Friday, 25 September 2015

BUKUKUWAN SALLAH: MASIFUN DA KE FUSKANTAR IYAYE

Ina yiwa mai karatu barka da Sallah, da fatan Allah ya maimaita mana ganin na wasu shekarun cikin yalwar arziki da lafiyar jiki da zaman lafiya.
Kusan na jima ina yin rubuce rubuce a kan irin abubuwan da kan faru a lokacin da a ke bukukuwan Sallah, ba zan iya tuna takamaimen lokacin da na fara ba, amma ina iya tuna dalilin da ya sa hankali na ya karkata ga bukukuwan Sallah.
A wadancan shekarun babban dalili shi ne; a duk ranar Sallah karama ko babba matasa kan yi gungu (a wasu garuruwan har su dinka kaya iri daya) su je wuraren da a ke yin wasannin sallah. Wurin wasannin kan hada ‘yan unguwanni daban daban, don haka sabani kalilan ya kan kunna wutar bala’in da zai kai ga kisan rai. An yi haka ya fi a kirga. Kamar a Kaduna wuraren da su ka yi kaurin suna a wancan lokacin kan fadace – fadace har da kisa sun hada da; ‘Gamji Gate’ da ‘Galady’.
Haka kuma a washegarin sallah, gungun matasan na sake ziyartan wadancan wurare, inda da zaran an hadu sai kuma a shiga batun daukar fansa, wanda a nan ma wasu rayukan ne ke salwanta. A hankali, wannan al’adar ta zama babba, a kusan garuruwa da daman gaske da ke Arewacin Nijeriya a na aikata hakan.
Sannan abu na biyu wanda ya biyo baya shi ne; matasa sun fara wayewa daga shiga harkokin daba da kauranci. Wannan kuma ya auku ne har da bunkasar wayewa da kuma yawan mu’amala da kafafen sadarwa. Amma sai na sake fahimtar cewa da a ka daina sare – sare a kungiyance a lokutan bukukuwan sallah, sai kuma wata muguwar al’ada ta bijiro, ita ce ta yin wasa da mota ko mashin a wannan lokaci.
A irin wadannan wasanni da mota ko babur a lokutan bukukuwan sallah a kan samu rahotannin rasuwar rayuka da dama daga jihohi har ma da kauyukan jihohin. Wanda wannan babban abin lura ne da damuwa.
Iyaye su ne ke da kaso mafi tsoka a wurin dakile ire – iren wadannan al’adu a lokutan bukin sallah, babu yadda za a yi gwamnati ta iya magance wannan abu ba tare da iyaye sun fara na su aikin ba.
Idan da a ce kowanne Uba zai tsawatarwa dansa cikin nasiha da lalama tare da yi mishi bayanin irin hadarin da ke cikin shiga zugar masu irin wadannan al’adu da za a samu karancin rahotannin barna. Haka kuma idan iyaye za su rika bibiyan mu’amalolin ‘ya ‘yansu a lokutan wannan shagali na Sallah, shi ma zai bayar da daman su iya dakile yiwuwar afkawar matasa ga irin wannan dabi’a.
Wasu iyayen sun yi kokarin hana ‘ya ‘yansu ga shiga harkokin dabanci da kauranci. Amma yanzu babbar matsalar da ke fuskantar al’umma ta girmi dabanci da kauranci, wanda kuma idan Iyaye ba su dauki matakin gaggawa ba, karshenta su ne za a bari da kukan takaici a kuma haifarwa da al’umma da annoba.
Kamar yadda al’amarin fasadin Luwadi ya zama ruwan dare; a wannan lokutan bukukuwan Sallah masu irin wannan dabi’a ta dabbobi za su fake su yi ta bata kananan yara. Kwanakin baya na ke ce ma wani abokina ya kamata mu yi bincike a kan dalilin da ya sa shaidanu ‘yan luwadi su ke farmakan kananan yara.
Idan a shekarun baya al’amarin luwadi bai shigo kasar hausa sosai ba, toh yanzu kam ya shigo ya mamaye wurare da dama. Kusan kullum sai ka ji labarin an cafke wani dan iskan ya na aikatawa. Abin takaicin shi ne kaso 80 da a ke kamawa, su na aikatawa ne da kananan Yara da kuma Matasa.
Tunda mun fahimci cewa wadanda su ka fi fadawa tarkon ‘yan luwadi su ne ‘yan shekaru 7 zuwa 30. Dole ne iyaye su sa idanu sosai a kan duk wani motsin ‘ya ‘yansu. Ba ko ina ya kamata a kyale Yara su rika zuwa ba. musamman ma ya kamata Iyaye su rage yawan yawace yawacen Yara da sunan ‘Yawon Sallah’.
Wannan zamanin ya zo da masifu da bala’o’i iri iri wadanda dole ne sai kowa ya shiga taitaiyinsa tare da daukar matakan kiyayewa. Ba wai ina nufin kar a bar yara su yi ziyara ba, amma a matsayinka na mahaifi ko mahaifiya ya kamata ne a ce kun san ina ne ‘ya ‘yanku su ka je, idan son samu ne ma, ya zama ku ne za ku kai su wurin ziyarar ta yadda za a samu ladan tare.
Na biyu shi ne, akwai wasu kuma wadanda mutane ne amma dabi’ar tamkar ta dabba. Su kuma wadannan, bata kananan yara mata su ke yi; Kaman ‘yan shekaru 5 zuwa 10. Su kan yi musu dabaru, tare da jan hankalinsu da sunan goron sallah. Saboda haka, a nan ma dole ne Iyaye ya zama sun takaita yawon ‘ya ‘yansu mata, saboda gudun sharrin dabba a rigar mutum.
Na uku shi ne yadda samari da ‘yan mata su ke yin amfani da lokacin sallah a matsayin ranakun da za a aikata zina ce zina ce da masha’a. Iyaye na da karfin ikon hana afkuwar wannan masifa, ta hanyar takaita yawace yawacen su ‘yan matan.
Daga karshe zan so iyaye su fahimci cewa; ko dai su tashi tsaye wurin yiwa ‘ya ‘yansu garkuwa daga wadannan mugaye da shaidanun mutane, ko kuma a yiwa rayukan ‘ya ‘yan nasu katoton tabon da warkewarshi sai an yi zufa. Binciken masana halayyar jama’a da zamantakewa ya tabbatar da cewa, idan a ka fara aikata alfashar luwadi da Yaro ya na wahala ya daina. Idan kuma bai daina ba, dole ne zai bata wasu yaran da ya ke rayuwa da su. Idan Iyaye ba su motsa ba yanzu, sai yaushe? Mu hadu mako mai zuwa!



Friday, 18 September 2015

Hadarin Da Ke Cikin Killace Yara

Tabbas rayuwa a tare da mutane wani babban al’amari ne mai muhimmancin gaske ga dan Adam, wannan ba ma ga mutane kadai ba, hatta Birai su na da bukatuwa ga rayuwa tare da ‘yan uwansu a matsayin al’umma.
Binciken ilmi da wasu masana halayyar dan Adam da zamantakewa Harry da Margaret Harlow su ka gudanar a shekarun 1962 da 1977, sun fitar da bayanai masu tasirin gaske dangane tasirin mu’amala a tsakanin dabbobi.
Masanan sun gudanar da binciken ne kamar haka: sun dauki jiriran Birai biyu daga wurin mahaifansu inda su ka kebe su a cikin keji daban daban. A kowanne keji akwai kirkirarrun Birai guda biyu a matsayin iyayen wadannan jarirai, akwai sakago (Biri mara rai) wanda a ka kera shi ta hanyar sanya abun tsotso ‘Feeding bottle’ a jikinshi. Sannan kuma akwai wanda a ka kera shi a ka lullube shi da irin jikin Biri amma babu wannan abin tsotso a jikinsa.
Binciken ya tabbatar da cewa jariran Birai din su kan haye kan kirkirarrun Iyayensu wadanda a ka kirkire su da irin jikin asalin Biri su kwanta har sai yunwa ta ci su, sai su sauko su nufi wurin dayan kirkirarren Birin da ke dauke da abin tsotso su sha idan sun koshi sai su koma saman wancan.
Bayan watanni shida da a ka fitar da wadannan Birai a ka hada su da ‘yan uwansu, sai ya kasance wannan tsawon lokaci da su ka dauka a kebe ya taba su, ta yadda a ko da yaushe sai dai su koma gefe su na kallon yadda sauran Birai ke gudanar da al’amuransu na yau da kullum ba tare da shiga ba. dalili kuwa shi ne wadannan Birai sun yi wayo ne a kebe, ba su samu damar koyon yadda a ke mu’amala da sauran ‘yan uwa Birai ba.
Da wannan dan takaitaccen misali wanda na dora shi a bisa binciken ilmi na ke son tabbatarwa cewa shi Mutum ya fi Biri bukatuwa zuwa ga koyon mu’amalolin yau da gobe.
Al’amarin killace Yara kuwa wani abu ne mai girma, duk da ya ke babu yadda za a yi don kawai a na so a fahimci me zai iya faruwa idan an killace su, sai masana halayyar dan Adam da zamantakewa su debi Jarirai su killace su a matsayin gwaji. Amma daga bincike da a ka gudanar dangane da irin sakacin da iyaye ke yi ko kuma wadanda a ke dauka domin rainon jarirai ke yi, an tattara bayanai sosai dangane da irin hadurrra da ke cikin killace Yaro. Zan yi kokarin kawo misalan binciken da a ka gudanar wadanda a cikinsu akwai darussa da ke nuni da hadurran aikata hakan.
Akwai wata yarinya da a ka haifa a shekarar 1932 mai suna Anna, iyayenta ba aure su ka yi a ka haife ta ba, bilhasali ma mahaifiyarta na da matsalar tabin kwakwalwa, saboda haka tun kafin haihuwarta babu wanda ya damu da ta rayu ko ta mutu. A haka a ka haifi Anna, wacce cikin rashin kulawa da nunawa damuwa a ka killace ta a wani kuryan daki da ke gidan mahaifin uwarta. Mahaifiyarta ta na fita tun da asuba ta tafi gona kuma sai dare ya yi nisa ta ke dawowa. Saboda haka ne Anna ba ta samu kulawa da kauna kamar yadda sauran ‘ya ‘ya ke samu.
Masanin halayyar jama’a da zamantakewa Kingsley Dabis a shekarar 1940 ya yi fashin baki dangane da halin da a ka tsinci Anna a shekarar 1938, kamar haka: (Anna) ba ta iya yin magana kamar yadda dan Adam ke yi, haka nan kuma ba ta iya yin tafiya kamar yadda kowa ke yi, ba ta fahimta don an alamta mata abu da hannu, ba ta iya cin abinci da kanta ko da an ajiye mata abincin a gabanta, sannan ba ta san menene tsafta ko kazanta ba.
Wannan al’amari duk ya faru da Anna ne a cikin shekaru shida a killace. A dai dai wannan lokaci ne a ka sa ka ta a makaranta ta musamman, inda a hankali ta fara koyon yadda a ke tafiya da kafafu biyu, yin magana, da kuma tsaftace kanta. Anna ta na ‘yar shekaru 10 a duniya ta mutu, amma kafin mutuwarta an ruwaito cewa ta koyi yadda a ke bin umurni, yin magana, wanke hannayenta biyu, goge bakinta tare da kokarin taimakon wasu Yaran.
A shekarar 1970 an tsinci wata yarinya ‘yar shekaru 13 mai suna Genie. Ita Genie an tsince ta ne a wani kullallen daki ita kadai tun ta na ‘yar watanni 20 a duniya. Mahaifiyarta ta yi haka ne saboda ba ta son a san ta haihu. Sai ta rika watsawa yarinyar abinci ta tagar dakin. Genie ba ta taba jin sautin dan Adam ba, saboda babu wanda ya taba yi mata magana, haka kuma babu talabijin ko Rediyo a dakin.
Masanan da su ka amshi Genie bayan an tsinto ta sun bayyana ta kaamar haka: a lokacin da a ka kawo ta sam ba ta san wani abu wai shi mu’amala ba. ba ta san ya a ke yin fitsari ko bayan gari ba, ba ta iya cin abinci yadda mutane ke tattaunawa a baki kafin su hadiye ba. ba ta iya rike fitsarinta balle bayan gari. Saboda rashin tauna abincin da ta ke yi a lokacin da a ka tsince ta, girman jikinta da tsawonta bai fi na Yaro mai rabin shekarunta ba.
Da wadannan ‘yan misalai za mu iya fahimtar cewa shi killace Yaro a hana shi mu’amala da mutane babban hadari ne wanda zai jefa yaron cikin sahun wadanda ba su iya mu’amala da mutane ba. kuma wannan rashin iya mu’amala na iya ci gaba da tasiri a rayuwar mutum har zuwa girmanshi, ta yadda za ka ga mutum cikakke amma idan ya kwafso maka wani shirmen sai ka dauka dan firamare ne.
Mu hadu mako mai zuwa

Monday, 7 September 2015

Taqaddama: MUGUNTA DA MUSABBABINTA 'AGGRESSION'

A wata taqaddama mai sarqaqiya, an ce kowanne mutum ma mugu ne, an ce kowa na da nau’in mugunta a cikin jininshi, sai dai wani mugun ya gawurta fiye da wani.
Ma’anar mugunta a fannin ilmin zamantakewa da sanin halayyar jama’a shi ne cutar da mutane bisa ganganci. Dalilin da ya sa mu ka mayar da hankali wurin karantar mugunta shi ne bisa la’akari da yadda mugaye su ka yi wa duniya yawa.
Saboda qoqarin ganin an fahimci mugunta da nau’o’inta, masana a wannan fanni sun kasu kashi uku; ‘yan sahun farko su ne wadanda su ka tafi a kan cewa mugunta halitta ce wacce a ke haifo mutum da ita ko kuma a ke iya gadonta. ‘yan sahu na biyu kuma su ne wadanda ke da ra’ayin cewa babu ruwan dabi’a ko gado da muguntar mutum. A yanzu an samu kaso na uku, wadanda su kuma ke ganin mugunta ta tattara abubuwa da yawa, ba abu guda daya ba ne ke zama dalilinta.
Akwai mugunta wacce ta qumshi cutar da gangar jikin mutum – misali mangari, naushi, caccaka wuqa, ko kuma harbi da bindiga ko kibiya. daya sashen mugunta shi ne wanda bai qumshi cutarwa kaitsaye ga gangan jikin mutum ba. Irin wannan muguntar sun hada da ta fatar baki, irinsu yiwa mutum ihu, rantsuwa bisa shaidar zir. Cikin irin wannan muguntar har da yin gulma domin cin zarafin wani mutum. akwai kuma wata samfurin mugunta wacce ba ta buqatar magana da fatar baki, kawai sai dai a yi amfani da alami, misali fashewa da dariya yayin da wani ya shigo wuri. Toshe hanci a yayin da wani ya gifta, da dai sauransu.
Zan bibiyi wadannan mabambantan ra’ayi ta yadda hatta mai karatu zai iya fahimtar daga ina mugayen da ke zagaye da shi su ka samo muguntarsu. Idan kuma kai ne mugun, bayan karanta musabbabin mugunta za ka so ka yi qoqarin daqile ta ko rage tasirinta a kanka.
Wadanda su ka ce mugunta a na haihuwar mutane ne da ita sun tafi a kan cewa akwai wata qwayar halitta mai suna ‘Thenatos’ wacce a ke haihuwar kowanne dan Adam da ita. Ita wancan qwayar halitta ne ke ingiza mutane wurin aiwatar da duk wani nau’in mugunta a kan mutane.
A wurin masu irin wancan fahimtar sun ce ita qwayar halittar ‘Thenatos’ an halicci mutum ne da ita a matsayin wani sindari da zai rusa shi. A maimakon mutum ya bari wannan qwayar halitta ta ‘Thenatos’ ta rusa shi, sai a riqa yin amfani da ita wurin cutar da mutane, dabbobi ko wasu halittun da ke kusa da shi.
Masanan sun ci gaba da cewa, idan a cikin mutane ka ga wani mutum wanda bai fiye aikata mugunta ba; ire iren wadannan mutanen su na danne waccan qwayar halittan ne ta yadda sai dai ta ci gaba da cutar da su.
Babban misali a nan shi ne, mutumin da ya qware a mugunta ba ya buqatar sai an tsokane shi ko an aikata wani aiki sannan zai aikata muguntan. Zai iya daukan mota ya hau titi ya na mugun gudun da zai riqa tsoratar da mutane, wasu lokutan ma har ya hau ta kan wasu. Ka ga kenan wannan mugun bai buqatar wani dalili kafin ya aikata. Amma akwai a cikin mutane wadanda ko ka nemi rikicinsu, za su danne su bar komi ya wuce. Za ka ga wani, an zo da mota an yi mishi tuqin ganganci har ma a yi mishi barna, amma wannan ba zai sa shi ma ya mayar da ganganci ba balle ya aikata barna.
bangaren wadanda ke ganin babu wata alaqa tsakanin mugunta da qwayar halitta sun bayyana ne sakamakon martani da raddi da su ka dabaibaye wancan ra’ayin na farko. Su kuma wadannan sun tafi ne a kan cewa mutum na zama mugu ne sakamakon tursasawa. Ma’anan tursasawa a nan shi ne a kange mutum daga cimma wani muradi na shi ko kuma a tauye mishi wani haqqi da ya ke ganin na shi ne.
Masu wannan ra’ayin na alaqanta mugunta da tursasawa sun tafi a kan cewa yanayin yadda za ka tursasa mutum yanayin irin samfurin muguntan da zai aikata maka. Shi ya sa a wurinsu mugunta ta fi yawa a wurin wadanda ba su da aikin yi, da wurin wadanda ba su da kudi, da kuma wurin wadanda su ka sha kaye a fagen soyayya.
Misali a nan shi ne, idan har a ka samu yawan matasa wadanda ba su da aikin yi a gari, wannan rashin aikin yi shi ne zai tursasa matasan su riqa sa kansu a cikin rikice rikicen da za su iya kaiwa ga salwantar rayuka, qone qone da sace sace.
Haka kuma idan mutum biyu su na neman budurwa daya. Sai na farko ya samu dacen sace zuciyar yarinyar, har ta kai idan na biyun ya zo zance, sai na farkon (wanda ya sace zuciyarta) ya zo ya janye ta gefe, sannan kuma su yi ta sheqewa da dariya; wannan irin cin fuska da su ke yi mai zai tursasa shi ya aiwatar da kowanne irin nau’in mugunta a kansu.
Shi ma wannan nazarin na alaqanta mugunta da tursasawa ya sha raddi da martani; martanin ne ma ya samar da wani nazarin dangane da mugunta, wanda ya tafi a kan cewa babu wani abu qwaya daya tak da ke zama musabbabin mugunta. A wannan fahimtar, mugunta babu ruwanta da qwayar halitta, sannan babu ruwanta da tursasawa. Ita mugunta a na koyonta ne kamar yadda a ke koyon sauran dabi’u. ta hanyoyin da a ke bi a koyi sauran dabi’u ta su kuma a ke bi a koyi mugunta.
Idan mutum ya fiye kallon fima fiman mugunta, babu makawa zai fara gina dabi’ar mugunta. Wanda a kodayaushe bai da aiki sai kallon fima fiman da Amurkawa ke yi, a na kwano da mota a na rusa gidaje da qaddamar da mugunta iri iri, akwai yiwuwar duk ranar da wannan mutumi ya dauki mota ya yi qoqarin gwada abin da ya ke kallo.
Kamar yadda mu ke koyon mu gaisa da mutane, haka nan mu ke koyon mu mari mutane. Kamar yadda mu ke koyon mu yi wa mutum murmushi haka nan mu ke koyon mu zare wa mutum ido don ya ji tsoro. Saboda haka idan a ka ce wai tursasawa ne ke janyo mugunta, sai mu ce ai akwai mutanen da mu ka sani wadanda za a tursasa su a kai su bango amma su hadiye fushinsu. Haka kuma yadda a ke samun mugaye a cikin talakawa haka nan a ke samu a tsakanin masu dukiya. Mugunta ba komi bace face wata dabi’a wacce mu ke koyo a muhallin da mu ke rayuwa; idan mu ka tsinci kawunanmu a tsakiyar mugaye, za mu ginu da dabi’ar yi wa mugunta kallon abu me kyau. Mu hadu mako mai zuwa!


Mu Fahimci Dabi’ar MUTUM 'ATTITUDE'

Matsalolin da ke tattare da yawancin ma’aikatu, masana’antu, cibiyoyi da hukumomi ba komi ba ne face matsalar rashin sanin dabi’un dan Adam. dabi’a aba ce me wahalan sha’ani, kadan ne daga cikin mutane su ke yin mu’amala da mutum a lokaci guda kuma su ke karantar dabi’arsa. Sau da yawa kawai mu’amala da fankon mutum mu ke yi, ba tare da nazarin dabi’arsa dangane da abubuwa ba.
                dabi’ar mutum ne ke taimakonsa ya fassara yanayi, kuma duk ta yadda ya yi fassaran yanayi a haka zai tafiyar da shi, kuma da wannan fassarar ne zai duba ya gani shin wacce irin mu’amala zai yi a dai dai lokacin.
                dabi’un mutane sun bambanta, sai dai a wasu lokutan a kan samu wani babban al’amari wanda ke zama sanadin haifarwa da mutane dabi’a iri guda. Misali a nan shi ne, a shekarar 2003 lokacin da qasar Amurka ta shirya za ta yaqi qasar Iraqi, mutanen qasar Amurka sun yi ta zanga zangan Allah wadai da wannan yaqi da a ke son gabatarwa. Wannan ya nuna mana cewa, mutanen Amurka sun gaji da yaqe yaqen da qasar ke shiga, saboda haka yawan yaqin da qasarsu ke yi sai ya haifar musu da dabi’ar qin jinin yaqi.     
                Akwai wasu abubuwa da dabi’ar mutum ne kadai ke kai shi ga aikata su. Na farko, dabia ce kadai ke sa mu qaunaci mutum ko mu qi shi, ita ke sa mu ji mu na son wasu gungun mutane ko qungiya. Haka nan dabi’arka ce kadai za ta iya zartarwa ka danganta kanka da qungiya; kamar misali idan dabi’arka ba ta qaunar tsiraici da kallon batsa, babu yadda za a yi ka kasance ma’abocin kallon fima fiman da ‘yan Kudancin Nijeriya ke yi a yanzu ‘Nigerian Films’, saboda dabi’arka ba ta son kallon irinsu, ko da bisa kuskure ka zo inda a ke kallo, yanayin fuskarka da yadda ka ke yi, zai nuna cewa ka ginu da dabi’ar qin irin wannan fima fimai.
                Na biyu shi ne, da dabi’a mutum ke dubawa ya ga shin idan ya aikata wani aiki me zai biyo baya? A nan za mu iya cewa saboda son biyan buqatar mutum ya na iya aikata dabi’un da zasu kai shi ga cimma muradunsa . Misali, mutumin da ya hango diyar wani ya na so, zai yi qoqarin ko ta wanne hali ya riqa aikata dabi’u masu kyau a wuraren da ya ke tsammanin mahaifin yarinyar ko wasu makusantanshi. Ba kawai biyan buqatun mutum ba, da dabi’a mutum ke kiyaye abubuwan da za su iya kasancewa barazana gare shi. Misali a nan shi ne, bayan da a ka samu sabuwar gwamnati a Nijeriya; da yawan manyan mutane sun fara sassauta dabi’unsu na almubazaranci, da almundahana saboda gudun kar Shugaban qasa Buhari ya yi sukuwa a kansu. Wannan dabi’ar ta ginu ne saboda tsoro.
                Na uku, a sau da yawa za ka ga wasu mutane na aikata abu babu kyawun gani. Su a wurinsu dabi’arsu ce ke nuna musu cewa wannan abu da su ke aikatawa dai dai ne. Abu daya ne ke dai daita dabi’ar mutum zuwa mai kyau kuma ta-gari, shi ne ilmi. Ilmi na da muhimmancin gaske wurin tasiri ga dabi’ar mutum. Misali a nan shi ne, za ka ga mutumin da bai je makarantar jami’a ba ko gaba da sakandare, zai tashi da wata irin dabi’a ta gani – gani ga duk wata qabila da ba ta shi ba. Amma a lokacin da mutum ya samu damar halartar makarantun gaba da jami’a, inda kusan kowacce qabila ta na da ‘ya ‘yanta a matsayin dalibai, bayan dogon lokacin da mutum zai dauka ya na karatu tare da mu’amala da mutane daga qabilu daban daban, za ka ga ya samu chanji a dabi’arsa daga qin jini ko gani – gani ga wasu qabilun da ba nashi ba.
                Na hudu, dabi’ar mutum ne ke ba shi dama ya bayyanawa duniya ko shi wanene, dabi’arsa ce ke ba shi daman bayyana al’adarshi da irin halayenshi. Kamar misali, a shekarun baya da su ka shude a jihar Kano, idan ka ga mutum da jar hula, babu tantama wannan jar hula na alamta qauna ne ko shauqin Malam Aminu Kano. A yanzu kuma idan ka ga mutum da hula a Kano, mutane na saurin fassara shi ne da kasancewa dan Kwankwasiyya. Wannan ne ya sa da yawan dattawa (tsofaffi) a cikin garin Kano su ka watsar da jajayen hulunansu (Na Malam Aminu Kano) saboda su ba’yan kwankwasiyya ba ne, kuma ba su so a fassara su a haka.
                Duk da dabi’a ba wata aba ba ce da a ke iya gani da ido, ko a taba, amma a na iya auna ta. Wannan ba sabon abu ba ne. idan ka na so ka fahimci inda dabi’ar mutum ta dosa dangane da wani al’amari bari ka ji yadda a ke auna dabi’a. Akwai wasu hanyoyin auna dabi’a da yawan gaske wadanda mu ke amfani da su, amma mafi sauqin ciki zan yi bayani a kai. 
                Kamar misali, ka na so ka fahimci shin menene ra’ayin mutum dangane da auren zawarawa da wasu gwamnoni ke bayarwa. Sai ka yi mishi tambaya kamar haka; Shin ka na goyon bayan auren zawaran da gwamnati ke jagoranta? Kai za ka qayyade amsoshin da mai amsawa zai zaba, ba wai za ka barshi ya yi ta zubo bayani ba ne. misali sai ka bashi zabi biyu; Eh ko A’a.
                Duk amsar da wanda a ka tambaya ya zaba a cikin biyun, da su za ka auna dabi’arsa dangane da auren zawarawa. Idan ya zabi EH. Shi kenan ka gano cewa dabi’arsa dangane da auren zawarawa ta goyon baya ce, wannan zai sa ba za ka riqa fargabar yin maganan auren zawarawa da shi ba, musamman muhimmancinshi da kuma amfaninshi. Idan kuma ya zabi A’A, ya na nuna dabi’arsa ba ta qaunar auren zawarawan da a ke yi, shi zai sa ka kiyaye yawan matsawa a kan auren zawarawa a duk wata tattaunawarka ko mu’amalarka da wannan mutumin. Mu hadu mako mai zuwa
    

SAUYI A CIKIN AL’UMMA: NAZARIN BUKIN ZAGAYOWAR RANAR HAIHUWA (Birthday)

Kowanne mutum a duniya haifo shi a ka yi, babu wani tarihi da ya riske mu a kan cewa ga wani wanda shi fadowa ya yi daga sama, ba a jariri ba, da girmanshi da wayonshi. Wannan dalili na cewa kowanne mutum haihuwarsa a ka yi a duniya ne ya samar da ranar haihuwa.
            A tsohuwar al’adar Malam Bahaushe, a ranar da a ka haifi mutum ba dole ba ne sai ya zama iyayenshi sun kiyaye kwanan wata da shekara, sai dai a kan yi wani abu mai ban sha’awa shi ne yi wa mutum lakabi da sunan ranar da a ka haife shi.
            Wadanda a ka haifa a ranar Juma’a, a kan kirasu da Danjuma ko Danjummai, mace kuma a kira ta da Jummai ko Juma. Macen da a ka haifa ranar Laraba kuwa sunanta Balaraba, shi namijin Balarabe  ko kuma Bala. Ranar litinin shi ne Dan liti, ranar Talata kuma dan tala.
            Nazarin wadannan sunaye su ma abubuwa ne masu tasiri wanda su na da muhallinsu a ilmin sanin halayyar Jama’a.
            Sauyi a cikin al’umma wani al’amari ne da ya zama wajibi, ba a iya kaucewa sauyi. Ko a na so ko ba a so ya na afkuwa. Kuma wani abun ban sha’awa da sauyi shi ne duk inda mutum ya je a fadin duniyar nan zai shaidi sauyin.
            Haka kuma sauyi kan dauki salon faruwa a cikin karamin lokaci ko kuma lokaci mai tsawo. Wani al’ada na sauyi shi ne idan a ka samu sauyi a wani bangare na al’umma yak an shafi sauran bangarori.
            Misali idan a ka samu sauyi a yanayin auratayya tsakanin mutane, wannan sauyi na iya shafar al’ada, idan sauyin da ya afku a yanayin auratayya ya afku ne ta fuskacin samuwar aure tsakanin kabilu mabambanta ba tare da la’akari da bambanci ba. Za a samu sauyi ne ta yanayin cakuduwar al’adu.
            Wani sauyin mutane ne ke tsara shi yadda zai auku, wani kuma ya na aukuwa ne ba tare da sanin mutane ba. Misali, mutane kan sauya yanayin shigarsu (sanya tufafi) a lokacin da yanayin sanyi ya kankama. Sanyin ke takura mutum ya yi shigan da bai saba da it aba. A wuraren da dusar kankara ke sauka, sai ka ga wannan dusar ta tilasta musu yin wani irin shiga, wanda babu yadda wani a yankin da babu dusar ya yi irinta.
            Cikin sauye sauyen da a ka samu a Nijeriya, mafi tasiri shi ne tasirin al’adar Bature a kasashen da ya mamaye a Afrika. Kamar a Nijeriya, an samu sauye sauye a yanayin zamantakewa; auratayya, buki, aiki (sana’o’i), tsarin abinci, sutura da sauransu.
            Cikin kuskuren da Bature ya tafka a kasashen Afrika shi ne karfa karfan da ya yiwa kakanninmu wurin raba su da al’adunsu, ta hanyar shigo musu da nashi, tare da nuna musu al’adunshi a matsayin mafiya fifiko da dacewa ga rayuwar mutum.
            Su ka fara sanyawa mutane dokokin tara iyali, kayyade haihuwa da auren mace guda daya rak, wai duk a sunan kiyaye bunkasar tattalin arzikin kasa. duk wannan bai kawar da mutanenmu 100% bisa 100% daga al’adunsu ba.
            Amma zuwan zamani, musamman bayyanar al’amarin ‘Globalisation’ dunkulewar duniya wuri guda ya haifar da sauye sauye a al’ummu fiye da tsammani. A yanzu abun da ke faruwa a birnin Ingila, wanda ke zaune a kauyen Neja zai iya kallo kaitsaye, ko dai ta wayar salula ko ta yanar gizo a na’urar kwamfuta ko tashar talabijin.
            Wannan ilmin sanin me ke faruwa a sassa daban daban na duniya ya taimaka wurin samun sauyi a yanayin bukin zagayowar ranar haihuwa. Ta yadda an jima a na kiyaye wacce rana a ka haifi mutum, wanne wata, a wacce shekara.
            Don haka idan shekara ta zagayo, dai dai wannan ranar a cikin watan da a ka haifi mutum, akwai buki na musamman da a ke shiryawa na tunawa da wannan rana ta haihuwa, wasu yaran ma iyayensu ke shirya musu, har zuwa su girma su shiryawa kawunansu.
            Al’adar bukin zagayowar ranar haihuwa, ba a kowacce al’ada ba ne akwai shi. Amma yanzu kuma ya zama a bu mafi wahalan gaske a rasa shi a cikin al’umma, komi kankanta akwai.
            Ya zuwa yanzu ma sauyi ya sake bayyana a yanayin wannan murna na zagayowar ranar haihuwa a Nijeriya. Yadda masu dukiya ke wannan murnar ta bambanta da yadda talakawa ke yi, duk da ya ke talakawan na ta kokarin ko ta halin kaka sai sun kwaikwayi masu kudi, su kuma masu kudin hankoronsu sai sun kwaikwayi turawa.
            A farko farkon bayyanar guguwar sauyin bukin zagayowar ranar haihuwa, yadda a ke taron shi ne a yi alkaki ‘cake’, ‘yan uwa da abokan arziki su taru, a yanka a ci, sannan a yi buki, masu bayar da kyauta ‘gift’ su bayar.
            Wannan al’ada ce ta masu kudi, musamman a Nijeriya, idan su na aikata wani aiki talaka ya fara kwaikwayo, sai su yi kokarin yin kari ko sauya na su don a ga bambanci. Tunda talakawa ma na rufe ido su kwaikwaiyi yanka ‘cake’, sai kuma a ka samu sauyin fara yin babban buki, wanda za a ce ga kalan kayan da a ke so mahalarta su sanya, (misali, bakin wando da jar riga), sannan kuma a kama hayan wani babban otal wanda a can za a yi bukin.
            Wannan sauyi a yanayin bukin zagayowar ranar haihuwa ya sa mata da yawa a yanzu na yin karyar ranar haihuwarsu, wata ma saboda kyaututtukan da samari kan kawo mata, ta kan shirya bukin zagayowar ranar haihuwa sau uku a shekara daya.
            Mafi muhimmanci a yanzu ba wai kiyaye ranar haihuwar ba ne ma kawai, a’a bukin da ke cikin ranar a ke yi mawa, kyautar da za a samu a ke yi mawa, wanda a irin kyaututtukan wata har sabuwar mota fil a ke bata, wata kuma kudade. bukin dai ya zama jari. Toh ku taya ni murna da addu’a, nawa na gaske ne, ni ma ranar haihuwata ta zagayo. Mu hadu mako mai zuwa!
                 

ILLOLIN BANGAR SIYASA DA RIKICIN ZABE GA MATASA

Tabbas matasa na da muhimmancin gaske a kowacce al’umma, tasirinsu ya fi gaban a zura ido kawai ga al’amura ko yanayin yadda su ke gudanar da rayuwa. Wajibi ne da ya hau kan al’umma kan yin tattalin rayuwar matasa, samar da hanyoyin shigar da saqonnin abubuwa masu kyau don su siffantu da su, haka kuma a yi musu bayanin illolin abubuwa marasa kyau don su qaurace musu.
Duk wata qasa da ta ci gaba a wannan duniya, idan ka waiwaiyi sirrin da ke tattare da samuwar wannan ci gaba, za ka ga a hannun matasansu ya ke. Saboda basu yin sakaci a fannin kulawa da rayuwar matasa.
Haqqi ne babba wanda ya rataya a wuyan iyaye da su kasance mataki na farko a inda ‘ya ‘yansu za su koyi tarbiyya, mu’amala da mutane, kiyaye dokokin qasa da oda, kaucewa ayyukan barna da sauransu.
Idan iyaye su ka gaza aikata hakan ga ‘ya ‘yansu, babu tantama a dai dai lokacin da yaron ya kai shekarun girma (Matashi) ya fara mu’amala da wasu abokai a waje za su koya mishi dukkan dabi’un da su ka ga dama. A wasu lokutanma ba sai sun koya mishi ba, yanayin mu’amala a tsakaninshi da su ne zai sa ya riqa kwaikwaiyon yadda su ke tafiyar da rayuwarsu a hankali har ya gina dabi’a.
Wannan ya nuna cewa haqqin iyaye ne, kuma ikon kiyaye ‘ya ‘ya daga fadawa hadurran kwaikwayon halayen banza a waje na hannun iyayen ne. wanda idan a ka samu kaso 60% cikin 100% su na sauke wannan nauyi, za a ga chanji.
Qasashen da su ka ci gaba din nan, doka ce mai qarfi wacce ta tilasta iyaye a kan tarbiyyar ‘ya ‘yansu. Har ma idan iyayen ba su iya yi ba, sai hukuma ta dauki wannan babban aiki, saboda fahimtar irin hadarin da ke tattare da barin matasa cikin halin rashin bambance kyakkyawa da mummuna.
A qasashen Afrika, sai ya kasance kaso mai yawa na iyaye babu ruwansu da halin da ‘ya ‘yansu za su shiga idan har basu dauki nauyin kula da tarbiyyarsu ba. Haka kuma a wannan yanki namu na Afrika, iyaye da dama (sai dai kadan) ba su wani taka rawar a zo a gani wurin hobbasa kan ‘ya ‘yansu su yi karatu.
Halayen banza da aikata duk wani aiki da zai cutar da mutum ko ya janyo asarar dukiya ya na da alaqa da jahilci. Saboda shi jahilci babu abun da ya ke umurtar qwaqwalwa ta aikata face son rai da aiki ba tare da tantancewa tsakanin mai kyau da marar kyau ba.
Wannan shi ne dalilin da ya sa baragurbin ‘yan siyasa, wadanda ba burinsu ganin ci gaban Nijeriya ba, su ke amfani da matasa wurin cimma mummunar manufarsu ta aika aika. Su ne su ke ba matasan makamai da qwayoyi.
daya daga cikin abun da ke tashe a tsakankanin matasa a Nijeriya shi ne bangar siyasa da rikici. Wannan al’amari ya na da matuqar hadarin da idan ba an magance shi ba ne, lallai ba zai taba yiwuwa a mori dimokradiyya ko wanzajjen zaman lafiya ba.
A al’ummun da su ka ci gaba ba qaramin aibu bane a kira mutum da dan bangar siyasa ballantana kuma daya daga cikin masu hura wutar rikicin siyasa, amma a Nijeriya wannan ba komi ba ne. Wannan bangar siyasa ta bambanta da asalin ‘yan sara – suka da mu ke da su, da ‘yan kalare da ‘yan daba.
Duk inda a ka kira wadancan sunaye, musamman a garuruwan Bauchi, Kano da Gombe, suna ne wanda ya shafi matasa masu ayyukan rashin mutunci, rashin da’a da keta haqqoqin al’umma.
Zaben shekarar 1999, wanda tsohon janar, Olusegun Obasanjo ya lashe. Sai dai tun a wannan lokaci ne ya kamata gwamnati ta tashi tsaye a kan rikicin zabe da bangar siyasa a tsakankanin matasa. Wannan irin mummunan dabi’a ta ci gaba da faruwa har a zaben shekarar 2003 da a ka yi. Maimakon a samu sauqe sai dai ma a ka yi ta samun qaruwar dabi’ar bangar siyasa da rikicin zabe ga matasa.
‘Yan siyasa masu mugun nufi a lokuta da dama su na aiki da matasan ne wurin sace akwatunan zabe, kai farmaki, da qone - qonen da su ka sabawa shari’a.
Yanayin da ke fuskantarmu, bisa la’akari da gabatowar babban zaben shekarar 2015, alamu na nuna matasan da ba su da ruwa da tsaki da da kalare, daba ko sara – suka akwai yiwuwar su fada ma irin wannan mummunan aiki na bangar siyasa da rikicin zabe.
A lokacin da a ka yi zaben fid da gwani na jam’iyyu a Nijeriya, an samu rahotannin yadda wasu ‘yan siyasa a jam’iyyun su ka yi amfani da matasa wurin tayar da hankula domin kawai su yi qaurin suna.
Ya kamata ne matasanmu su hankalta, su gane cewa bangar siyasa da rikicin zabe babu wani alheri da su ke haifarwa, sai dai sharruka birjik.
Rahotanni sun adana cewa a rikicin zaben shugaban qasa da ya auku a watan Afrilun 2011 ya yi sanadiyyar rasa rayuka sama da 800, kamar yadda hukumar kare haqqin bil’adama su ka bayyana. Wadanda su ka mutu din an kashe su ne cikin kwanaki uku a jihohin arewa 11, wanda a kasha 90 na kashe – kashen matasa ne su ka aikata, haka ma rikicin zaben matasa ne su ka tayar.
Zaben shekarar 2011 da ya gabata ya tafi ya bar baya ta qura, bilhasali ma ba a taba yin zabe wanda a ka zubar da jinni kamar shi ba. An tarwatsa mutane daga muhallinsu, wasu sun rasa iyaye da ‘yan uwa. Hukumar bayar da tallafin gaggawa ta shaida cewa sama da mutane dubu 65,000 ne su ka bar gidajensu sakamakon rikicin.
Idan matasa su ka hankalta ta hanyar qauracewa bangar siyasa da rikicin zabe, tabbas baragurbin ‘yan siyasa da basu son zaman lafiya a Nijeriya ba za su kai ga cimma burinsu ban a zubar jinin mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.
A matsayinka na matashi, ya kamata ne ‘yan siyasa su taimake ka wurin gina rayuwarka, a samar da ayyukan da matasa za su yi bankwana da zaman banza, a samar musu guraben karatu a makarantun da mu ke da su; wannan shi ne aikin gina rayuwar mutum ba a bashi makami da qwaya ba. Makami da qwaya sai dai rusa rayuwarka, ya zama ba ka da fata nagari ga kanka da al’ummar da ka ke tare da su. Mu hadu mako mai zuwa!



A SIYAR DA RAI A NEMO SUNA!

Haha! Matuqar ka na raye za ka yi gane – gane a duniyan nan, musamman idan ka na mu’amala da mutane barkatai, ko kuma ka na da ikon samun labarun yanayin yadda mutane daban daban daga sassan duniya su ke gudanar da rayuwarsu. A nan ne za ka tabbatarwa da kanka qarfin halin ‘yan neman suna.
Siyar da rai kala kala ne, kuma kusan masu irin wannan dabi’a ta siyar da rai sun san duk wata hanya da za su bi su aikata hakan, a wasu lokutan ta sha rutsawa da su, a wasu lokutan kuma su tsallake rijiya da baya.
Idan a ka ce siyar da rai kawai a ka yi shiru. Sai mutum ya dauka a na nufin a wurin siyar da ran dole sai ya kasance akwai barazana ga rayuwa. Wanda kuma ba haka ba ne, siyar da rai a nemo suna, ya na iya qumsar aikin da zai zubar da mutunci, qima, dattako ko ya rage kaifin wayonka a idon jama’a. wannan shi ne ma babban siyar da rai.
Wasu misalai na siyar da rai amma a ka samo sunan da a ke nema, shi ne irin qeqyashewa da tsayin dakan da tsohon mataimakin shugaban qasa, Alhaji Atiku Abubakar ya yi gab da zaben shekarar 2007. Inda ya fito kaitsaye ya yi fito na fito da muradin mai gidanshi, tsohon shugaban qasa Olusegun Obasanjo.
Siyar da ran da Atiku Abubakar ya yi, a na iya cewa ya ci riba, ya kuma yi suna sosai a wancan lokaci. Musamman yadda ‘yan Nijeriya su ka fara kallonshi a matsayin wani sabon gwarzo, wanda ya rusa sabuwar aqidar ‘Third Term’.
Atiku Abubakar bai tantance fada wa kasadar siyar da rai ba, har sai da ya samu tabbatattun hujjoji a kan maigidanshi Obasanjo ba zai tallafa mishi don ya maye gurbinshi ba. Sannan ya tabbatar da cewa idan har haqar ‘Third Term’’ ta cimma ruwa, shi kam sai dai kuma tarihi. Zabi biyu a wancan lokaci Alhaji Atiku Abubakar ke da su; ko dai ya danne zuciyarshi ya hadiyi haquri da duk wani wulaqanci da zai biyo baya. Ko kuma ya qaddamar da yaqi ba qaqqautawa.
A ‘yan kwanakin baya ma, siyar da ran da Malam Ibrahim Shekarau ya yi babban misali ne, saboda shi kanshi ya san ya siyar da rai ne a matakai biyu; komawa jam’iyyar PDP wacce a baya ya la’ance ta iya la’anta da abubuwan da za su biyo baya na kallon da jama’a za su riqa yi mishi. Na biyu shi ne ya zauna a cikin jam’iyyar adawa ta APC ma siyar da rai ne. bisa dalilin ita uwar jam’iyyar ta qasa ta shardanta cewa duk jihar da gwamna ko mataimakin gwamna ya komo jam’iyyar, shi ne zai zama shugabanta na jiha.
A halin da Malam Shekarau ya tsinci kanshi, ko dai ya zauna a cikin jam’iyyar ta APC qarqashin abokin adawanshi gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso ko kuma ya kama gabanshi (matakin da ya dauka). Qarshenta dai da Malam Ibrahim Shekarau ya duba da kyau, ya natsu ya ga cikin biyun, wanne siyar da rai ne zai zamar mishi mai sauqi sauqi.
Tsoron yin kasadar siyar da rai ne ya hana mutane irinsu Gwamna Sule Lamido, da Gwamna Babangida Aliyu su biye ma takwarrorinsu su Gwamna Aliyu Magatakarda Wamakko, Gwamna Kwankwaso da Gwamna Amaechi. Saboda ba su shirya ba, kar wurin neman suna su kwan ciki.
Wadannan su ne kadan daga cikin misalan siyar da rai a siyasance. Haka nan a mu’amalarmu ta yau da kullum, cike ta ke da siyar da rai. Musamman wadanda babban burinsu shi ne neman suna da son a ce su ne su ka yi kaza da kaza.
Wasu mutanen dabi’arsu kenan a ce su ne su ka fara aikata wani al’amari, ko su ne su ka dai daita wani abu, alhali ba za su yi nazarin me neman sunan nan zai iya janyo musu ba. Shin idan sun siyar da rai, qima da darajar da su ke kwadayi za su samu ko a’a?
Kowanne mutum mai hankali a duniyan nan, ya na da lura da kiyaye abubuwan da kan je kan dawo. Kawai yawancin abun da ke cutar da mutane a wannan zamani shi ne rashin tunani. Kyau a ce duk abun da ka riska ka tsaya ka yi tunani, ka yi nazari na musamman dangane da abun, ka tantance ka cire abubuwan da za su iya shafar mutuncinka ko qima, ko daraja, idan har akwai wadannan barazana masu yawa, sai ka yi haquri kawai.
Saboda mutunci shi ne mutum. Duk lokacin da kaso 40 cikin 100 na jama’an da ke kallonka da mutunci su ka daina, ina mai tabbatar maka da ka rasa wani babban abu a rayuwanka wanda zai yi ta janyo maka asarori na daukaka da amintan jama’a, har zuwa lokacin da za a sake sakankancewa da kai da al’amuranka.
Sau da yawa, ya fi kyautuwa ka yi shiru a abun da bai shafe ka ba. Wasu kan yi alqawuran siyar da rai, don kawai su farantawa mutum rai, alhali idan alqawarin bai cika ba, maimakon su nemo suna, sai dai su zubar da suna.
Daga qarshe ina kira ga masu dabi’ar siyar da rai don neman suna, su taimakawa kansu su rage, saboda ba kowanne siyar da ran ba ne ke tattare da suna. Wani maimakon nemo suna, sai dai ya janyo kuka da raunin da tabonshi ba zai taba gushewa ba. Mu hadu mako mai zuwa!