A wasu lokutan idan na yi dubi ga yadda al'amura su ke gudana a Nijeriya, na kan shiga cikin matsanancin damuwa marar misaltuwa.Wasu abubuwan idan su ka faru, na kan cire rai na fid da tsammanin yiwuwar dai daituwar komi kamar yadda ya dace. Tambaya ma a nan ita ce, shin menene matsalar Nijeriya?
Mafiya yawan 'yan kasar nan da za ka tunkara da waccan tambayar, da gaggawa za su amsa da cewa Nijeriya ba ta da wani matsala wanda ya wuce shugabanni.Wannan kuma ba haka ba ne, ba don matsalolin mu a dai daiku ba, da babu yadda za a yi sama da shekaru 50 mu na rayuwa cikin tagumi da matsanancin kuncin rayuwa., ba tare da tasirin namu gazawar ba.Ina yin wannan rubutun ne cikin takaici da damuwa, zukatan kaso mafi rinjaye na 'yan Nijeriya sun mutu murus. Ba a mutuwar zuciya kadai abun ya tsaya ba, gurbatar tarbiyyar da ta mamaye mafiya yawan gidaje, ga yawan mutuwar aure ko ta ina.Idan har mu na son ganin gyara, babu makawa sai mun gyara kawunanmu, mu'amala da kyautata zamantakewa.
Cikin babban kuskuren da dan adam ke aikatawa a rayuwarshi akwai rashin daukar darasi, daga tarihi ko kuma daga wadanda su ka gaba ce shi.Shi amfanin tarihi, ba wai kawai a na labarta mana ba ne, ku saurara mu yi kuka ko mu saurara mu yi nishadI. Idan da darussan tarihi sun takaita ne kan wadancan ababe da na lissafa, da babu bukatar adana tarihi, sai a rika yin tsatsuniyoyi kawai yayin da a ke son sa mutum kuka ko dariya.
Abun da zai kona ma rai shi ne yanzu al'umman da mu ke rayuwa a cikinta ba ma wai wawantar da daukar darasi daga tarihi kadai ta yi ba, a'a mun ma raina tarihin ne, sannan mu kan yi girman kai ga darussan da ke cikinsa.Idan ka tsaya ka natsu da kyau, za ka fahimci wannan. Musamman ka yi nazarin zamantakewar da ke tsakaninmu a matakin daidaiku. Ko shekara guda cur ba a yi ba da wata amarya a garin Gaya ta barbada ma mijinta maganin bera a dan wake ya ci shi da abokai su ka bakunci lahira. Yarinyar ta koka da cewa auren dole a ka yi mata, shi kuma mahaifinta ya ce sam fa shi ba auren dole ya yi ma diyarsa ba.Kwatsam! 'yan kwanakin nan sai ga wani sabon rahoto daga kano inda amarya ta aika da mijinta lahira.Ina ganin wannan sai na cewa zuciya ta, wai wadanne irin mutane ne mu ke rayuwa da su? Komi alherin da ke tattare da wanda ka ke so ka aura ma diyarka, matukar ba ta so, alherin da ke cikin janyewa ya fi na zartarwa.
Matsalarmu ta biyu a wannan lokaci ita ce rashin hakuri. Kusan kamar kowa na makale ne a wuya ya na jiran dan uwanshi. Abun da bai kai ya komo ba, sai ka ga har an kai ga zub da jini.Masana a fannin sanin halayyar jama'a sun yi fashin baki da cewa, Duk al'umman da zubar da jini ya yawaita a cikinta, su cire rai ga tsammanin wanzajjen zaman lafiya.Matsalarmu mai muhimmanci ita ce ta iyaye, yanzu tabbas iyaye sun yi kasa a gwiwa wurin daukar dawainiyar 'ya 'yansu. Ta fuskacin ciyarwa, tufatarwa, ladabtarwa, da kuma ilmantarwa.Rashin daukar wannan nauyin na yara ne ke ci gaba da samar da yawa yawan 'yan ta'adda, zauna gari banza, da sauran miyagun halaye a cikinmu. Cikin matsalolinmu akwai tsoron gaskiya, wasu lokutan ma ta na biyo mu mu na gudunta. Musamman a wannan tsakanin na siyasa, lokacin da kowanne mai nema ya buga gangar takara.Saboda lalacewar harkar siyasa a Nijeriya, sai mutum ya tattara dukiya ta sata ko ba ta sata ba, sannan zai iya kai labari. Sai ka ga wani mutumin kirki ne, ya daya takara, amma don bai da nauyin da zai iya bin mu gida gida da sabulun naira 10 ko omon wanki, da naira ashirin ashirin, sai ka ga mun guje ma zabenshi.
A fili mu na iya fahimtar cewa mu ma azzaluman kawunanmu ne, saita al'amuran rayuwarmu ta yau da kullum, shi ne matakin magance matsalarmu muhimmiya.Mu yi tunani, wannan kwakwalwar an yalwata mu da ita ne, a ka cusa mana hankali wanda ya bambanta mu da dabbobi. Ba don mu fi so hauka Allah ya yi mana wannan Ni'imar ba, a'a sai dai don mu bambanta da su a zamantakewarmu. Mutunta juna, kiyaye darajar juna, kauna da tausayi. Tauna magana, yafiya da sauransu. Sai mun gyara kawunanmu sannan za mu iya gyara komi.
No comments:
Post a Comment