A lokacin da mawaqi Lil Wayne ya saki sabuwar waqarsa ta ‘Lolipop’ shekarun baya, haka ko ina ya cika da kwaikwayon mawaqin, samari da ‘yan mata kusan ko ina za ka gansu da alawar ‘Lolipop’ a baki. Wani ma bai son zaqi, amma dai don ya shigo gari, babu ruwanshi zai bare ya yi ta tsotsa.
Matuqar saurayi na son ya ci gari ya tashi wasa, toh dole sai ya dan sa wannan alawar a baki, ya na tafiya ya na gyada kai kamar wani jinjirin qadangare, duk fa wannan wai burgewa ce da wayewa, saboda kawai Lil-Wayne ya aikata. Da a ce a lokacin al’umma ta dakatar da komi ta mayar da hankali kan yekuwa da shelanta wadannan dabi’u na Lil-Wayne da matasanmu su ka aro, da a maimakon yadda matsalar ta kau a yanzu, da har yanzu akwai ta.
A ‘yan kwanakin nan yaanar gizo da sauran wuraren tattauna batutuwa sun cika sun batse da maganar sabon salon daukan hoto da a ke yiwa laqabi da ‘DAB’. Ra’ayoyi mabambanta sun yi ta yawo a tsakankanin jama’a dangane da ‘DAB’ din, kuma abin mamaki kowa na son dole sai an aminta da ra’ayinshi ko da kuwa babu wata magodara ko qwaqqwarar hujja da ya dogara da ita.
Babban abin da ya fi ban haushi da mamaki dangane da wannan sabon salon daukan hoto shi ne yadda wasu masu fashin faqi a yanar gizo su ka cika ko ina da qirqirarren zance wai wannan sabon salo ba komi ba ne face ‘bautar iblis’.
Ba ina goyon bayan sabon salon daukan hoton na ‘DAB’ ba ne, kuma ba na goyon bayan duk wani kwaikwayon dabi’a da matasanmu ke yi wanda ya saba da al’adun al’ummanmu. Amma fa a matsayina na dalibin fannin sanin halayya da zamantakewa duk wani abu da ya zo, zai zama ina kallonshi ne da idon basira sannan na san a wanne rukunin bayani zai fado.
A wannan yanayin da mu ke ciki a Nijeriya, musamman ma a qasar hausa, sabon salon daukan hoto na ‘DAB’ ba shi ne babban barazanan da ke fuskantar al’ummarmu ba. akwai matsaloli na zamantakewa da daman gaske wadanda sun fi ‘DAB’ din hatsari, ba ma a iya kwatantawa.
Kafin bayyanar ‘DAB’ din ai an yi lokacin da matasanmu ke kwaikwayon salon aski daga shahararrun ‘yan qwallon qafan nahiyar Turai. Matasa sun yi ta yin aski su bar tulin gashi kamar yashi a tsakiyar kai, sai su aske gefen hagu da gefen dama a bar tsakiya, da sunan wai su na kwaikwayon ‘Balatolli’, yayin da wasu kuma ke kwaikwayon dan kwallo ‘Gallas’. Wasu ma sun yi ta kwaikwayon askin Neymar din qasar Birazil da Bidal din qasar ‘Chile’.
Ba ma fa sai an je da nisa ba, a ‘yan kwanakin baya mun ga yadda matasa musamman a arewacin Nijeriya su ka yi ta kwaikwayon salon askin da dan wasan hausa Ali Nuhu ya ke yi, su na kiran askin ‘FKD’. Yadda a ke askin shi ne za a cinye kadan daga qasan gashin kusa da kunne, sai a yi wani tozo a gaban gashin Kaman hular ‘Facing cap’.
A ‘yan kwanakin nan, babban kwaikwayon da ya shahara a tsakanin matan Arewa, musamman ‘yan mata shi ne sabon salon sa hijabi wanda su ka kwaikwayo daga wani fim din hausa mai suna ‘Salma’ a inda ‘yar wasa Aisha Tsamiya ta ke sa hijabi mai hannu da haba, sannan ta sa farin gilashi me igiya. Sunan kwaikwayon ‘Wankan Salma’.
Na dan kawo wadannan qananan misalai ne don in nuna yadda kwaikwayon dabi’a ta ke, haka kuma a kowacce al’ummma a kan samu irin haka. A fannin ilmin sanin halayya da zamantakewa mu na kiran irin wannan kwaikwayo da ‘Fad’. ‘Fad’ wani salon dabi’a ne wanda ya ke samun karbuwa a tsakankanin matasa na dan gajeren lokaci, amma daga baya sai a neme shi a rasa. Da yawa daga ‘Fads’ ba su cutar da al’umma, kuma ba su dadewa na tsawon zamani.
Duk da cewa shi abin da mu ke kira da ‘Fad’ idan ya zo, mutane (matasa) na tururuwan amsanshi, har sai ta kasance a kusan kowanne gida akwai mai kwaikwaiyo. Masana da dama sun yi bahasi mai ma’ana dangane da irin wannan dabi’a ta ‘Fad’, wanda su ka yi sharhi mai inganci bisa dogaro da hujjojin bayan bincike.
Misalin da na bayar a baya na dabi’un kwaikwayon Lil-Wayne, da Ballatolli, da Gallas, da Ali Nuhu, da Aisha Tsamiya, dukkansu ‘Fad’ ne wadanda su ka samu amsuwa a wurin matasa. Da ya ke dama ita dabi’ar ta ‘Fad’ ba ta jimawa a cikin al’umma, yau an nemi masu kwaikwayon Lil-Wayne an rasa, idan da mun ajiye komi mun ce da qarfin tsiya sai matasa sun daina yawo da alawar ‘Lollipop’ a bakunansu, da har yanzu a na nan a na fafatawa da matasa, a na su bari, su na ba za a barin ba. da ya ke an yi burus da su, sai ga ‘Lollipop’ ya zama tarihi.
Idan da qwarewar masananmu da marubuta ya qare a yiwa matasa raddi da dagargazansu dangane da dabi’ar kwaikwayon askin Gallas da Ballatoli, da a yanzu adadin masu tuntu a tsakiyar kai ya qaru. Haka kuma da mun ce ‘DOLE’ sai an daina kwaikwayon askin Ali Nuhu, da mun sa matasa sun mayar da askin wani kayan Gabas.
Damuwar da a ka nuna a kan sabon salon daukan hoto na ‘Dab’ shi ne ya janyo wasu wadanda ba su san da dabi’ar ba su ka sani. Shekaru da dama an jima a na yin ‘Dab’ idan za a dauki hoto, a wasu qasashen ciki har da Afrika, an jima a na yi a qasar Ghana, saboda akwai wani aboki na da ke karatu a Ghana, a shekarar da ta gabata sai na ga ya dauki hoto ya rufe fuska, ya miqar da hannu, na yi ta mamakin wannan kuma menene haka? A kudancin Nijeriya ma an jima a na yin wannan salo, saboda mawaqan jabun turanci na kudanci sun aikata wannan salo sosai a waqoqinsu.
A ‘yan kwanakin nan ne mutanenmu a Arewa su ka san da kwanan zancen, inda a ka fara daukar samfur daga dabi’ar ta ‘Dab’. Sai dai abin mamaki, a Arewa sai marubuta su ka mayar da abin wani abin a zo a gani. A ka yi ta rubuce – rubuce a na cewa wai bautar shaidan ne, dabi’ar banza ce, kwaikwayon ‘yan Illuminati ne da sauran maganganu masu kama da mafarki.
Saboda tsabar yayata batun ‘Dab’ din da a ke yi ne ya sa dabi’ar ta samu karbuwa. Matasa su ka hau kujerar na qi na watsar da ita. Har ta kai Iyalai kan hadu a lokaci guda gaba daya ‘Family’ din su dauki hoto cikin salon ‘Dab’. Wannan yayatawan da marubuta su ka yi ta yi ne ya sa a ka samu wasu su ka yi salon ‘Dab’ a Makkah. Haka akwai wani hoton dan agaji shi ma da ke yawo wanda ya yi ‘Dab’, akwai na tsofaffi shi ma ya na yawo sun yi ‘Dab’.
Sai ka yi mamaki, shin menene abin damuwa a kan wannan dabi’ar wacce idan da an yi banza da ita, cikin qanqanin lokaci za a neme ta a rasa. Shin dabi’ar ‘Dab’ ita ce babban hadarin da ke fuskantar mu a matsayin al’umma? Ina batun yawaitar mutuwar aure, ina batun rashin aikin yi da ya addabi matasanmu, ina batun karuwanci, ina batun cin hanci da rashawa, ina batun annamimanci da cin amana?
A maimakon lokacin da mu ka bata mu na yayata wannan sabon salon na ‘Dab’ da mun bata ne mu na tattauna batun janye jarabawar ‘Post-UME’ da gwamnati ke shirin yi, wanda ga dukkan alamu sai ‘ya ‘yan talakawa sun sha baqar wahala kafin su samu gurbin karatu a jami’o’i.
Kamar yadda na fadi a farkon wannan sharhi, ba na goyon bayan wannan sabon salo na ‘Dab’, amma kuma ban yarda da qarairayin da a ke yadawa dangane da dabi’ar ba. sannan kuma ba wani abin damuwa da tayar da hankali ba ne, idan a ka kau da kai, nan da wani lokaci za a nemi masu aikatawa a rasa. Mu hadu a mako mai zuwa!
No comments:
Post a Comment