Saturday, 17 January 2015

Barazanar Dokubo Asari: Bebebebebe…


A ‘yan tsakankanin nan, al’umman kasar nan sun fuskanci wasanni da hankali iri iri, sai da ta kai an daina wasa ma da hankalin, a’a kwakwalen mutane a ke bugawa tamkar kwalo daga hagu zuwa dama.
A haka nan yadda a ke kwallo da kwakwalen mutane, wasu sai kwakwalwarsu ta ci karo da dutse ta juye, sai ta yi ta diba ko yarda da kowanne irin tarkace aka zuba ma ta, ba tare da tantance tsakanin karya da gaskiya ba.
 Sauyin yanayi ya kawo mu wani zamani na rainin hankali, wanda karfin iko da mulki ba su tafiya dai dai har sai an sirka suda dabarun mallakar kwakwale da tunanin al’umma.
 Kuma zamani wanda a ke haifar da bala’I, masifa, tashin hankali, barazana, firgici domin samar da mafita ga wata matsala.
 Tun shekaru aru aru wasu kasashen duniya (musamman yammacin turai) su ke amfani da irin wannan lissafi domin cimma burinsu, misali da yadda kasar Amurka ta yi ta ruguza wasu kasashe domin bukasa tattalin arzikinta.
 Wannan bahaguwar falsafa ba ta samu wurin zama na musamman a Nijeirya ba, har sai wannan lokaci na mulkin farar hula wanda ke tafiya bisa turbar dimokradiyya. Tun mutane ba su fahimta, har ta kai ana fahimtar sabon salon, kuma kowanne shugaba idan ya zo, ya na zuwa ne da irin na shi rainin hankalin.
 Wannan dabara da wasa da hankali ne ya samar da mutane irinsu Alhaji Muhammad Dokubo Asari, wanda a ka kirkire shi a cikin dirkirarrun tsagerun yankin masu gadara da shimfidadden danyen man fetur a karkashin kasa (Neja Delta).
 Ga wadanda sunanshi kawai su ke ji, Dokubo Asari mutum ne wanda bai iya furuci ba ko miskala, hotunanshi babu abun da su siffantawa face rashin natsuwa da kamala.
 Mayaki ne (a ikirari) wanda bai san salo da dabarun fito na fito ba, shugaba ne (na ‘yan tsagera) wanda wakilcin shi ga wadanda yak e wakilta abun tir ne da Allah wadai.
 Ban dauki alkalami da niyyar hyiwa yankin Arewacin Nijeriya garkuwa ba, a’a sai don wayar da kawunan wadanda a ke son a zurma su cikin rami kuma a rufe.
 Samuwar Arewa da rashin samuwarta ya na a hannun al’umman yankin ne, idan sakaci da rashin sanin ya kamata ya sa su ka lankwashe hannuwa, su ka rungumi kaddara (kamar yadda kakanninsu su ka yi a ka yage Nijar daga Arewa), ai kuwa dole ne ta fashe a yi wasosonta.
 Barazanar ‘ya ‘yan biyuu-ahu irinsu Dokubo ba shi ne babban matsalar ba, su dai kumfar bakinsu kamar ‘yar nune ce wacce ke shaidawa al’umman yankin cewa sha-zumamu na sunsuno zaki.
 Mutum mai iyali, wanda shi ne shugaban gidanshi ba zai kuskura ya fadi wata magana wacce furta ta zai iya tarwatsa zaman lafiyan gidan ba. kai ko da kuwa rashin zaman lafiyan tsakanin gidanshi da gidajen makwabta ne.
 Ballantana kuma a ce shugaba, ba abin mamaki ba ne ga shugabannin yankin Neja Delta, tunda ba farau ba inda sakin layi ne a fadi zancen bur. Sai dai kalaman Alhaji Dokubo dole ne su girgiza mai hankali.
 Su girgiza mai hankali… da sunan wai ya tsoratar?. Haba dai, a matsayin shi dai na tsagera wanda ya yi babbar sa’ar shaidawa da kadaicin Allah, kuma ya yi imani da kasantuwar Annabi Muhammadu (S) Manzon Allah ne, cikamakin Annabawa.
 Amma da tsakar rana sai ga shi ya na cewa ‘na jimawa ina fadi, ina fada ne saboda samuwar ‘yancin mutane na kabilar Ijaw. Gaskiyar maganar kenan, kuma son ganin al’umman yankin Neja Delta da Igbo sun samu jin dadi da walwala. Saboda na hada jini da Igbo. Ni dan kabilar Ijaw ne, kuma Igbo ne, kuma dan Neja Delta. Babu ruwa na da damuwar wasu mutane can daban.’ A wata hira da jaridar Sun.
 A iyaka wannan tabargaza ta Dokubo, wanda shi a zatonshi burgewa ne da kekyashewa a tsageranci ya nuna. A bangare guda kuma bai san irin mummunan tabon da wadannan kalaman rashin dattako da natsuwa za su yi mai ba. mu dai a musulunci mun san Annabi (S) ya ce, Musulmi ‘yan uwan juna ne.
 Wannan ma ai bai ce komi ba tukunna, ga zantukanshi wadanda na nakalto kaitsaye daga jaridar Vanguard ta ranar 11 ga watan Mayun 2013. “Ina son jaddada cewa babu fa zaman lafiya da zai wanzu, ba wai a yankin Neja Delta ba, a’a a dukkanin Nijeriya, matukar Goodluck Jonathan bai ci zaben 2015. Sai dai idan kuwa Allah ya dauke rayuwarshi ne, wanda kuma ba mu fatan haka. Kamar yadda tsarin mulki ya zo da shi, Jonathan ya na da shekaru 8 cur wadanda zai yi a kujerarshi.”
 Mu a Arewacin Nijeriya, idan ka ji mutum na fadin irin wadannan soki – burutsu za ka ji ana cewa ya na zancen ‘yan tasha. Domin tasha can za ka je ka tarar da zauna gari banza, marasa tai do. Hatta ‘yan tashan cikin siyasa daidaiku ne za su iya runtse ido su yi ta soko maganganu haka.
 Sai dai kash!, mutumin fa da ya ke ta wadannan maganganu ba komin komai ba ne, kuma ba kowa ba ne shi, zaman lafiya kuma da ya k eta kurarin zai kare ai mu tuni a yankin Arewacin Nijeriya mu ka yi bankwana da zaman lafiya. Manyan jihohinmu da mu takama da su kirkirarrun tsagera ‘yan uwansu dokubo sun tarwatsa mana su da bama bamai.
 Misalin barazanar Dokubo, kamar mata ne. Kun san ai mata su na da abun mamaki a wannan duniyar, yanzun nan idan mace ta yi wani abun sai ka dauka ifiritu ne ke kimtsa mata a kwakwalwa. Su ne su ke kirkirar aljanu domin wani biyan bukatunsu.
 Wata mata ce wai aljanu sun kama ta, su kuma wadannan aljanun sikari (sugar) kawai ta ke sha sai su tashi. Yadda a ke gane aljanun sun karaso shi ne matar za ta fara wasu irin kalamai ta na fadin ‘bebebebebe’.
 Wai ashe aljanun na ta bebaye ne, don haka ko magana idan za su yi, sai dai su yi shi a tsamin baki. Ni ko har so na ke aljanun su zo, domin duk abun da su ke fadi kanzon kurege ne.
 Kawai watanni kadan sai a ka ce ai an samu maganin aljanun, amma sun ce sun daina cutar da ita, sai dai za ta rika bayar da magunguna ga mutane, ta na samun ‘yan silallan batarwa. *dariya*
 Ku saurara da kyau, wadanda kuma za su iya, su bibiya, za ku gano cewa Alhaji Dokubo Asari ya fara bebebebebe ne don a karshe ya siyar da magani, ko kuma ya riga ya ci ladar kuturu.      

No comments:

Post a Comment