Saturday, 11 April 2015

SHIN AKWAI AL’ADAR DA TA FI TASIRI?



Mai karatu a wannan makon, wannan shafi zai ta¬o al’ada ne, domin ya na daga cikin muhimman abubuwan da su ka bambanta mutum da dabba, shi ne al’ada.
            Idan ka ga wata al’umma wacce a ka ce ba ta da al’ada, babu makawa kawai ka bugi kirji ka ce rayuwar da mutanen da ke wannan al’umma su ke yi ba ta da bambanci da ta dabbobi.
            Kamar yadda ba a samun wata al’umma da ba ta da al’ada, haka kuma al’ada ma ba zai yiwu ta samu ba har sai akwai al’umma. Dalilin haka ne masana ke cewa, al’ada da al’umma kamar wayar salula ce da memori (memory card).
            Al’adar al’umma ita ce ke nuna ya yarensu ya ke, ya su ke mu’amala da junansu, menene kyakkyawa a wurinsu, menene mummuna a wurinsu. Wadannan na daga kadan daga abubuwan da ke bambanta wannan al’ummar da wacccan al’ummar.
            Kowacce al’umma na gane daya daga cikinta ne ta hanyar al’ada. Ba sai ma mutum ya yi Magana ba ne kawai za a gane daga inda ya ke, daga yanayin sanya tufafi ma kadai al’ummuu na iya bambance na su da wadanda ba na su ba.
            Idan ka ga mutumin yankin Neja Delta sanye da tufafi, zabgegiyar hular malfa ta isa ta bambanta shi da Bayaraben Ikko wanda ke sutura da leshi. Haka kuma idan ka ga asalin bahaushen Arewa ya zubo babbar riga da hular kube, shigar ta isa bayani.
            A wasu lokutan kuma mai wata al’adar na iya sa suturar wata, abun da ke bayyana hakikanin inda ya fito shi ne ya yi furuci, da zaran ya yi, tsamin bakinsa ko kuma tasirin yaren al’adar ba zai bar shi ya yi furuci irin na wani ba.
            Kafin zuwan turawan mulkin mallaka Afrika (musamman wannan kasar ta mu ta Nijeriya), akwai wasu al’adu wadanda a ke yi, amma sakamakon karfa karfa, bature ya dushe wadannan al’adun, ya maye gurbinsu da na shi.
            Kamar misali; yanayin auratayya a wancan lokaci (na kafin zuwan Bature) al’ummu da yawa a tsarin aurensu shi ne su na bayar da ‘ya ‘yansu mata tun a lokacin da a ka haife su. Idan yarinya ta balaga ta ce ita ba ta so, sai iyayenta su tsangwame ta, idan kuma namijin ne ya ce ba ya so, sai dai ya tattara komatsenshi ya bar garin. Irin wannan al’ada ta yi kaurin suna a tsakankanin mutanen garin Chawai da ke Zariya.
            Su kuwa mutanen tsibirin Nuba (nuba hills) a al’adarsu bai haramta ba namiji da mace su sadu ba tare da aure ba. Mace ta na iya zuwa ta kwana a gidan saurayin da ta ke soyayya da shi. Irin wannan al’adar ta dace da wacce mutanen Ashanti ta kasar Ghana ke yi, amma su a al’adarsu, namiji kafin ya yi aure, kanwarsa ko wata ‘yar danginsu ce za ta koya mishi yadda a ke saduwa da mace, (wai) don kar ya janyo musu abun kunya.
            Haka kuma mace na iya saduwa da saurayin da ta ke so. Sai dai su al’ummar Ashanti, idan mace ta yi ciki a wajen gidan aure, hukunci kisa ne a kanta. Idan mace ta yi aure a Ashanti na kasar Ghana, ta haifi mata tagwaye, dukkansu sun zama kadarorin sarki, ma’ana za a lissafa su cikin jerin matan Sarki, sai dai idan mahaifiyar tagwayen sun hada jini da sarkin.
            Aure a al’adar Kanuri, wani samfurin aure ne mai cike da al’ada, tun kafin zuwan turawan mulkin mallaka, auren Kanuri aure ne mai tsadan gaske da cin kudi, idan ka san ba ka da dukiya mai tarin yawa, kar ma ka fara tarbo ma kanka auren ‘yar Kanuri.
            A al’adar Kanuri, idan mutum ya auri mace kuma ya gano cewa shi ne na farko da ya fara saduwa da ita, su kan hada gagarumin buki, sannan akwai wani kaso na tukuici da zai kai gidansu amaryar. Idan kuwa ango ya gano akasin haka, shi ne ya ke fasa tukunya a kofar gida. Auren budurwa a al’adar Kanuri shi ne mafi muhimmanci da tsada, fiye da na bazawara.
            Dukkan wadannan al’adu da na kawo sun fuskanci  sauye sauye bayan zuwan Bature ta hanyar gabatar da na shi al’adar wacce ya ke ganin ita tafi dacewa da mutanen da ya zo ya taras a Afrika.
            Wannan abu da turawan mulkin mallaka su ka yi babban kuskure ne, wanda a ilmance ya sa¬a. saboda a ilmin zamantakewar jama’a, duk mutumin da ke ganin cewa al’adarshi ta fi na wani, wannan mutumin a na mishi kallon wanda bai san me a ke nufi da ‘al’ada’ ba. Haka kuma wanda ya ke ¬oye al’adarshi ya na jin kunyan a danganta shi da al’adar, shi ma wannan bai san me a ke nufi da ‘al’ada’ ba.
            Matsayar masana ilmin zamantakewar jama’a ita ce; babu wata al’ada da ta fi wata a duniya. Dukkan al’adu su na da matsayi da tasiri.
            A dai dai lokacin da ka ke ganin al’adarka ita ce mafificiya, a wurin wasu al’ummun kuma yanayin gudanarwar wannan al’ummar taka shi ne mafi kaskanci.
            Abun nufi a nan kawai shi ne al’adu su ne al’umma, don haka al’umma da kansu ne za su tantance tsakanin mai kyau da mummuna a wurinsu, sannan su samar da tsare tsare na yadda rayuwarsu za ta kasance. Hatta dakushe hasken al’adu da bature ya zo ya yi, wauta ne da kuskure babba, cin zali da danniya, kuma ya sa¬a ma tsarin dan adamtaka. Mu hadu mako mai zuwa

NAZARIN KYAUTA DA ROWA



Mai karatu a wannan makon zan ta~o wasu muhimman abubuwa guda biyu, wadanda ke kishiyantar juna. Kuma dukkaninsu na da alaka da rayuwarmu ta yau da kullum.
            A da ban hankali na bai ta~a zuwa kan wadannan abubuwa ba, saboda ko kadan kwakwalwata ba ta salwanta min muhimmancinsu da kuma tasirinsu a rayuwa ba. Wasu lokuta baya mu na darasi, sai malaminmu ya shigo da batun ‘Kyauta da rowa’, ya yi mana dogon bayani (wanda shi a wurinshi ya takaita). Har ma ya sha alwashin in Allah ya yarda zai yi nazarin kyauta da rowa.         
            Kafin na ci gaba da bayani, akwai wani abu mai sarkakiya wanda ya kamata mu warware shi. Shin kyauta ko rowa a na yin gadonsu ne, ko kuwa koyonsu a ke yi?
            Wannan tambayar ba ta da wani bambanci da tsohuwar tattaunawar nan dangane da dabi’ar dan Adam, wanda wasu ke hakikancewa a kan cewa ai dabi’a tana tattare ne a cikin jininmu, daya ~angaren kuma su ka ce, a na koyon dabi’u ne a cikin al’umma.
            Idan mutum na da yawan kyauta, za ka ji hausawa na cewa ya na da jinin kyauta. Sai dai wannan Karin Magana kadai bai isa madogara gare mu ba, mu yanke hukuncin cewa ai in dai mutum ya hada jini da masu kyauta babu makawa shi ma zai zamo mai kyauta.
            Wannan rusasshen zance ne, idan za mu yi la’akari; misali akwai tagwaye (twins) wadanda a ka haifa a garin Kaduna. Sunansu Hasan da Husaini, tun bayan kwana bakwai da haihuwansu, sai mahaifinsu ya yanke shawarar zai raba su wurare daban daban a hannun kannenshi.
            Da a ka tashi sai a ka kai Hasan kasar Ingila, shi kuma Hussaini a ka kai shi garin Gombe. Har zuwa lokacin da su ka girma su ka fara aiki. Abun lura a nan shi ne, idan Hasan da ke kasar ingila ya taso tare da mutane masu ra’ayin turawa na cewa taimakon talaka kuskure ne, saboda idan yau ka taimaki talaka ba zai mike ya nemi na kanshi ba. Shi kuma Husainin ya taso a wurin mutanen Gombe, wadanda za su iya sadaukar da dukkan abun da ke cikin aljihunsu domin yin hidima ga bako, ko kuma mutanen da ke fito da abinci kofar gida a taru a ci.
            Wannan ya nuna mana a fili cewa Hasan zai koyo rowa matsananciya, shi kuma Husaini zai koyo yadda a ke kyautata ma mutane. Wannan dan gajeren misali kadai ya isa mu gane karfin ikon wurin da mutum ya taso ga halayyenshi, musamman halin kyauta ko rowa.
            Tun a rayuwarmu ta yau da kullum mu kan ga alheran da ke tattare da kyauta, haka kuma mu kan ga sharrrukan da ke tattare da rowa. Mutumin da ke da kyauta, ya kan zama mafi soyuwa a tsakanin mutane, sannan mutane ba za su aminta a hada kai da su wurin cutar da shi ba.
            Akasin haka ga marowaci. Idan mai gida (oga) ya kasance marowaci, babu makawa da yaranshi (ma’aikata) za a hada baki a halaka shi ko a gurgunta al’amuranshi. Saboda ai tsaro ba ya na nufin mai gadi da bindiga ba ne kawai, mafi girman tsaro shi ne tsaro wanda mutum ya samarwa kanshi ta hanyar mallakar zukatan wadanda ya ke tare da su. Idan kai mai arziki ne, amma ma’aikatanka ko da yaushe su na cikin matsanancin wahala. Kenan watan wata rana makiya za su iya ba mai dafa mishi abinci (kuku) guba ya zuba mishi don ya ci ya halaka.
            Sirrin cin moriyar rayuwa na tattare da kyauta. A wasu lokutan ma kyautar da mutane ke yi kanana su na ganinsu ba a bakin komi ba, amma wannan abun alheri zai ci gaba da binsu har ‘ya ‘ya da jikoki.
            Idan kuwa halin ka kenan rowan tsiya, wannan tabon na marowaci, ya yi ta binka kenan. Har ma idan a ka ci sa’a cikin ‘ya ‘yanka ko jikoki a ka samu wani mai halin kyauta, sai ka ji jama’a na cewa Allah sarki mahaifinshi ko Kakanshi marowaci, amma shi kuma mai kyauta.
            Abubuwa biyu ne masu karo da juna. Sai dai ya na da kyau mu gane cewa wadannan halaye guda biyu, al’umma na da hakkin koya wa mutum su. Idan mu ka kasance masu halin kyautatawa, ‘ya ‘yanmu da wadanda ke tare da mu za su taso da wannan hali. Shi ya sa masana halayyan jama’a da zamantakewa su ke cewa al’umma ne ke gina dabi’ar mutum. Mu hadu a mako mai zuwa
           
                              

ABUN DA KE HANA MUTANE NASARA A RAYUWA



Idan da a ce za a bani zabi a ce wannan rubutun shine rubutu na karshe da zan yi a rayuwa na a wannan filin, kuma an bani damar yin rubutu akan wani al’amari guda daya kacal, babu makawa akan wannan abun da ke hana da yawan mutane nasara a rayuwa zan yi, kuma ya ke dankwafe su wuri daya.
            Zan zabi yin haka ne kawai saboda la’akari da irin dabi’ar mutanenmu da kuma halayyansu akan fahimtar nasara a rayuwa. Idan ma da za a ce na ba mutane shawara akan wani abu, lallai ba zai wuce wancan batu ba. kodayake, wannan wani abu ne wanda gabakidaya duniya ke fama da shi, amma mu namu ya yi yawa.
            Watakila wani ya shiga mamakin me na ke son bayyanawa, ko kuma ma wani yace me na ke nufi ne?, muhimmin abu na ke nufi, domin kuwa babban abun da ke hana mutane nasara a rayuwa shine rashin sanin DALILI.
            Da yawan mutane su na kuskurewa a abubuwan da su ka sa a gaba sakamakon rashin sanin muhimmancin DALILI. Shin kana iya tuna wani muhimmin al’amari wanda ka sa a gaba a rayuwarka, wanda ka dauki matakai domin ganin wannan al’amari ya tabbata?. Amma kuma sai daga bisani ka fara yiwa kanka tambaya, kana tantamar anya wannan al’amari mai yiwuwa ne kuwa.
            Dukkanin dan adam na da wani abu wanda ya ke son ya cimma a rayuwarshi, wanda zuciyarshi ne ta wanzar mai da kaunar aikata wannan abu. A kullum mutane marasa adadi ne su ke shiga tsaka mai wuyar kudurin aiwatar da wani muhimmin abu, wani lokaci wanda zai kawo canji ga rayuwarsu.
            Irin wadannan abubuwa su kan hada da son daina shan taba (sigari), neman aiki, fara kasuwanci, neman hanyar daina mu’amala da miyagun mutane, tsara hanyoyin wanzajjen rayuwa cikin koshin lafiya, kiyaye gaskiya, rikon amana. Tabbas da yawan mutane burinsu bai zarce kwanaki ko awanni ya rushe, su koma tamkar ba su yi wannan kuduri ba, saboda tunaninsu bai fadada ba, sun tsuke shi a wuri guda.
Mai karatu!, matukar za ka yi amfani da wannan shawara, babu makawa za ka ga canji a dukkanin abun da ka sa a gaba. Kowanne abu a rayuwa ana cin nasara akanshi ne ta hanyar sanin dalilin aikata shi. Duk kuwa abun da aka surfafeshi ba tare da ayyanannen dalili ba, ko ya kafu zai rushe saboda ba a san don me ake yi ba.
Yawancin al’amuran mutane su na bin kyale kyale ne ko kuma abun da zuciyarsu ta bijirar musu na dan wani lokaci, ko kuma sha’awa, ko kuma ganin wasu na aikatawa, sai wannan ya rinjayesu su kuma karfafa kawunansu akai.
Rashin sanin dalilin aikata abu yana saurin ruguza komi da mutum ya shirya aikatawa. Zan bayyana wasu matakai wadanda idan mutum ya yi nazarinsu, zai fahimci inda na dosa.
Matakin farko shine mutum ya kasance ya sanyawa kanshi RA’AYIN yin abun da yake son aikatawa. Idan kasuwanci ne, aure ne, ko kuma karatu ne. misali, a ba dalibi gurbin karatun karatun kimiyya, ba zai taba ganin fa’idar karatun ba idan bai da ra’ayin yi.
Sai mataki na biyu kuma mutum ya san DALILIN da ya sa yake son aikatawa. Ka yiwa kanka wannan tambayar, shin menene dalilin da ya sa ka ke son aikatawa?, me zai biyo baya idan ba ka yi nasara ba?, wannan abu da ka ke son aikatawa zai iya cutar da mutanen da kake tare da su?, idan ka yi nasara, ya rayuwarka zata kasance?. Don haka dole ne sai ka san dalilin da ya sa ka yi ra’ayin aikatawa. Idan har ka kasa samarwa kanka dalilin kowanne mataki da za ka dauka, akwai tsammanin rashin yin nasara.
Ba wai kawai ginuwa akan ra’ayi  da kuma sanin dalilin aikata abu ba. babban abun lura wanda kuma ya ke da muhimmancin gaske, shine mutum ya adana a zuciyarshi ba tare da ya manta ba ko da na dakika guda cewa yana da dalilin matakan da yake dauka a abun da yake aikatawa.
Na san wanda ya fahimci inda na dosa zai gano bakin zaren bayanin, domin kuwa wani abu ne wanda yake a fili kuma mu ke rayuwa a cikinshi yau da kullum, ba zai yiwu mu guje daga gareshi ba, mafi kyautuwa shine mu yi aiki da shi domin samun nasara a al’amuranmu, shine sanin DALILIN da ya sa za mu aikata abu. Ruwan alkalamina ya kare, sai na yi sabon zubi.

KOWANNE MUTUM ABUN ZARGI NE 'Suspect'



Kullum na tuna da wata ‘yar dirama da mu ka yi da wani malami, sai na kai kas ina dariya. Ranar da na fara jin wannan batu na cewa kowanne dan adam abun zargi ne a aji ne lokacin a na koyar da mu darasin ginshikan ilmin halayyar jama’a ‘Element of Sociology’.
            Dai dai lokacin da malamin ya ce ‘kowanne mutum abun zargi ne’, sai gabaki daya ajin ya yi tsit a na mamakin irin wannan wuce gona da iri. Shi kuwa da ya ga haka sai ya ce ko akwai mai jayayya ne?. sai wani ya mike ya ce kamar ya abun zargi?
            Mai karatu wannan makon zan yi bayani ne dangane da dalilan da su ka sa a fannin sanin halayyar jama’a ‘Sociology’ a ke cewa kowa ma abun zargi ne. Saboda na jima ina haduwa da mutanen da ke ganin maganar a matsayin shaci-fadi, a wurin wasu ma zancen bur ne.
            Ba zai yiwu zargi ya zo ba har sai idan akwai wani wanda ya aikata barna, saba doka da oda, ko kuma laifuka kanana da manya. Idan a ka aikata laifi, sai ya zama wanda ya aikata laifin ya gudu ba tare da wani ya riske shi ba, sannan ne za a fara zargin wadanda zai iya yiwuwa su aikata.
            Kacokaf din barna ‘Crime’ ta kasance ta na samar da abubuwa da daman gaske, wadanda idan da babu ita, ba za a same su ba. Misali anan shi ne, idan da ba barna da ba zai zama kwata – kwata akwai wani abu wai shi zargi ba.
            Haka nan kuma akwai wani magana mai karfi a fannin sanin halayyar jama’a (sociology) wanda wani mashahurin masanin fannin Emile Durkheim ya ke cewa ‘|arna na da amfanoni ga rayuwar mutane’. Wannan magana na Durkheim na daga cikin zantuka wadanda ba su fuskancin kakkausar suka ba a fannin. |arna ne ta samar da aikin tsaro, wanda kuma aikin ya zama hanyar cin abinci mutane da yawan gaske. Irinsu Jami’an tsaro, lauyoyi, alkalai, masu tsaron kurkuku da sauransu.
            Idan har mun gamsu cewa barna na da amfani komi kankantarshi ga al’umma, sai kuma wani batun da ke cewa ‘babu wata al’umma da ke rayuwa ba barna a cikinta’. Idan ba ka fahimce ni ba, haka nan dai na ke nufi. Ka kawo min al’umma (society) tun da a ka kafa duniya har zuwa yanzu wacce babu barna ko kadan a cikinta.
            Kawai dabarar da a ka yi shi ne a na amfani da matakai mabambanta domin ganin an rage karfin barna a cikin al’umma, idan ma ka ce za ka yi fada da barna ne domin ka kawo karshenta, lallai za ka gama wahala ka bari ne, saboda dabi’ar mutum ne sabawa duk abun da a ka nemi tilasta mai.
            Sanin haka ne ya sa a cikin ilmin sanin halayyar jama’a (Sociology) a ka fitar da wani darasi wanda a ke kira ‘Criminology’ don a horas da wasu zarata wadanda za su yi wa barna da mabarnata tarkon rage kaifinsu.
               Don an ce kowanne mutum abun zargi (suspect) ne ba wani abu ne mai nauyin a fahimta ba. ba ma sai na shigar da ku fannin ilmin halayyar jama’a ba, saboda idan ta wannan bangaren zan dora bayani na zan dauki watanni ina zubo rubutu ba tare da kammalawa ba.
             Yanzu da a ke cikin halin rashin tsaro a Nijeriya, kodayaushe babu kwanciyar hankali. A gefe guda jami’an tsaron gwamnati na ta farautar wadanda ke tayar da zaune tsaye musamman ma su dashe dashen bama bamai.
            Su kuma a bangaren masu dasa bama bamai, da harbe harben jami’an tsaro ba a bayyane su ke ba. kullum cikin buya su ke, a wannan buyan ne kuma su ke shirya yadda za su gudanar da ayyukansu ba tare da an sani ba.
            Misali, ka na da wani aboki wanda tun tasowarku tare ku ka yi yarinta, hatta makaranta tun daga firamare har jami’a daya ku ka yi. kuma ku ka yi sa a wurin aikinku daya. Ka shaidi abokin nan na ka mutum kirki, ba ya son rigima ballantana tashin hankali. Kwatsam!. Sai a wayi gari da asuba gabakidaya kafafen yada labarai sun dauko labarin cewa an cafke aminin nan na ka da laifin dasa bam. Shin ba zai zamar ma ka abun mamaki da waswasi ba?.
            Wani misalin anan shi ne kana da dan uwa wanda ku ke uwa daya uba daya. Sai labari ya same ka cewa ga shi can an kama shi cikin masu dana bom. Kuma kai ka san ko dan yatsa a ka sa mai a baki ba zai ciza ba, anya ba za ka shiga rudanin samun shakkun kama shi ba?.
            Shi ya sa a ka ce kowanne mutum abun zargi ne. Saboda mutum ya na da wata dabi’a bahaguwa sannan yana da badamiya. Son zuciya ita ce bahaguwar dabi’a wacce kuma bincike ya tabbatar da cewa ta na da wahalar dannewa. Idan ka sa a ranka cewa kowa abun zargi ne, ba za ka rude ba duk lokacin da wani ya aikata laifi mai girma.
            Da wannan na ke so a gane cewa babu batun yarda ko aminci dari bisa dari. Wanda ka yarda da shi dari bisa dari shi ma dan adam ne, zai iya bin son zuciyarshi har ya aikata barna.