Mai karatu a wannan makon zan tabo fagen yanayin dabi'un mutane ne, wanda al'amari ne jai muhimmancin gaske a dukkan zamantakewa. Idan ka san yanayin dabi'ar mutanen da ka ke rayuwar yau da kullum da su, wannan zai ba ka damar kiyayewar aukuwar rashin fahimta da sabanin ba gaira ba dalili.
Shafin namu a yau zai yi bayani ne dangane da dabi'un mutane (personality). Akwai nazarori (theories) da daman gaske dangane da dabi'u (personality). Amma dai zan takaita ne ga yin bayanin guda daya watakila sauran zan yi bayaninsu nan gaba a hankali.
Akwai musayar ra'ayi da martanoni birjik dangane da dabi'a, an samu takaddamomi daga masana mashahurai tun a karnonin baya. Akwai wadanda ra'ayinsu shi ne cewa ita dabi'a a na gadonta ne daga jini, a na haihuwar mutum ne da dukkanin dabi'unsa. Yayin da wasu masanan ke ganin ai ko kadan ba haihuwar mutum a ke yi da dabi'unsa ba, koyonsu ya ke yi a hankali sakamakon tarayya da al'umma.
Wadanda ke da ra'ayin haihuwar mutum a ke yi da dabi'unsa su ne a ke kira da 'Nativist', su kuma wadanda ke da ra'ayin mutum na koyon dabi'u ne su ne a ke kira da 'Enviromentalist'.
A karkashin wadannan mabambanta ra'ayoyi guda biyu, wadanda a ke yiwa muhawararsu ta ke da 'Nature versus Nurture debate', akwai nazarori daban daban wadanda kowanne ke son tabbatar da gamsassun bayanai.
sai dai har wayau bayan dogon nazari akwai masanan da ke ganin ba zai yiwu mutum ya ce dabi'u na ginuwa ne ta bangare daya kawai, dole sai dai a kalli abun ta fuska biyu. Ta fuskacin haihuwar mutum da dabi'unsa da kuma ta fuskacin koyonsu bayan ya zo duniya.Nazarin da zan yi bayani shi ne TEMPARAMENT THEORY.Nazarin ya tafi a kan cewa gaba daya mutanen duniya dabi'unsu sun kasu gida hudu ne, ta na iya yiwuwa a samu wani da dabi'u duka hudun, amma dole sai an samu daya daga ciki wanda ya fi rinjaye. Wadannan dabi'u su ne:1.Sanguine personality. 2. Phlegmatic personality. 3. Choleric personality. 4. Melancholic personality
1. SANGUINE PERSONALITY: Masu irin wannan dabi'a sun kasance a cikin jininsu kwayoyin jan jini ya fi rinjaye (red blood). Za ka gansu su na yawan son taba mutane, su na son shakatawa, su na son harkokin more rayuwa, sun fiye surutu, su na saurin qulla abota, su na son su ga sun sa mutane annushuwa da farin ciki. A na gane wadannan masu dabi’a ne da siririyar fuska.
2. PHLEGMATIC PERSONALITY: Su kuwa wadannan su na da kwayoyin Phlegma da yawa a jininsu. Masu wannan dabi’a sun kasance mutane masu son zaman lafiya, saukin kai sannan su na da tsauri da kiyaye dokoki. Su na da zurfin ciki, ba su damu da harkokin more rayuwa ba, su na da yawan bautan Allah. Kamanninsu shi ne, su na da fuska zagayayye (rounded), fatansu na da laushi, su na da lebe cikakke, sannan hancinsu karami ne
.3. CHOLERIC PERSONALITY: Wannan dabi'a ce ta mutanen da ke da yawaitar kwayar jini yalo (yellow) a jikinsu. Yawancinsu shugabanni ne, jagorori ne, akwai aiki tukuru. Su na yawan karatu kuma su kan ci nasara a rayuwa. Ba su da yawan abokai, su na da kiyaye lokaci saboda komi na rayuwarsu tsare tsaren gaba ne. Ba su yin kwana kwana a mu'amala. Su na saurin yin fushi saboda akwai hadafin da su ke son cimma. Su a wurinsu morewa rayuwa bata lokaci ne kawai. Kamanninsu shi ne, ba su da tsayi, su na da fadin qirji da qosasshen jiki. Da yawansu na a cikin maza, kadan a ke samu daga mata.
4. MELANCHOLIC PERSONALITY: Mutane masu yawaitar bakin kwayar jini a jikinsu. Ba su yawan yin magana, su na da gaskiya, ba ruwansu da harkokin morewa rayuwa. Sun fi son aikata komi da kansu ba su son wani yayi musu hidima. A na gane wadannan ta hanyoyi kamar haka: idanuwansu na da duhu, sannan za ka ga kansu na wani lilu.
Ta na iya yiwuwa a samu wani mutum wanda za a ga jifa jifa daga cikin wasu dabi'unsa a dukkan hudun, amma maganar gaskiya ita ce, dole ne ya zama akwai inda dabi'un nasa su ka fi karkata.
Da fatan mai karatu ya gano wacce dabi'a ta fi rinjaye a rayuwarshi.
No comments:
Post a Comment