Saturday, 17 January 2015

ZABEN 2015: YIWUWAR DAWOWAR SOJA


KUri'u su na da tasirin gaske a dukkanin siyasar da asasinta ya ginu a kan turbar dimokradiyya. Sai dai, wani abu da ya kamata mu sani shi ne kuri'u ba su ne ke ayyana sakamako ba 100 bisa 100.
Kowacce kasa ta na da na ta hanyoyin cimma sakamako a matakin karshe. Misali, a kasar Amurka, komi yawan kuri'un da dan siyasa zai samu ba za su cika mishi burinshi na lashe zabe ba. Dole ne sai wannan shugaba ya na da goyon baya daga Yahudawa. Wadanda su ne ke juya akalar siyasar Amurka. Ko da kaso 70 na mutanen Amurka sun mika kuri'unsu ga dan takara, matukar bai da alaka ko kusanci da wadannan kebabbun Yahudu, sun yi a iska.
Haka nan a kasar jamhuriyar Musulunci ta Iran, tun kafin ma zaben, akwai majilisar koli ta malamai wacce ke tantance 'yan takara. Su a na su bangaren ma, idan wani mai tarihin matsala ya fito takara, su ka gano wani tabo da ya ke da shi wanda ya saba da tushen ka'idojin kasar. Tun a takun farko za a zabge shi kafin ma a yi ruwan kuri'u. Don haka duk wanda ya fado cikin 'yan takara to majalisar malamai sun aminta da shi.
Na kawo wannan ne da wadancan kasashe biyu mabambanta, don in yi sharar fage ga irin dabi'ar siyasa, zabe da kuma kuri'un al'umma.
Shin kuri'u na iya kawo mutum ga mukami a siyasance, musamman mukamin da ya fi kowanne a kasa ta shugaban kasa.
Zan takaita rubutun ne a iyaka Nijeriya, saboda la'akari da gabatowar zaben gamagari a 'yan kwanaki masu zuwa.
Maganar gaskiya ita ce, mutum bai bukatar a yi mishi dogon bayani kafin ya gane cewa akwai wasu hannaye da ke jujjuya al'amuran Nijeriya, ban da ikon shugaban kasa. Wannan wani abu ne da ke bayyane a fili.
Wadannan mutanen boye ne ke murda murdar ganin wanda su ke so ya samu mulki, kuma in ka zamo shugaba dole ka taka rawa yayin da su ka kada ganga. Kamar misali, tarihi ya nuna cewa kusan duk wani juyin mulki da a ka yi ko za a yi, sai ya kasance akwai hannun wasu masu fada a ji daga wajen kasar, kuma a waje a ke shirya shi.
Hatta daga cikin 'ya 'yan jam'iyyar PDP masu mulki, ba su san cewa ba tsagoron karfin jam'iyyarsu ba ne ke ba su damar ci gaba da mulkar Nijeriya. Shi ne ma ya sa su ke cika bakin sai sun mulki kasar na sama da shekaru 60 ba tazara.
Zaben da ke fuskantarmu a wannan sabuwar shekara, alamu na nuna zai yi wahalan gaske kuri'u su yi aiki. Za a buga zabe ne tsakanin wasu ra'ayoyi wadanda ke karo da juna.
A matakai na kasa-kasa, nan ne kuri'u ke iya taka rawa. Misali, a zabukan Kansiloli, ciyamomi, 'yan majalisun jiha, wasu wuraren ma har 'yan majalisun tarayya, wakilai, da gwamnoni.
Kamar yanzu da a ka samu gamayyar jam'iyyu su ka samar da jam'iyyar APC, za ka samu a kananan kujeru 'yan siyasar da a ka tsayar takara a jam'iyyar sun cinye, saboda guguwar Buhariyya da APC.
A wadannan matakan ma kuri'u su na aiki ne a lokacin da son ran masu ikon juya zabe bai yi karfi a kujerun ba. Ba wai tayar da jijiyar wuya ba, ko kafawa a tsare, ko da mutanen yankin za su mutu mafiya yawansu, sai an murgude.
Misali a nan, a zaben 2011 a jihar Kaduna, da bakin bindiga a ka ayyana marigayi Yakowa a matsayin Gwamna. A na gab da sanarwa, sai kawai sojoji su ka fara harbi a sama a lokaci guda kuma gidajen rediyo na sanar da dokar hana zirga zirga, sannan a ka sanar da sakamakon zabe. Kun ga kenan, wannan karfa karfa ta nuna cewa ba kuri'u ba ne su ka yi aiki, karfin ra'ayi da iko ne ya yi aiki.
Wannan zaben mai zuwa, hatta masu juya al'amuran kasar sun san wani babban al'amari na shirin faruwa. Na farko idan su ka aminta da guguwa da sabon yayi na APC, har su ka aminta da mika mulki ga Buhari (idan ya lashe zabe), kasar na iya fadawa yakin bangaranci, saboda tun yanzu wasu rikitattun mutane a yankin Kudanci sun fara sumbatun za a yi fito na fito idan Jonathan ya ruguzo.
Haka kuma idan Jonathan ya ci, mutanen Arewa babban abun da zai zo a ransu, shi ne an murgude za be ne, kuma ba za su yarda ba. Har ma da wasu daga mutanen yankin Yarbawa. Wannan zai haifar da bore da zanga zangar kin jinin gwamnati.
Idan har kasar ba ta fada ma yakin bangaranci ba, tsakanin Kudu da Arewa, za a yi bore. Wannan rashin gamsuwa daga mutane, da rashin gane bakin zaren daga masu juya kasar, idan sun ga dama sai su ingizo wani soja, wanda su ka kimtsa don gudun ko - ta - kwana, ya sanar da juyin mulki.
Mu na fatan ba za a yi yakin basasa ba. Haka nan mu na fatan ba za a yi magudI ba ballantana a yi bore. Mu na rokon Allah ya kiyaye rayukan jama'a. Wannan kawai hasashe ne! Mu hadu mako mai zuwa.

No comments:

Post a Comment