Friday, 2 December 2016

KIWON LAFIYA DA CUTUTTUKA A MAHANGAR ILIMIN KIMIYYAR ZAMANTAKEWA (SOCIOLOGY) 2

(Ci gaba daga makon da ya gabata)…
Ba a qarin haske dangane da bambancin alamomin cuta da bayyanarta kawai zan tsaya ba, akwai kuma wani qarin bayanin dangane da cuta, ciwo, da kuma rashin lafiya. Wadannan abubuwa guda uku bayaninsu shi ne ke kan gaba wurin bayyana bambancin da ke tsakanin kiwon lafiya da kuma sabon bangaren ilimi na ‘Medical Sociology’.

Idan a ka yi maganan Cuta (disease), a na nufin wani abu wanda ya sabbabawa gangan jiki ko wani bangare na jikin mutum sauyawa daga yanayin da ya kamata ya kasance na qoshin lafiya. A na gane cuta ne ta hanyar alamomin cuta ko kuma bayyanar cutan.

Ciwo kuwa ya na nufin wani hali da mutum zai tsinci kanshi na jin ba dai dai ba a jikinshi ko wani bangare na jikin nashi. Ciwo kan fara daga yanayin yadda mutum ke jin zafi, damuwa, da kuma rashin sakewa a al’amuransa na rayuwa. Babban bambanci a tsakanin cuta da ciwo, shi ne ita cuta ta kan bayyana kowa ya iya ganin alamominta ko bayyanarta a jikin mutum, idan an ga me fama da wata cuta a na iya cewa wancan cuta kaza c eke damunsa, saboda ga alamominta nan a tattare da shi. A yayin da Ciwo kuma wanda ke fama da ciwon ne kaDai ke jin raDaDin abin da ke damunsa. Ba dole ba ne sai ya zama ciwon ya bayyana ko an iya ganin alamominsa. Matuqar mutum zai riqa jin wani bangare na damunsa, shi kenan ya zama wanda ke fama da ciwo. Haka kuma don akwai cuta a tattare da mutum ba ya nufin mutumin nan na fama da ciwo ba ne.

Misali a nan, za a iya samun mutum da cutar qanjamau, zai yiwu alamomin cutar su bayyana na cewa ya na da cutar bayan an yi gwajin asibiti. Amma shi wannan mai cutar qanjamau ba ya jin wani ciwo a jikinsa, garau ya ke jinsa ba tare da wani raDaDi ba. Irin wannan ya na nuna cewa mutumin mai cutar qanjamau ya na fama da cuta ne ba ciwo ba. har sai zuwa lokacin da wannan cuta ta yi qamari tukunna, sannan ne mutumin zai tashi daga mai fama da cuta zuwa wanda ke da ciwo.

Haka nan a daya bangaren, za a iya samun mutum ya na fama da ciwo amma kuma babu wata cuta a jikinsa, ya na yiwuwa sosai ma. Sai ka ga an je asibiti an yi ta gwaje gwajen neman cutar da ke sa mutum jin ciwo a wani bangare na jikinsa amma a rasa samunta. Mutanen da ke fama da ciwon ‘Myalgic Encephalomyelitis’ sun a jin zafin ciwon, amma idan an gwada ba a ganinsu da wata cuta a tattare da su.

Bayan bayanin bambance bambance da ke tsakanin cuta da ciwo, akwai kuma bambanci tsakanin waDannan abubuwa biyu da RASHIN LAFIYA. Rashin lafiya ba kawai ya na nufin kasantuwar cuta ko fama da ciwo ba ne, haDakar duka biyun ne ke samar da rashin lafiya. Rashin lafiya ya na nufin wani yanayi da mutum zai tsinci kanshi a wani yanayi wanda ba zai iya gudanar da al’amuran rayuwarshi kamar yadda ya saba gudanar da su ba sakamakon wata cuta ko ciwon da yak e fama da shi.

Bambanci a tsakanin ciwo da rashin lafiya shi ne yanayin yadda al’amarin ya yi qamari. A yayin da mutum ke fama da ciwo shi kaDai abin ya shafa, saboda ya na iya fita kasuwa ko zuwa wasu uzurorinshi. Amma idan mutum na fama da rashin lafiya, hakan na iya shafar mutanen da ya ke rayuwa tare da su. Ba zai iya zuwa kasuwa ba, ba zai iya ci gaba da gudanar da al’amuransa na yau da kullum ba.

Sakamakon rashin lafiya na taba mu’amala a tsakanin wanda ba shi da lafiyan da sauran al’umma ne masana ilimin kimiyyar zamantakewa su ka mayar da hankali a kan kiwon lafiya da cututtuka. Saboda idan za a zura ido wata annobar cuta ta shigo ta addabi al’umma, zai zama yanayin tafiyar da al’amura sun samu matsala, ba kamar yadda a ka saba tafiyar da su ba.

Kamar yadda ya ke a ilimin na kimiyyar zamantakewa da sanin halayyar jama’a (Sociology), akwai mabambanta nazarori dangane da yadda mabambantan bangarori su ke kallon rayuwar zamantakewa. wadannan bangarori sun kasu gida uku, akwai; bangaren ‘Functionalism’, ‘Conflict’ da kuma ‘Symbolic Interactionism’.

Nazarin bangaren ‘Functionalism’ shi ne ya fara bayyana a ilimin, haka kuma shi ne ya fara yin nazarin kiwon lafiya da cututtuka. Wannan bangare ne wanda ke bayanin yanayin yadda gabadaya al’umma ke gudanarwa, ta yadda kowanne bangare na al’umma zai riqa bayar da nashi gudummawan domin a kai ga nasara, ba tare da wata tangarda ba. Alal misali, bangaren al’adu zai riqa gudanar da aikinshi na tabbatar da ci gaban al’ada da wanzuwarta, bangaren addini kuma zai riqa hada kan mabiya domin qarfafa imaninsu, bangaren tattalin arziki kuma domin samarwa al’umma da abin masarufi, haka nan sauran bangarorin, irinsu gidan sojoji, iyali, makarantu da sauransu.

A sakamakon wannan tushe na bangaren ‘Functionalism’ ne ya sa nazarinsu ke kallon kowanne mutum a matsayin mai amfani a cikin al’umma, kuma wanda a ke buqatar gudummawarsa domin al’umma ta ci gaba da gudanarwa yadda ya kamata. Idan mutum ya kasance ba shi da lafiya, za ta yiwu magidanci ne, kuma ma’aikaci a wata ma’aikata. Idan rashin lafiyan ya kwantar da shi, ba zai yiwu ya iya fita zuwa ma’aikatarsu ba, hakan na nufin kenan babu wanda zai nemowa Iyalin gidansa abin da za su ci. A dalilin haka wannan nazarin ya ke ganin cewa dole ne a Dauki mataki a kan al’amarin rashin lafiya.

A qoqarin ganin ya samar da wani nazari mai amfani, masani Talcott Parsons ya samar da wani nazari wanda ya kira da ‘Sick – Role’, wanda shi ne nazari mafi amsuwa a ilimin kimiyyar zamantakewa bangaren kiwon lafiya da cututtuka ‘Medical Sociology’. A nazarin Talcott Parsons, rashin lafiya wani abu ne wanda ba a so, wanda ya saba da qa’idar al’umma, ta yadda mutanen da su ke fama da rashin lafiyan za su riqa aikata wasu Dabi’un da su ka saba.

Duk da cewa Talcott Parsons ya gina nazarinshi ne ta hanyar dubi ga al’umman Yammacin Turai, amma za mu iya ganin amfanin wannan nazari na ‘Sick Role’ a al’ummunmu da ba chan din ba. ya kasa nazarin gida hudu, sannan hudun sai ya raba su gida biyu. Biyun farko ya yi bayani dangane da ‘yancin da mara lafiya ke da shi, biyun qarshe kuma ya yi bayanin nauyin da ya hau kan mara lafiya. Mu hadu mako mai zuwa.

Tuesday, 29 November 2016

KIWON LAFIYA DA CUTUTTUKA A MAHANGAR ILIMIN ZAMANTAKEWA (SOCIOLOGY) 1

A shekarun baya idan a ka yi maganan cututtuka a na danganta su ne kaitsaye da bangaren kiwon lafiya na kimiyya, rashin lafiya kuma a na danganta ta ne da wani bayyanannen alama a jikin mutum na cewa ya na fama da cuta. Haka kuma a wancan lokacin samar da magani ga cututtuka sun taqaita ne kawai ga shan magunguna ko kuma a yi wa mara lafiyan aiki (Surgery). Saboda wannan dalilin ne ya sa idan a na son fahimtar cuta yadda ya kamata, sai dai a yi nazarin wanda ke dauke da cutan.

Sakamakon ci gaba da a ka samu a fannin kimiyya da fasaha ne ya sa duniya ta ci qarfin tunanin mutane a kan kiwon lafiya da cututtuka. Wanda a da mutane idan ba su da lafiya, sai su alaqanta cutar da wani zunubi, ko kuma annoba, ko kuma wani laqani na Kakanni. Amma a sakamakon ci gaban, sai ya zama yanzu idan mutum ba shi da lafiya, ya kan nufi asibiti ne domin likita ya duba shi.

Wannan ci gaba da kimiyya da fasaha su ka kawo a fannin kiwon lafiya ne ya sa a qasashen da su ka habbaka (Developed Nations) ta kai ga an kawar da wanzuwar wasu cututtukan da a ke iya dibansu a lokacin mu’amalar yau da kullum. Sai dai a makwafin irin wadancan cututtuka, sai ya zama an samu wasu sabbin cututtuka wadanda su ne ke zama sanadin mutuwar al’umma. Irinsu cutar Kansa, Ciwon Suga, Qanjamau, da hadarin mota ko abin hawa, da dai sauransu.

Idan mutum ya kalli wasu daga cikin wadannan sababbin cututtukan da na bayyana a sama, zai iya fahimtar wani abu da su ke kamanceceniya da juna a kai, ko kuma in ce akwai wani sanadi guda daya da ke janyo su. Wannan sanadin shi ne yanayin yadda mutum ya ke tafiyar da rayuwarsa ‘Life – style’. Kenan harkar kiwon lafiya da cututtuka ta fi qarfin a taqaita ta ga wani bangaren ilimi guda daya. Dole ne a na buqatar a fahimci me ke janyo cututtukan, shin sababbin cututtukan nan na da alaqa da yanayin tunanin mutum? wanne gudummawa al’umma ke bayarwa ga mutum wurin kamuwa da cututtukan nan? Wanne tsarin rayuwa ya kamata mutum ya bi domin kaucewa wadannan cututtuka?

Wadannan tambayoyi da wasu da dama ne su ka samar da sabon fanni a ilmin zamantakewa da sanin halayyar jama’a (Sociology) wanda a ke yi wa laqabi da ‘Medical Sociology’. Ma’ana bangaren ilmin sanin halayya da zamantakewa da ke nazarin kiwon lafiya da cututtuka. Shi wannan bangare na ilimi aikinshi shi ne binciken yanayin yadda a ke gudanarwa da tafiyar da al’amarin kiwon lafiya, da kuma yadda a ke kallon cututtuka. Wannan bangaren ilimin ya na binciken alaqar likitoci da marasa lafiya, da kuma lokacin da zai yiwu a iya yi wa mara lafiya uzuri da lokacin da ba zai yiwu a yi mishi uzuri ba. sannan bangaren ilimin kan yi bincike a kan magunguna da tasirinsu, da kuma ra’ayoyin masana halayyar jama’a da zamantakewa dangane da kiwon lafiya da cututtuka.

Bayan samuwar wannan fannin, matsalar farko wacce tuntuni dama akwai ta a fannin kiwon lafiya da cututtuka ita ce ta samar da wani tsayayyen fassarar me a ke nufi da wadannan abubuwa; Lafiya da Cuta. Wanene mara lafiya? Wanene mai lafiya? Shin rashin lafiya na nufin samuwar cuta? Shin cuta na da bambanci da rashin lafiya? A sharar fage ga wannan bangare na ilimi sai da a ka fara samar da bayani ga wadannan tambayoyi wadanda a baya babu cikakken bayani a kansu.

Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta fitar da wani fassara kan menene lafiya. Inda a shekarar 1977 hukumar ta bayyana cewa, lafiya shi ne wani yanayi na cikakken kuzarin gangan jiki, qwaqwalwa, da kuma wadatuwa a mu’amalolin rayuwa, ba wai kawai rashin samuwar cuta ko kuma samuwarta ba.

Wannan fassarar ta hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta fuskanci raddi da martani ta bangarori da dama. Saboda a bayaninsu ya na nufin kenan babu yadda za a yi a samu wani mutum mai lafiya a wannan duniyar, sai dai ko a wata duniyar. Cikakken kuzarin gangan jiki da qwaqwalwa da kuma wadatuwa da mu’amalar rayuwa wasu abubuwa ne da ba za su yiwu ba. ko ba komi dabi’ar damuwa ma ta ishi mutum, haka kuma ga tunani wanda zai kawo naqasu ga cikakken kuzari ga qwaqwalwa. Da wannan kadai za mu iya cewa babu wani gamsasshen fassaran abin da a ke nufi da lafiya.

Kafin na ci gaba da bayani zan so na yi qarin haske dangane da wasu abubuwa guda biyu, su ne alamomin cuta (Symptoms) da kuma bayyanar cutan (Signs). Wadannan abubuwan biyu su na da bambanci. Na farko a na gane bayyanar cuta (Signs) ne ta hanyar gani da ido, misali ko a jikin fatar mutum, ko kuma idan a ka auna jininshi. Ita kuma alamar cuta (Symptoms) ba a iya gane ta da ido, sai dai shi mara lafiya ya yi wa likita bayanin abubuwan da ke damunsa, kamar misali mutum ya riqa jin jiri na dibansa, da sauransu.

Ba a qarin haske dangane da bambancin alamomin cuta da bayyanarta kawai zan tsaya ba, akwai kuma wani qarin bayanin dangane da cuta, ciwo, da kuma rashin lafiya. Wadannan abubuwa guda uku bayaninsu shi ne ke kan gaba wurin bayyana bambancin da ke tsakanin kiwon lafiya da kuma sabon bangaren ilimi na ‘Medical Sociology’. Za mu ci gaba a mako mai zuwa

SABON SALON DAUKAN HOTO NA ‘DAB’: MENENE ABIN TAYAR DA HANKALI?

A lokacin da mawaqi Lil Wayne ya saki sabuwar waqarsa ta ‘Lolipop’ shekarun baya, haka ko ina ya cika da kwaikwayon mawaqin, samari da ‘yan mata kusan ko ina za ka gansu da alawar ‘Lolipop’ a baki. Wani ma bai son zaqi, amma dai don ya shigo gari, babu ruwanshi zai bare ya yi ta tsotsa.
Matuqar saurayi na son ya ci gari ya tashi wasa, toh dole sai ya dan sa wannan alawar a baki, ya na tafiya ya na gyada kai kamar wani jinjirin qadangare, duk fa wannan wai burgewa ce da wayewa, saboda kawai Lil-Wayne ya aikata. Da a ce a lokacin al’umma ta dakatar da komi ta mayar da hankali kan yekuwa da shelanta wadannan dabi’u na Lil-Wayne da matasanmu su ka aro, da a maimakon yadda matsalar ta kau a yanzu, da har yanzu akwai ta.
A ‘yan kwanakin nan yaanar gizo da sauran wuraren tattauna batutuwa sun cika sun batse da maganar sabon salon daukan hoto da a ke yiwa laqabi da ‘DAB’. Ra’ayoyi mabambanta sun yi ta yawo a tsakankanin jama’a dangane da ‘DAB’ din, kuma abin mamaki kowa na son dole sai an aminta da ra’ayinshi ko da kuwa babu wata magodara ko qwaqqwarar hujja da ya dogara da ita.
Babban abin da ya fi ban haushi da mamaki dangane da wannan sabon salon daukan hoto shi ne yadda wasu masu fashin faqi a yanar gizo su ka cika ko ina da qirqirarren zance wai wannan sabon salo ba komi ba ne face ‘bautar iblis’.
Ba ina goyon bayan sabon salon daukan hoton na ‘DAB’ ba ne, kuma ba na goyon bayan duk wani kwaikwayon dabi’a da matasanmu ke yi wanda ya saba da al’adun al’ummanmu. Amma fa a matsayina na dalibin fannin sanin halayya da zamantakewa duk wani abu da ya zo, zai zama ina kallonshi ne da idon basira sannan na san a wanne rukunin bayani zai fado.
A wannan yanayin da mu ke ciki a Nijeriya, musamman ma a qasar hausa, sabon salon daukan hoto na ‘DAB’ ba shi ne babban barazanan da ke fuskantar al’ummarmu ba. akwai matsaloli na zamantakewa da daman gaske wadanda sun fi ‘DAB’ din hatsari, ba ma a iya kwatantawa.
Kafin bayyanar ‘DAB’ din ai an yi lokacin da matasanmu ke kwaikwayon salon aski daga shahararrun ‘yan qwallon qafan nahiyar Turai. Matasa sun yi ta yin aski su bar tulin gashi kamar yashi a tsakiyar kai, sai su aske gefen hagu da gefen dama a bar tsakiya, da sunan wai su na kwaikwayon ‘Balatolli’, yayin da wasu kuma ke kwaikwayon dan kwallo ‘Gallas’. Wasu ma sun yi ta kwaikwayon askin Neymar din qasar Birazil da Bidal din qasar ‘Chile’.
Ba ma fa sai an je da nisa ba, a ‘yan kwanakin baya mun ga yadda matasa musamman a arewacin Nijeriya su ka yi ta kwaikwayon salon askin da dan wasan hausa Ali Nuhu ya ke yi, su na kiran askin ‘FKD’. Yadda a ke askin shi ne za a cinye kadan daga qasan gashin kusa da kunne, sai a yi wani tozo a gaban gashin Kaman hular ‘Facing cap’.
A ‘yan kwanakin nan, babban kwaikwayon da ya shahara a tsakanin matan Arewa, musamman ‘yan mata shi ne sabon salon sa hijabi wanda su ka kwaikwayo daga wani fim din hausa mai suna ‘Salma’ a inda ‘yar wasa Aisha Tsamiya ta ke sa hijabi mai hannu da haba, sannan ta sa farin gilashi me igiya. Sunan kwaikwayon ‘Wankan Salma’.
Na dan kawo wadannan qananan misalai ne don in nuna yadda kwaikwayon dabi’a ta ke, haka kuma a kowacce al’ummma a kan samu irin haka. A fannin ilmin sanin halayya da zamantakewa mu na kiran irin wannan kwaikwayo da ‘Fad’. ‘Fad’ wani salon dabi’a ne wanda ya ke samun karbuwa a tsakankanin matasa na dan gajeren lokaci, amma daga baya sai a neme shi a rasa. Da yawa daga ‘Fads’ ba su cutar da al’umma, kuma ba su dadewa na tsawon zamani.
Duk da cewa shi abin da mu ke kira da ‘Fad’ idan ya zo, mutane (matasa) na tururuwan amsanshi, har sai ta kasance a kusan kowanne gida akwai mai kwaikwaiyo. Masana da dama sun yi bahasi mai ma’ana dangane da irin wannan dabi’a ta ‘Fad’, wanda su ka yi sharhi mai inganci bisa dogaro da hujjojin bayan bincike.
Misalin da na bayar a baya na dabi’un kwaikwayon Lil-Wayne, da Ballatolli, da Gallas, da Ali Nuhu, da Aisha Tsamiya, dukkansu ‘Fad’ ne wadanda su ka samu amsuwa a wurin matasa. Da ya ke dama ita dabi’ar ta ‘Fad’ ba ta jimawa a cikin al’umma, yau an nemi masu kwaikwayon Lil-Wayne an rasa, idan da mun ajiye komi mun ce da qarfin tsiya sai matasa sun daina yawo da alawar ‘Lollipop’ a bakunansu, da har yanzu a na nan a na fafatawa da matasa, a na su bari, su na ba za a barin ba. da ya ke an yi burus da su, sai ga ‘Lollipop’ ya zama tarihi.
Idan da qwarewar masananmu da marubuta ya qare a yiwa matasa raddi da dagargazansu dangane da dabi’ar kwaikwayon askin Gallas da Ballatoli, da a yanzu adadin masu tuntu a tsakiyar kai ya qaru. Haka kuma da mun ce ‘DOLE’ sai an daina kwaikwayon askin Ali Nuhu, da mun sa matasa sun mayar da askin wani kayan Gabas.
Damuwar da a ka nuna a kan sabon salon daukan hoto na ‘Dab’ shi ne ya janyo wasu wadanda ba su san da dabi’ar ba su ka sani. Shekaru da dama an jima a na yin ‘Dab’ idan za a dauki hoto, a wasu qasashen ciki har da Afrika, an jima a na yi a qasar Ghana, saboda akwai wani aboki na da ke karatu a Ghana, a shekarar da ta gabata sai na ga ya dauki hoto ya rufe fuska, ya miqar da hannu, na yi ta mamakin wannan kuma menene haka? A kudancin Nijeriya ma an jima a na yin wannan salo, saboda mawaqan jabun turanci na kudanci sun aikata wannan salo sosai a waqoqinsu.
A ‘yan kwanakin nan ne mutanenmu a Arewa su ka san da kwanan zancen, inda a ka fara daukar samfur daga dabi’ar ta ‘Dab’. Sai dai abin mamaki, a Arewa sai marubuta su ka mayar da abin wani abin a zo a gani. A ka yi ta rubuce – rubuce a na cewa wai bautar shaidan ne, dabi’ar banza ce, kwaikwayon ‘yan Illuminati ne da sauran maganganu masu kama da mafarki.
Saboda tsabar yayata batun ‘Dab’ din da a ke yi ne ya sa dabi’ar ta samu karbuwa. Matasa su ka hau kujerar na qi na watsar da ita. Har ta kai Iyalai kan hadu a lokaci guda gaba daya ‘Family’ din su dauki hoto cikin salon ‘Dab’. Wannan yayatawan da marubuta su ka yi ta yi ne ya sa a ka samu wasu su ka yi salon ‘Dab’ a Makkah. Haka akwai wani hoton dan agaji shi ma da ke yawo wanda ya yi ‘Dab’, akwai na tsofaffi shi ma ya na yawo sun yi ‘Dab’.
Sai ka yi mamaki, shin menene abin damuwa a kan wannan dabi’ar wacce idan da an yi banza da ita, cikin qanqanin lokaci za a neme ta a rasa. Shin dabi’ar ‘Dab’ ita ce babban hadarin da ke fuskantar mu a matsayin al’umma? Ina batun yawaitar mutuwar aure, ina batun rashin aikin yi da ya addabi matasanmu, ina batun karuwanci, ina batun cin hanci da rashawa, ina batun annamimanci da cin amana?
A maimakon lokacin da mu ka bata mu na yayata wannan sabon salon na ‘Dab’ da mun bata ne mu na tattauna batun janye jarabawar ‘Post-UME’ da gwamnati ke shirin yi, wanda ga dukkan alamu sai ‘ya ‘yan talakawa sun sha baqar wahala kafin su samu gurbin karatu a jami’o’i.
Kamar yadda na fadi a farkon wannan sharhi, ba na goyon bayan wannan sabon salo na ‘Dab’, amma kuma ban yarda da qarairayin da a ke yadawa dangane da dabi’ar ba. sannan kuma ba wani abin damuwa da tayar da hankali ba ne, idan a ka kau da kai, nan da wani lokaci za a nemi masu aikatawa a rasa. Mu hadu a mako mai zuwa!

HATSABIBANCIN CUTAR BACCI ‘INSOMNIA’

Masana kimiyya sun tafi a kan cewa cutan bacci wani zaunannen abu ne, wanda a kowacce shekara a kan samu kaso 30 zuwa 40% na mutane da ke fama da wannan cuta. Shi cutan bacci wata alama ce da a ka ganewa, amma ba wai wani sharadi ba ne da a ka samar a kimiyyance. Sai dai shi wanda ke fama da cutar ne zai riqa ji a jikinsa cewa wani abu na damunsa.

Cutar bacci ta kaso gida – gida ne. Akwai mutanen da su babban damuwansu shi ne za su iya fara bacci a kowanne hali kuma a kowanne lokaci, wasu kuma su na da matsalar rashin iya samun isasshen bacci, ko kuma farkawa a bacci da sauri ba tare da ya wadace su ba. Haka nan kuma wannan matsaloli da su ka shafi bacci, su na iya zama matsaloli ne na wucin – gadi, ma’ana za su addabi mutum ne na tsawon kwanaki ko makonni, wani lokaci kuma ya kan zama na tsawon zamani ne, daga watanni zuwa shekaru a na fama.

Ita cutar bacci ta ‘Insomnia’ a na daukarta a matsayin barazana ne yayin da ya zama ta takurawa yanayin tafiyar da rayuwar mutum, misali shi ne mutum ya farka bacci amma ya riqa jin wani irin kasala kamar bai yi baccin ba, ko kuma ya wuni cikin wani irin maye na jin bacci. Mutane masu yawan shekaru yanayin baccinsu yak an qaranta, ba zai yiwu su riqa bacci sosai kamar yadda su ke yi a lokacin da su ke da qananan shekaru ba. rashin bacci da yawa ga manya ba wani abin damuwa ba ne, ba shi da alaqa da cutar bacci.

Masana kimiyya sun rarraba yanayin awowin da mutane ke buqata a matakin shekarunsu na haihuwa. Sabbin haihuwa (jarirai) su na buqatar bacci na awowi 13 zuwwa 17, Jarirai ‘yan shekaru 2 su na buqatar bacci na awowi 9 zuwa 13, Yara ‘yan shekaru 10 su na buqatar bacci na awowi 10 zuwa 11, matasa ‘yan shekara 16 zuwa 65 su na buqatar bacci na awowi 6 zuwa 9, haka kuma dattawa ‘yan sama da shekaru 65 su na buqatar baccin awowi 6 zuwa 8 ne. Dattawa ko tsofaffi wadanda su ka haura shekaru 65 a duniya ba su wani buqatar bacci me yawa, kaso 25% kawai na bacci su ke buqata, ba kamar jarirai da matasa ba wadanda su ke buqatar bacci mai yawa, wanda ya kai kaso 50%.

Akwai wasu abubuwa da dama da ke janyo cutar bacci ta ‘Insomnia’. Cikinsu akwai yawaita tafiya a jirgin sama, masana sun ce musamman ma idan tafiyar ta kasance a na yawan yin ta daga Yammaci zuwa Gabashi ne, damuwa da yawan takaici, shanyewan bangaren jiki, yawan shan giya, abubuwan da ke da sindarin ‘Nicotine’ da ‘Caffeine’, talauci, rashin lafiya ko mutuwar wani makusanci.

Daga cikin alamomin kamuwa da wannan cutar ta bacci ‘Insomnia’ sun hada da mutum ya kasa daukan lokacin da ya dace ya na yin bacci, ko kuma ya kasance ya na yawan farkawa da sassafe, kuma ya gaza komawa baccin. Ko kuma ko da mutum ya kwashe awowi ya na bacci amma kuma ya tashi ya na jin jiri ko kuma baccin bai ishe shi ba. ko kuma mutum ya riqa jin ciwon kai da rana kuma ya kasa gudanar da al’amura yadda ya dace. Rashin samun wadataccen bacci wanda ke kawo cutar ta bacci na iya jefa mutum zuwa ga cutar mantuwa, wanda sai abin ya yi qamari a ke kai wa ga wannan cutar. A bisa al’ada cutar bacci ta ‘Insomnia’ ba ta da alaqa da mugayen cututtuka irinsu cutar mantuwa. Cikin manyan cututtukan akwai cutar minshari. Wadanda ke yawan yin mishari a na shawartarsu da su je su ga likita, duk da cewa mutane masu qiba sun fi kamuwa da laruran minshari.

Daga cikin barazanar wannan cutar bacci idan ta yi qamari, ta kan jefa mutum ga gazawa a wurin aiki, sannan idan dalibi ne zai zamo ba ya fahimtar karatu yadda ya kamata, sannan kuma zai kasance me fuskantar barazanar hadari idan ya na tuqin mota. Masana sun tafi a kan cewa ita cutar bacci a na gane alamominta, kuma likitoci su na iya gane alamomin tun kafin cutar ta yi qamari. Likita ne zai fahimci ya tsarin baccinka yak e, shin ka na bin sharuddan da a ka gindaya? Likitanka zai sanar da kai cewa ka samarwa kanka da tsarin yin bacci na mako guda kuma ka chanza tsari. Idan kuma cutar ta yi qamari sai a dora mutum kan wasu tsararrun magunguna . sannan za a hana mara lafiyan yawan yin amfani da sinadaran ‘Nicotine’ ko shan giya da sauransu. Sannan za a sanar da mai fama da cutan a kan ya cire duk wata damuwa daga zuciyarsa.

Haka nan kuma masana sun tafi a kan cewa akwai buqatar a yi gwaji ga mutumin da ke fama da wannan cutar. Saboda zai yiwu akwai wasu cututtukan qwaqwalwa da ya ke fama da su. Zai iya yiwuwa damuwa ce, ko takaicin wani lamari ya jefa shi ga cutar. Likita idan ya yi wa mutum gwaji zai tura shi zuwa cibiyar da ke lura da wannan bangare na cutar bacci, su ne za sus a mutumin da ba shi da lafiya ya kwana a wurinsu, sannan su sa ka wasu na’urorin gwaji domin gwada yanayin matakin da cutar ta ke a kai.

Daga cikin irin matakan da a ke dauka a kan maganace wannan matsalar akwai magungunan da likita ne ke bayarwa, sannan sai a koya mishi yadda zai riqa tsara baccinshi da kuma irin abincin da zai riqa ci, za a koya mishi yadda zai gyara dabi’unsa na rayuwa don qauracewa fadawa matsalolin da za su jefa shi ga wannan cuta. Shi samar da tsarin samun bacci yadda ya kamata ya danganci yadda mutum ya ke sarrafa darensa. Haka nan har ma da yadda mutum ya ke sarrafa dabi’unsa. Mutum na iya sanya wa kansa lokacin da zai fara bacci a farkon dare, wanda kuma zai kasance ba ya saba ma wannan lokacin.

Haka kuma akwai shawarar bai kamata mutum ya riqa yawan mu’amala da dakin bacci ba, sai a lokacin da ya da mu’amala da haka. Bai kamata mutum ya ci chakuleti ko shayi ba kafin ya kwanta. Ka da mutum ya kwanta bacci ya na tunanin aiki ko wasu abubuwan damuwa. Mutum na iya karanta littafi ko yin wani aiki da zai taimaka masa ya rage damuwa.

Domin qauracewa wannan cuta mutum ya riqa yin bacci a dai dai lokaci guda da ya tsara ko da kuwa a qarshen mako ne. Mutum na da buqatar ya ragewa kansa damuwowi yayin da zai kwanta bacci, sannan ya riqa yawan tunanin abubuwa masu amfani ba marasa amfani ba. idan kuma mutum na matsalar baya, zai iya kwanta amma sai ya sa matashin kai a qasan qafafunshi. Bai kamata mutum ya sha madara mai dumi, ko ya yi wanka da ruwan dumi ba yayin da ya ke gab da kwantawa.

Daga qarshe, mutum na buqatar ya riqa motsa jiki, idan motsa jiki cikin dare na hana ka bacci, sai ka mayar da lokacin motsa jikin da safe. Haka kuma mutum ya qauracewa shan tabar sigari ko shan giya da yammaci ko dare. Sannan ya kamata mutum ya qauracewa yawan kallon agogo, idan ma sai ya sa lokacin tashi, toh ya sa sai ya kawar da agogon daga yadda zai iya kallo. Mu hadu mako mai zuwa!

Tuesday, 12 April 2016

MATSANANCIYAR DAMUWA: MUSABBABINTA DA ILLOLINTA


Damuwa iri – iri ce, amma wanda zan fi mayar da hankali a kan ta a wannan makon ita ce wacce mu ke samu sakamakon mu’amalarmu da mutane. Shiga yanayi mara dadi abu ne wanda ke samun mutum idan ya tsinci kanshi a halin qunci, jin cewa ba ka da muhimmanci, bahagon tunani.
Wasu daga cikin abubuwan zahiri da mutum zai ankare cewa matsananciyar damuwa ta fara damunshi shi ne yayin da ya fara jin bakinshi bai da dandano (alhali akwai matsalar da ke damunshi), da kuma rashin iya yin bacci.
Matsananciyar damuwa na da dalilai da yawa. Akwai masana (‘yan qalilan) da ke danganta tsanantar damuwa da qwayar halittan mutum, ma’ana a kan haifi mutum din ne da wasu qwayoyin halittu wadanda ke jefa shi cikin irin wannan yanayi.
Sai dai mafiya yawan masana sun tubure ne a kan cewa lallai matsananciyar damuwa a na samunta ne sakamakon mu’amalar yau da kullum tare da sauran jama’a. sannan kuma hanyar da za a iya magance irin wannan damuwa dole sai an sa hankali da lura.
Mataki na farko na fadawa tarkon matsananciyar damuwa shi ne mutum ya yanke hulda ko mu’amala da jama’a. Duk mutumin da ke yawan jin kunya, ma’ana kunyar shi ta tsananta ta yadda bai iya yin hulda ko mu’amala da jama’a, irin wannan sun fi kallon kansu a matsayin wadanda ba za su iya yin abota yadda ya kamata ba.
Wadanda kunyar tasu ta tsananta a lokuta da dama su kan rayu cikin kadaici ne. Shi kuma rayuwar kadaici ya na da hatsarin jefa mutum cikin matsalolin da za su iya shafar qwawalwa.
Mutumin da ke da dabi’ar yawan jin kunya ya na ganin cewa duk wani motsinshi jama’a na bibiya ne kuma su na tattaunawa a kai, wannan ne ya sa bai samun qwarin gwiwar yin mu’amala da mutane. Amma shi wanda ya tsinci kanshi a matsananciyar damuwa, shi ne wanda ya yanke mu’amala da mutane ba tare da wani dalili ba.
Shi ya sa bincike ya tabbatar da cewa wadanda ke da aure sun fi wadanda ba su da aure tsawon rai. Saboda shi wanda ba shi da aure duk wata damuwa da ya je ya dibowa kanshi, a haka zai kwana ya wayi gari da ita qumshe a zuciya, ta na cinshi.
Amma shi wanda ya ke da aure. Idan ya fita a ka bata mishi rai, ya shiga damuwa. A lokacin da ya koma gida wurin Iyalinshi, ta fahimci cewa ya na cikin wani irin yanayi na damuwa, za ta yi qoqarin sassaita mishi al’amura tare da lallashinshi. Wannan tarairaya da lallashi zai sauqaqa mishi radadin wannan damuwa har ta sauko.
Shi ya sa a sau da yawa a ke ba mutane shawarar idan za su yi aure su auri mace wacce ta ke qaunarsu, ta ke son su, ta ke tausayinsu, ta ke baqin ciki da baqin cikinsu, ta ke damuwa da damuwarsu.
Idan ka auri mace don kyawunta ko don hasken fatarta, alhali ba qaunarka ta ke yi ba. Duk ranar da ka je kasuwa ko wurin aiki a ka bata maka rai ko kuma wani al’amari ya afku wanda ya jefa ka a cikin matsananciyar damuwa, a maimakon wannan kyakkyawar farar matar ta ka ta yayyafa maka sassauci a zuciya, harkokin gabanta za ta ci gaba da yi. A lokacin da ka fahimci matarka ba ta damu da damuwarka ba, wannan zai sake jefa ka cikin tsananin damuwa fiye da wacce ka kwaso.
Fushi ma ya na daga cikin abubuwan da ke taimakawa wurin jefa mutum cikin matsananciyar damuwa. Idan ka na da yawan fushi ko saurin yin fushi, za ka riqa yanke mu’amala da mutane. Za ka rasa abokai, za ka rasa shaqiqai da makusanta.
A duk lokacin da fushinka ya janyo ka rasa abokai da shaqiqai da makusanta, ‘yar qaramar matsalar da ke buqatar shawara ka warware ta za ta girmama ta zamar ma matsananciyar damuwa.
Hassada ma na kawo matsananciyar damuwa. Idan har za ka riqa kallon rayuwar wasu wadanda ka ke mu’amala da su, ka na damuwa da irin ci gaban da su ke samu a rayuwa, tare da fatan su fado qasa warwas. Lallai ka bi hanyar jefa kanka cikin matsananciyar damuwa.
Yawan damuwa da rayuwar wanda bai damu da kai ba. ko yawan damuwa da rayuwar wanda bai ma san kai ya rayuwar ta ka ta ke ba. Misali, ka riqa sanya ido a harkokin mutumin da bai ma san ka na sa mishi ido ba. duk wani abu da ya aikata, idan abin bai yi maka dadi ba, zuciyarka za ta sawwala maka cewa da gangan ya aikata kuma da kai ya ke yi. Wannan zai jefa ka cikin damuwa.
Babbar illar matsananciyar damuwa shi ne ta na cinye zuciya, ta na haifar da cututtuka wadanda magani ba zai iya warkar da su ba. Ta na jefa mutum ga aikata abubuwan da ba su dace ba, wanda zai baqanta mutuntakar mutum a idon duniya. Matsananciyar damuwa na shafar qwawalwa, a wasu lokutan har a yi hauka. Mu hadu mako mai zuwa!