantakewa (Sociology). Alqalamin shafin zai fi karkata ga rayuwa, musamman na matasa. Sunan shafin ya samo asali ne daga jaridar Leadership Hausa. Shafi ne wanda ke kawo rubuce rubucen marubuci Sulaiman Bala Idris (ISB DAURAWA) +2347036666850
Saturday, 17 January 2015
Babu arzikin da ya kai Ilmi
Da yawan mutane ba su san hakikanin ma’anan ilmi ba, don haka ne ma su ke kuskurewa wurin neman shi yadda ya dace. Hatta Allah ya ce ku sanni kafin ku bauta min. duk abun da ba ka san shi ba, ba za ka iya nemanshi ba, ballantana ka same shi har ka yi aiki da shi.
Ilmi shi ne neman sanin abun da ya shige ma mutum duhu. Wannan it ace takaitacciyar fassarar ilmi. Don haka ka neman sanin wani abu wanda ya shige ma dan Adam duhu zai iya faruwa ne kawai ga mutumin da Allah ya azurta da hankali, sannan kuma mutumin da ya iya sarrafa hankalinshi yadda ya dace.
Ilmi shi ne tushen dukkan alheri a wannan duniya. Ilmi na da kishiya wato jahilci, a duniya dole ne mutum ya kasance dayan biyu, ko dai mai ilmi ko kuma jahili.
Idan ka kasance daga cikin jahilai, ayyukanka wadanda su ka hada da mu’amala na yau da kullum da sauran mutane za su nuna jahilcinka a bayyane, sannan yanayin furucinka da motsinka ma jahilci zai tasirantu a cikinsu.
Shi kuwa wanda ya kebanta da ilmi, rayuwarshi za ta haskaka ta siffofi marasa adadi, zai ga tasirin wannan ilmin kamar yadda hasken wata ke tasiri ga duhun dare. Mutanen da ya ke rayuwa a cikinsu za su kauna ce shi, sannan za su girmama shi tare da daukaka ra’ayinshi fiye da na su.
Akwai wani mutum wai shi MATI ALJAN, mutum ne da bai san damansa da hagunsa ba (wato ba ilmin Arabi ba na Boko). Bayan wata ‘yar hatsaniya da a ka yi sai ya ke rantsuwa “Na rantse da Alkur’ani hizufi 90”, sai a ka ce mati ai Alkur’ani hizufi 60 ne, sai yace yanzu duk girman alkur’ani hizufi 60 ne?.
Dadin ilmi kenan, wannan wani babi ne na sanin ilmin addini kacokaf, amma shi Mati da girmanshi ga aure ga ‘ya ‘ya bai sani ba saboda jahilci. Alhali a makarantun Islamiyyoyi idan ka tarad da kananan yara ‘yan shekaru 7 zuwa kasa za su fadi maka Alkur’ani hizufi 60 ne.
Akwai karin wani misali na wani mutum (shugaba ne) ya na yiwa ‘yan kwana – kwana jawabi, ba shi da ilmi, amma kuma ya na da mulki, wannan mulkin ne ya ba shi daman ya yi jawabin kwantar da hankalin ‘yan kwana kwanan da mutane ke tsangwama. Cikin nasihan da wannan shugaba ya yi musu har ya na cewa ‘Ku yi ta hakuri, haka su Annabi Sani su ka yi ta hakuri da jama’a.’
Na kawo wadannan misalai ne don na sake fadada al’amarin jahilci ga mai karatu. Babu wani ado ko kwaskwarima da za a iya yiwa jahilci, idan mutum jahili ne dole ne a zantukanshi ta tabbata shi din haka ne.
Sannan kuma ba a iya siyan ilmi da dukiya, kuma ba a iya yiwa ilmi barazana da mulki ko mukami. Ilmi abu ne wanda idan mutum ya same shi, zai tasirantu a kwakwalwa, sannan ya bi jiki da furuci.
Cikin nasarorin da mai ilmi ke samu shi ne hikima. Ba kowanne zauna gari banza ba ne ke iya samun hikima. Hikimomin su na da yawa, akwai hikimar iya magana, akwai hikimar zurfin tunani, akwai hikimar iya mu’amala da mutane.
Da yawan ayyukan ta’addanci da a ke aikatawa a wannan duniyar su na kammaluwa ne da tallafin jahilai. Dalilin haka ne ma wasu malaman falsafa ‘Philosophy’ su ke cewa, duk al’umman da jahilanta su ka fi yawa, barnanta zai kazanta, sannan kuma babu fatan alheri ga wannan al’umma.
Kamar yadda karin maganar hausawa ke cewa ‘Itace tun ya na danye a ke lankwasa shi’. Al’amarin neman ilmi hakki ne mai girma da ya hau kan iyaye, wanda kuma idan ba su sauke ba, lallai a rayuwa za su kuka da ‘ya ‘yansu.
Idan da kowanne mahaifi zai dora dansa a turbar neman ilmi, lallai da kazanta da rashin tarbiyya sun karanta a cikin al’ummarmu. Amma abun mamaki sai ka ga mutum ya na fakewa da talauci a matsayin garkuwan da ya hana shi kai ‘ya ‘yanshi makaranta.
Idan ba ka iya namijin kokarin tura ‘ya ‘yanka zuwa ga neman ilmi ba, ka na fakewa da kangin talauci, lallai ya kamata ka farka daga wannan gurbataccen tunani ka fahimci cewa babu talaucin da ya kai jahilci, sannan kuma babu arzikin da ya kai ilmi.
Musamman ma yanzu yadda duniya ta ci gaba, hanyoyin neman ilmi sun sake fadada. ba dole sai an kashe makudan kudade ba wurin neman ilmi. Ci gaban kimiyya da fasaha sun zo da na’urori da hanyoyi saukaka binciken abubuwan da su ka shige ma mutum duhu.
A cikin dakinka da ‘yar kwamfuta za ka yi ta karance karance, idan ma ba ka da kwamfuta, zamani ya kawo mu da ‘yar wayar salularka za ka tsunduma yanar gizo ka yi bincike, ka yi ta karance karance a laburare iri iri na duniya.
Babu uzuri a wurin wanda bai nemi ilmi ba, saboda kofofin neman ilmin a wannan zamanin namu a bude su ke, kuma a yi shinge ga kowanne daya daga cikin wadannan kofofi ba, sai dai idan kai ne ka hana kanka. Ilmi zaki gare shi, kamar yadda jahilci ya ke da daci.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment