Saturday, 17 January 2015

Ya a ke nuna wa MUTUM kauna?


Mai karatu a wannan makon zan karkata sannan in dai dai ta don yin bayani dangane da kauna. Da yawan mutane, musamman hausawan da ba su san hausa ba (sai dai sun iya furuci da fahimtar harshen).
 Da yawa a na kuskure kalmomin So da kauna. Alhali wasu abubuwa ne mabambanta guda biyu, wadanda kuma kowannensu ke taka rawarshi tare da tasiri na daban a cikin zukatan mutane.
 So wani halitta ne mai karfi wanda ke ruruwa a cikin zuciya. A falsafance a na kallon So a matsayin wani al’amari wanda ke tattare da jin kai, kusanci, da kuma aminta da juna.
 Kusan gabakidaya addinai masu da’awar bauta sun tafi a kan hanyar tarbiyyantar da mabiya soyayyan juna. A na iya kallon So a matsayin wani abu wanda za ka nuna na damuwa ga wani (ko ga kanka) bisa zabin kanka.
 A kamus din fassarar kalamai na masana ilmin halayyar jama’a, sun yiwa Soyayya fassara da wani al’amari wanda ke kunshe da mabambantan abubuwa, daga ciki akwai yanayi, dabi’a, gamsuwa, don janyo hankalin wani.
 Saboda bambance bambancen da ke tsakanin al’ummu na yadda su ke kallon al’amura, shi ne dalilin da ya sa a al’adance kowa ya na tafiyar da rayuwarshi ne dai dai gwargwadon yadda al’adar garinsu ya shardanta.
 Za ka iya samun wasu gungun mutane wadanda su al’adarsu ce ta zo da halascin Mace ta auri mazaje da fiye da daya, kuma idan ma ba ta aikata hakan ba, kamar ta yi sabo ne.
 Auren Mazaje da yawa al’ada ce mai karfin gaske ga duk wata mace da ta tsinci kanta a kabilar Nayar da ke garin Kerala a Kudancin Indiya. Dole ne ta yi aure mazaje da daman gaske wadanda a al’adance su ke kira da Sandbanham.
 Wannan ya saba da wasu al’adu mafiya rinjaye a duniya, wanda dolen dole Mace a zamantakewar aurenta ta kebanta ga mutum guda, ba mazaje ba kamar waccan al’adar da na misalta.
 Ban da wannan, akwai misalai da yawan gaske wadanda ke nuni da bambancin yanayin tafiyar da rayuwa a al’adun al’umma. Idan dan wata al’ummar ya ga dabi’ar wasu al’ummun sai ya yi ta mamaki, ya na fadI a zuciyarshi ‘Anya mutane ne kuwa?’.
 Dalilin da ya san a kawo wannan misali na al’adu shi ne don na sake fito da maudu’I na fili. A dukkanin mafi yawancin al’adun duniya sun samu kansu ne dalilin kaunan juna. Duk mutanen da su ka wayi gari babu kaunar juna a tsakaninsu, ba da jimawa ba za su zama tarihi.
 Tunda a can baya na yi bayani mai tsawo dangane da Soyayya, kuma a dan iya abun da na iya bayyana da shi, na san a na iya fahimtar me Kalmar So ke nufi. Don haka ne zan yi kokarin fayyace bambance bambancen da ke tsakanin wadannan kalmomi masu kamanni da juna.
 Soyayya na kulluwa (a bisa mafi saukin fahimta) tsakanin jinsin maza da mata, wanda kuma a wasu lokutan idan tafiya ta yi tafiya, sai a kai ga aure.
 Ita kuwa kauna ta fi karfin nan, ta girmi a kira ta ko a kwatanta da wani abu wanda ke kulluwa tsakanin Maza da Mata. {auna ita ce rayuwa, kuma duk zuciyar da babu wadataccen kauna a cikinta, wannan matacciyar zuciya ce wacce kullum ta ke a cikin damuwa da nadama.
 A na fara samun tarbiyyar kauna ne tun a lokacin da a ka haifi jinjiri, sannan ne mahaifiya za ta fara tarbiyyantar da danta kauna, za ta kaunace shi ta yadda kukanshi cikin tsakar dare na iya zama sanadiyyan gushewar baccinta har wayewar gari.
 Saboda tsananin kaunar mahaifiya ga jinjirinta, zai yi fitsari da bayan gida a lokacin sanyi, amma kuma damuwarta ba wai ya bata ta ba ne, babban damuwarta kawai sanyi zai iya cutar da yaron. Sannan kuma komi tsananin sanyi haka nan za ta tsaftace fitsarin jinjirin da ruwa mai sanyi.
 Idan da a ce mutum zai rika zaunawa, ya natsu ya rika tunanin irin kaunar da mahaifiya ke nunawa danta (tun a lokacin da ya ke jinjiri) da babu wanda zai zama mai ciwon hassada, bakin ciki, munafunci, mugunta da duk wasu munanan halaye.
 Sannan kuma da mutane za su rika kulla zamantakewar aure bisa turbar kauna ba Soyayya zalla ba, da an yi bankwana da yawan mace – macen aure.
 A yau mutane su na wani irin zaman munafunci ne wanda kuma al’amari ne mai bakanta rai. Za ka ga mutum ya na yi maka faran faran, kuma ya rika rayawa tare da furucin shi mai kaunarka ne alhali kuma mu’amalarku ta na karya ta kasantuwar haka.
 Idan har ka na tare da mutum, ka na aikata wasu munanan dabi’u amma kuma ya kasa jurewa ya kwakkwafa ka don ka dawo ma turbar gaskiya, to wannan mutumi ko kadan ba ya kaunarka.
 Duk inda ba za a iya fede ma ka gaskiya ba duk dacinta a yayin da ka yi ba dai dai ba, wannan ba wurin zama ba ne, ko kuma shi ba abokin tafiya ba ne.
 Idan ka na kaunar mutum, a shirye ka ke kowanne lokaci ka fadi mishi gaskiya, idan ta kama ka ladabtar da shi don ya dawo hayyacinshi ko da kuwa hakan na iya zama sanadiyyan da zai fara jin haushinka, kai dai kawai ka yi don Allah.

No comments:

Post a Comment