Saturday, 11 April 2015

KOWANNE MUTUM ABUN ZARGI NE 'Suspect'



Kullum na tuna da wata ‘yar dirama da mu ka yi da wani malami, sai na kai kas ina dariya. Ranar da na fara jin wannan batu na cewa kowanne dan adam abun zargi ne a aji ne lokacin a na koyar da mu darasin ginshikan ilmin halayyar jama’a ‘Element of Sociology’.
            Dai dai lokacin da malamin ya ce ‘kowanne mutum abun zargi ne’, sai gabaki daya ajin ya yi tsit a na mamakin irin wannan wuce gona da iri. Shi kuwa da ya ga haka sai ya ce ko akwai mai jayayya ne?. sai wani ya mike ya ce kamar ya abun zargi?
            Mai karatu wannan makon zan yi bayani ne dangane da dalilan da su ka sa a fannin sanin halayyar jama’a ‘Sociology’ a ke cewa kowa ma abun zargi ne. Saboda na jima ina haduwa da mutanen da ke ganin maganar a matsayin shaci-fadi, a wurin wasu ma zancen bur ne.
            Ba zai yiwu zargi ya zo ba har sai idan akwai wani wanda ya aikata barna, saba doka da oda, ko kuma laifuka kanana da manya. Idan a ka aikata laifi, sai ya zama wanda ya aikata laifin ya gudu ba tare da wani ya riske shi ba, sannan ne za a fara zargin wadanda zai iya yiwuwa su aikata.
            Kacokaf din barna ‘Crime’ ta kasance ta na samar da abubuwa da daman gaske, wadanda idan da babu ita, ba za a same su ba. Misali anan shi ne, idan da ba barna da ba zai zama kwata – kwata akwai wani abu wai shi zargi ba.
            Haka nan kuma akwai wani magana mai karfi a fannin sanin halayyar jama’a (sociology) wanda wani mashahurin masanin fannin Emile Durkheim ya ke cewa ‘|arna na da amfanoni ga rayuwar mutane’. Wannan magana na Durkheim na daga cikin zantuka wadanda ba su fuskancin kakkausar suka ba a fannin. |arna ne ta samar da aikin tsaro, wanda kuma aikin ya zama hanyar cin abinci mutane da yawan gaske. Irinsu Jami’an tsaro, lauyoyi, alkalai, masu tsaron kurkuku da sauransu.
            Idan har mun gamsu cewa barna na da amfani komi kankantarshi ga al’umma, sai kuma wani batun da ke cewa ‘babu wata al’umma da ke rayuwa ba barna a cikinta’. Idan ba ka fahimce ni ba, haka nan dai na ke nufi. Ka kawo min al’umma (society) tun da a ka kafa duniya har zuwa yanzu wacce babu barna ko kadan a cikinta.
            Kawai dabarar da a ka yi shi ne a na amfani da matakai mabambanta domin ganin an rage karfin barna a cikin al’umma, idan ma ka ce za ka yi fada da barna ne domin ka kawo karshenta, lallai za ka gama wahala ka bari ne, saboda dabi’ar mutum ne sabawa duk abun da a ka nemi tilasta mai.
            Sanin haka ne ya sa a cikin ilmin sanin halayyar jama’a (Sociology) a ka fitar da wani darasi wanda a ke kira ‘Criminology’ don a horas da wasu zarata wadanda za su yi wa barna da mabarnata tarkon rage kaifinsu.
               Don an ce kowanne mutum abun zargi (suspect) ne ba wani abu ne mai nauyin a fahimta ba. ba ma sai na shigar da ku fannin ilmin halayyar jama’a ba, saboda idan ta wannan bangaren zan dora bayani na zan dauki watanni ina zubo rubutu ba tare da kammalawa ba.
             Yanzu da a ke cikin halin rashin tsaro a Nijeriya, kodayaushe babu kwanciyar hankali. A gefe guda jami’an tsaron gwamnati na ta farautar wadanda ke tayar da zaune tsaye musamman ma su dashe dashen bama bamai.
            Su kuma a bangaren masu dasa bama bamai, da harbe harben jami’an tsaro ba a bayyane su ke ba. kullum cikin buya su ke, a wannan buyan ne kuma su ke shirya yadda za su gudanar da ayyukansu ba tare da an sani ba.
            Misali, ka na da wani aboki wanda tun tasowarku tare ku ka yi yarinta, hatta makaranta tun daga firamare har jami’a daya ku ka yi. kuma ku ka yi sa a wurin aikinku daya. Ka shaidi abokin nan na ka mutum kirki, ba ya son rigima ballantana tashin hankali. Kwatsam!. Sai a wayi gari da asuba gabakidaya kafafen yada labarai sun dauko labarin cewa an cafke aminin nan na ka da laifin dasa bam. Shin ba zai zamar ma ka abun mamaki da waswasi ba?.
            Wani misalin anan shi ne kana da dan uwa wanda ku ke uwa daya uba daya. Sai labari ya same ka cewa ga shi can an kama shi cikin masu dana bom. Kuma kai ka san ko dan yatsa a ka sa mai a baki ba zai ciza ba, anya ba za ka shiga rudanin samun shakkun kama shi ba?.
            Shi ya sa a ka ce kowanne mutum abun zargi ne. Saboda mutum ya na da wata dabi’a bahaguwa sannan yana da badamiya. Son zuciya ita ce bahaguwar dabi’a wacce kuma bincike ya tabbatar da cewa ta na da wahalar dannewa. Idan ka sa a ranka cewa kowa abun zargi ne, ba za ka rude ba duk lokacin da wani ya aikata laifi mai girma.
            Da wannan na ke so a gane cewa babu batun yarda ko aminci dari bisa dari. Wanda ka yarda da shi dari bisa dari shi ma dan adam ne, zai iya bin son zuciyarshi har ya aikata barna. 

ILLOLIN BANGAR SIYASA DA RIKICIN ZABE GA MATASA

Tabbas matasa na da muhimmancin gaske a kowacce al’umma, tasirinsu ya fi gaban a zura ido kawai ga al’amura ko yanayin yadda su ke gudanar da rayuwa. Wajibi ne da ya hau kan al’umma kan yin tattalin rayuwar matasa, samar da hanyoyin shigar da saqonnin abubuwa masu kyau don su siffantu da su, haka kuma a yi musu bayanin illolin abubuwa marasa kyau don su qaurace musu.
            Duk wata qasa da ta ci gaba a wannan duniya, idan ka waiwaiyi sirrin da ke tattare da samuwar wannan ci gaba, za ka ga a hannun matasansu ya ke. Saboda basu yin sakaci a fannin kulawa da rayuwar matasa.
            Haqqi ne babba wanda ya rataya a wuyan iyaye da su kasance mataki na farko a inda ‘ya ‘yansu za su koyi tarbiyya, mu’amala da mutane, kiyaye dokokin qasa da oda, kaucewa ayyukan barna da sauransu.
            Idan iyaye su ka gaza aikata hakan ga ‘ya ‘yansu, babu tantama a dai dai lokacin da yaron ya kai shekarun girma (Matashi) ya fara mu’amala da wasu abokai a waje za su koya mishi dukkan dabi’un da su ka ga dama. A wasu lokutanma ba sai sun koya mishi ba, yanayin mu’amala a tsakaninshi da su ne zai sa ya riqa kwaikwaiyon yadda su ke tafiyar da rayuwarsu a hankali har ya gina dabi’a.
            Wannan ya nuna cewa haqqin iyaye ne, kuma ikon kiyaye ‘ya ‘ya daga fadawa hadurran kwaikwayon halayen banza a waje na hannun iyayen ne. wanda idan a ka samu kaso 60% cikin 100% su na sauke wannan nauyi, za a ga chanji.
            Qasashen da su ka ci gaba din nan, doka ce mai qarfi wacce ta tilasta iyaye a kan tarbiyyar ‘ya ‘yansu. Har ma idan iyayen ba su iya yi ba, sai hukuma ta dauki wannan babban aiki, saboda fahimtar irin hadarin da ke tattare da barin matasa cikin halin rashin bambance kyakkyawa da mummuna.
            A qasashen Afrika, sai ya kasance kaso mai yawa na iyaye babu ruwansu da halin da ‘ya ‘yansu za su shiga idan har basu dauki nauyin kula da tarbiyyarsu ba. Haka kuma a wannan yanki namu na Afrika, iyaye da dama (sai dai kadan) ba su wani taka  rawar a zo a gani wurin hobbasa kan ‘ya ‘yansu su yi karatu.
            Halayen banza da aikata duk wani aiki da zai cutar da mutum ko ya janyo asarar dukiya ya na da alaqa da jahilci. Saboda shi jahilci babu abun da ya ke umurtar qwaqwalwa ta aikata face son rai da aiki ba tare da tantancewa tsakanin mai kyau da marar kyau ba.
            Wannan shi ne dalilin da ya sa baragurbin ‘yan siyasa, wadanda ba burinsu ganin ci gaban Nijeriya ba, su ke amfani da matasa wurin cimma mummunar manufarsu ta aika aika. Su ne su ke ba matasan makamai da qwayoyi.
            Daya daga cikin abun da ke tashe a tsakankanin matasa a Nijeriya shi ne bangar siyasa da rikici. Wannan al’amari ya na da matuqar hadarin da idan ba an magance shi ba ne, lallai ba zai taba yiwuwa a mori dimokradiyya ko wanzajjen zaman lafiya ba.
            A al’ummun da su ka ci gaba ba qaramin aibu bane a kira mutum da dan bangar siyasa ballantana kuma daya daga cikin masu hura wutar rikicin siyasa, amma a Nijeriya wannan ba komi ba ne. Wannan bangar siyasa ta bambanta da asalin ‘yan sara – suka da mu ke da su, da ‘yan kalare da ‘yan daba.
            Duk inda a ka kira wadancan sunaye, musamman a garuruwan Bauchi, Kano da Gombe, suna ne wanda ya shafi matasa masu ayyukan rashin mutunci, rashin da’a da keta haqqoqin al’umma.
            Zaben shekarar 1999, wanda tsohon janar, Olusegun Obasanjo ya lashe. Sai dai tun a wannan lokaci ne ya kamata gwamnati ta tashi tsaye a kan rikicin zabe da bangar siyasa a tsakankanin matasa. Wannan irin mummunan dabi’a ta ci gaba da faruwa har a zaben shekarar 2003 da a ka yi. Maimakon a samu sauqe sai dai ma a ka yi ta samun qaruwar dabi’ar bangar siyasa da rikicin zabe ga matasa.
            ‘Yan siyasa masu mugun nufi a lokuta da dama su na aiki da matasan ne wurin sace akwatunan zabe, kai farmaki, da qone - qonen da su ka sabawa shari’a.
            Yanayin da ke fuskantarmu,  bisa la’akari da gabatowar babban zaben shekarar 2015, alamu na nuna matasan da ba su da ruwa da tsaki da da kalare, daba ko sara – suka akwai yiwuwar su fada ma irin wannan mummunan aiki na bangar siyasa da rikicin zabe.
            A lokacin da a ka yi zaben fid da gwani na jam’iyyu a Nijeriya, an samu rahotannin yadda wasu ‘yan siyasa a jam’iyyun su ka yi amfani da matasa wurin tayar da hankula domin kawai su yi qaurin suna.
            Ya kamata ne matasanmu su hankalta, su gane cewa bangar siyasa da rikicin zabe babu wani alheri da su ke haifarwa, sai dai sharruka birjik.
            Rahotanni sun adana cewa a rikicin zaben shugaban qasa da ya auku a watan Afrilun 2011 ya yi sanadiyyar rasa rayuka sama da 800, kamar yadda hukumar kare haqqin bil’adama su ka bayyana. Wadanda su ka mutu din an kashe su ne cikin kwanaki uku a jihohin arewa 11, wanda a kasha 90 na kashe – kashen matasa ne su ka aikata, haka ma rikicin zaben matasa ne su ka tayar.
            Zaben shekarar 2011 da ya gabata ya tafi ya bar baya ta qura, bilhasali ma ba a taba yin zabe wanda a ka zubar da jinni kamar shi ba. An tarwatsa mutane daga muhallinsu, wasu sun rasa iyaye da ‘yan uwa. Hukumar bayar da tallafin gaggawa ta shaida cewa sama da mutane dubu 65,000 ne su ka bar gidajensu sakamakon rikicin.
            Idan matasa su ka hankalta ta hanyar qauracewa bangar siyasa da rikicin zabe, tabbas baragurbin ‘yan siyasa da basu son zaman lafiya a Nijeriya ba za su kai ga cimma burinsu ban a zubar jinin mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.
            A matsayinka na matashi, ya kamata ne ‘yan siyasa su taimake ka wurin gina rayuwarka, a samar da ayyukan da matasa za su yi bankwana da zaman banza, a samar musu guraben karatu a makarantun da mu ke da su; wannan shi ne aikin gina rayuwar mutum ba a bashi makami da qwaya ba. Makami da qwaya sai dai rusa rayuwarka, ya zama ba ka da fata nagari ga kanka da al’ummar da ka ke tare da su. Mu hadu mako mai zuwa!
           
             
             

A SIYAR DA RAI A NEMO SUNA!



Haha! Matukar ka na raye za ka yi gane – gane a duniyan nan, musamman idan ka na mu’amala da mutane barkatai, ko kuma ka na da ikon samun labarun yanayin yadda mutane daban daban daga sassan duniya su ke gudanar da rayuwarsu. A nan ne za ka tabbatarwa da kanka karfin halin ‘yan neman suna.
            Siyar da rai kala kala ne, kuma kusan masu irin wannan dabi’a ta siyar da rai sun san duk wata hanya da za su bi su aikata hakan, a wasu lokutan ta sha rutsawa da su, a wasu lokutan kuma su tsallake rijiya da baya.
            Idan a ka ce siyar da rai kawai a ka yi shiru. Sai mutum ya dauka a na nufin a wurin siyar da ran dole sai ya kasance akwai barazana ga rayuwa. Wanda kuma ba haka ba ne, siyar da rai a nemo suna, ya na iya kumsar aikin da zai zubar da mutunci, kima, dattako ko ya rage kaifin wayonka a idon jama’a. wannan shi ne ma babban siyar da rai.
            Wasu misalai na siyar da rai amma a ka samo sunan  da a ke nema, shi ne irin kekyashewa da tsayin dakan da tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya yi gab da zaben shekarar 2007. Inda ya fito kaitsaye ya yi fito na fito da muradin mai gidanshi, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.
            Siyar da ran da Atiku Abubakar ya yi, a na iya cewa ya ci riba, ya kuma yi suna sosai a wancan lokaci. Musamman yadda ‘yan Nijeriya su ka fara kallonshi a matsayin wani sabon gwarzo, wanda ya rusa sabuwar akidar ‘Third Term’.
            Atiku Abubakar bai tantance fada wa kasadar siyar da rai ba, har sai da ya samu tabbatattun hujjoji a kan maigidanshi Obasanjo ba zai tallafa mishi don ya maye gurbinshi ba. Sannan ya tabbatar da cewa idan har hakar ‘Third Term’’ ta cimma ruwa, shi kam sai dai  kuma tarihi. Zabi biyu a wancan lokaci Alhaji Atiku Abubakar ke da su; ko dai ya danne zuciyarshi ya hadiyi hakuri da duk wani wulakanci da zai biyo baya. Ko kuma ya kaddamar da yaki ba kakkautawa.
            A ‘yan kwanakin baya ma, siyar da ran da Malam Ibrahim Shekarau ya yi babban misali ne, saboda shi kanshi ya san ya siyar da rai ne a matakai biyu; komawa jam’iyyar PDP wacce a baya ya la’ance ta iya la’anta da abubuwan da za su biyo baya na kallon da jama’a za su rika yi mishi. Na biyu shi ne ya zauna a cikin jam’iyyar adawa ta APC ma siyar da rai ne. bisa dalilin ita uwar jam’iyyar ta kasa ta shardanta  cewa duk jihar da gwamna ko mataimakin gwamna ya komo jam’iyyar, shi ne zai zama shugabanta na jiha.
            A halin da Malam Shekarau ya tsinci kanshi, ko dai ya zauna a cikin jam’iyyar ta APC karkashin abokin adawanshi gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso ko kuma ya kama gabanshi (matakin da ya dauka). Karshenta dai da Malam Ibrahim Shekarau ya duba da kyau, ya natsu ya ga cikin biyun, wanne siyar da rai ne zai zamar mishi mai sauki sauki.
            Tsoron yin kasadar siyar da rai ne ya hana mutane irinsu Gwamna Sule Lamido, da Gwamna Babangida Aliyu su biye ma takwarrorinsu su Gwamna Aliyu Magatakarda Wamakko, Gwamna Kwankwaso da Gwamna Amaechi. Saboda ba su shirya ba, kar wurin neman suna su kwan ciki.
            Wadannan su ne kadan daga cikin misalan siyar da rai a siyasance. Haka nan a mu’amalarmu ta yau da kullum, cike ta ke da siyar da rai. Musamman wadanda babban burinsu shi ne neman suna da son a ce su ne su ka yi kaza da kaza.
             Wasu mutanen dabi’arsu kenan a ce su ne su ka fara aikata wani al’amari, ko su ne su ka dai daita wani abu, alhali ba za su yi nazarin me neman sunan nan zai iya janyo musu ba. Shin idan sun siyar da rai, kima da darajar da su ke kwadayi za su samu ko a’a?
            Kowanne mutum mai hankali a duniyan nan, ya na da lura da kiyaye abubuwan da kan je kan dawo. Kawai yawancin abun da ke cutar da mutane a wannan zamani shi ne rashin tunani. Kyau a ce duk abun da ka riska ka tsaya ka yi tunani, ka yi nazari na musamman dangane da abun, ka tantance  ka cire abubuwan da za su iya shafar mutuncinka ko kima, ko daraja, idan har akwai wadannan barazana masu yawa, sai ka yi hakuri kawai.
            Saboda mutunci shi ne mutum. Duk lokacin da kaso 40 cikin 100 na jama’an da ke kallonka da mutunci su ka daina, ina mai tabbatar maka da ka rasa wani babban abu a rayuwanka wanda zai yi ta janyo maka asarori na daukaka da amintan jama’a, har zuwa lokacin da za a sake sakankancewa da kai da al’amuranka.
            Sau da yawa, ya fi kyautuwa ka yi shiru a abun da bai shafe ka ba. Wasu kan yi alkawuran siyar da rai, don kawai su farantawa mutum rai, alhali idan alkawarin bai cika ba, maimakon su nemo suna, sai dai su zubar da suna.
            Daga karshe ina kira ga masu dabi’ar siyar da rai don neman suna, su taimakawa kansu su rage, saboda ba kowanne siyar da ran ba ne ke tattare da suna. Wani maimakon nemo suna, sai dai ya janyo kuka da raunin da tabonshi ba zai taba gushewa ba. Mu hadu mako mai zuwa!

MAMA DAME PATIENCE: WAHIDI IYA!



Lallai sauyi ya zo; wata rana ina zaune a kofar gida, na jima ban ji almajiri na bara ba (neman taimakon abinci), bayan sallar Isha’i ne. kawai sai na ji wani ya zo, abun da ya bani mamaki shi ne sai da ya yi sallama. Ni a baya ban san almajirai na sallama ba kafin su fara bara.
            Ya ce; “Assalamu Alaikum, wahidi iya, sabida Allah, a taimaki almajiri Iya, domin Allah, don Kur’ani, ko dan kanzo, ko gaya ne ba miya Iya, Iya yunwa ba ta da hankali.”
            Har abada duniya  ba za ta manta da tarihin siyasar Nijeriya ba, musamman a zamanin dimokradiyya wacce ta faro daga shekarar 1999 bayan gushewar mulkin Soja sakamakon faduwar gwamnatin Janar Sani Abacha ta hanyar mutuwa.
            A lokacin sai wadanda a ke gani a matsayin jiga jigai a dukkan fannoni na Nijeriya, su ka kirkiri jam’iyyar PDP, wacce ita ta fara mulkin farar hula na dimokradiyya, bayan zagayowar shekaru hudu cur, a shekarar 2003 jam’iyyar ta ci gaba daga inda ta tsaya, wasu shekaru hudun su ka zo, a shekarar 2007 jam’iyyar PDP din ne dai. Bayan an lashe wasu shekaru hudun, a shekarar 2011 labarin dai shi ne babu wani canji, PDP.
            Wannan tagomashi da nasara, da karfi da izza da jam’iyyar PDP ke ganin ta samu, wanda a hakikanin gaskiya akwai karfin, kuma wannan karfi ya tsole ma ‘yan Nijeriya ido, karfin ya takurawa ‘yan Nijeriya musamman talakawa.
            Hatta jiga jigai, wasu ma da su a ka kafa jam’iyyar PDP idan masu mulki ko uwa a bakin murhu su ka yi wani siddabarun wanda ya saba da hankalinsu, ba su isa su ce uffan ba; ko dai su yi shiru ko kuma su yi magana a tsangwame su, idan ma ba su yi sa’a ba, sai a yi amfani da wannan karfi a toshe su, a kashe kaifin tasirinsu.
            Wannan karfi na jam’iyyar PDP ya sa a yawancin lokuta a ke kiranta da giwar jam’iyya a nahiyar Afrika. Duk wani abu da jam’iyyar PDP ta sa a gaba, zaman lafiya da kwanciyar hankalin kowa shi ne ta kai ga nasara, saboda idan ba haka ba, kowa zai ji a jikinsa.
            Hatta al’amarin da ya auku a shekarar 2011 na kone konen muhallan ‘yan jam’iyyar PDP a Arewa, sakamakon zargin murda murda a wasu jihohi. Maimakon ya nuna karshen kaskanci ga jam’iyyar, sai dai ma ya zama hannun jari ga ‘ya yan jam’iyyar da a ka kone ma gidaje da dukiyoyi. Idan an kona maka gida, uwar jam’iyyar za ta mayar maka da wani sabon gida a unguwar da ta fi na ka, da kayan bukatun rayuwa cike da gidan, sannan ta gyara maka gidanka fiye da baya.
            Idan dukiya a ka lahanta ma, za su mayar ma da ninkinta ba tare da dar dar ko faduwar gaba ba. Irin wannan nuna karfi da isa na jam’iyyar PDP ne ya kwantar da hankalin ‘ya ‘yan jam’iyyar, har su ke ganin shekaru 60 da su ke mafarkin za su yi su na mulkar Nijeriya, babu makawa sai sun kai cur sannan za su takawa tafiyar burki (shi ma idan sun so).
            ‘Ya ‘yan jam’iyyar PDP, musamman manyan jam’iyya sun dau wani irin girman kai da dagawa sun jibgawa kawunansu. Wannan zakin karfin jam’iyyar PDP ne ya yaudari mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo ya ke cewa babu wasu dattawa a Arewa sai shi. Shi a iya ka tunaninsa dattijontaka shi ne karfin ikon taka duk wanda ka so, tare da juya duk abun da ka so.
            Shi bai san cewa dattijo, natsattse ba ne, kammalalle wanda ya san ya kamata, ya ke kiyaye hakkokin wadanda Allah ya ba shi aron karfi a kansu, ba wai ya yi amfani da karfin wurin danne duk wanda ya nuna mishi yatsa ba.
            Wannan zakin karfin jam’iyyar PDP ne ya sa mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo duk ranar da zai shiga Kaduna a karshen mako, mutane da yawan gaske su kan rasa kasuwancinsu, saboda jami’an tsaro na tarwatsa duk wata hidima da ta shafi hanyar da zai bi. Maimakon a matsayinshi na mai ikirarin dattijo ya kiyaye irin wannan.
            Wani babban abun mamaki shi ne irin nuna isa da karfin iko da matar shugaban kasar Nijeriya , Madam Dame Patience Jonathan, wacce a kafafen watsa labaru a ke yi mata lakabi da ‘Mama Peace’ wai maman zaman lafiya.
            Ka na kallon fuskan Mama Dame Patience ba ka bukatar a ce ma ka irin mutanen nan ne da ke sako magana ba dadin ji. Tun bayan da Allah ya dauki rayuwar marigayi Umaru Musa ‘Yar’aduwa, mataimakinshi shugaba Goodluck Ebele Jonathan ya maye kujerar, Mama Patience ta fara zubo maganganu, har ta kai ‘yan kasa na tsokanarta, musamman a fannin gurbataccen turanci da ta kware a kansa.
            Lokacin da babban zabe ya matso a shekarar 2015, Mama Patience ta yi ta sakin layi, sai dai abun bai wuce gona da iri ba, har sai bayan da a ka dage zaben shugaban kasa zuwa 28 ga watan Maris, daga nan ne fa ta karbi ragamar yakin nemawa mijinta dawwama a kujerarsa.
            Duk inda ta je yawon kamfen sai ta kafa tarihi, bakin tarihi ga Nijeriya da bakin fenti ga matsayin uwargidan Shugaban kasa. Wani wurin ta ce ai Janar Buhari kwakwalwarshi ta zama jabu, ta kusa daina aiki. Me za a ci da mutum tsofai – tsofai, zai zo ya na takara da ‘ya ‘yan cikinshi. A jihar Ribas cewa ta yi, duk wanda ya zo ya ce musu chanji, su yi mishi jifan rajamu ba kakkautawa.
            Mafi munin sakin bakin ‘Mama Peace’ shi ne inda ta ke cewa wai mai gidanta bai bukatar kuri’un ‘yan Arewa. Mutanen da ba su da aiki sai haihuwar yara su na zubarwa a titi, karshe su zama Almajirai.
            Lallai fa MAMA kin ga aikin almajirai. Su ne dai su ka yi ruwan miliyoyin kuri’u daga jihohin Kano, Katsina. Mama almajiran jihar Kaduna, Yobe, Sakkwato da Zamfara duk sun ki su zabi mijinki. Almajiran jihar Adamawa, da na jihar Kebbi duk sun ki jefa ma mijinki ne saboda kin ce a kai kuri’unsu kasuwa. Mama almajiran jihar Borno sun jima cikin kuncin kisan gilla, dole ta sa su ka ce, su dai PDP Sam!
            Mama Patience baki shi ke yanka wuya; maimakon ki ja bakinki ki yi shiru, ga shi yanzu kin janyowa mijinki asarar kuri’un dukkan almajiran Arewa, ‘ya ‘yan da kika yiwa kazafin a na banzantar da su a titi.
            Cikin fushi da hasala da irin wadannan kalamai na ki marasa fasali da dadin ji, almajiran nan su ka yi mursisi, su ka yi ta ruwan kuri’u ga babban almajiri, mutumin da ki ka kira da tsofai tsofai, wanda ki ka ce kwakwalwarsa ta mace; shi din dai, da wannan kwakwalwa ya yi tasiri a kan mutanen yankin Yarbawa. Mama ya ki ka ga aikin mutanen Osun, Oyo, Legas? Mama mutanen Binuwai ma sun fusata, watakila su ma almajiran ne, domin babban almajiri Janar Buhari tsaf ya cinye jihar.
            Mama na san sarai kin kasance a gaban akwatun talabijin dinki, a dai dai lokacin da dattijon yankinku na Neja Delta, Orubebe ya tayar da hayaniya a dai dai lokacin da a ke tattara sakamakon alkaluman jihohi. Shi dole tsagera, amma abun mamaki, ko da ya gama kumfar baki da cije cije hade da zare idanu, sai almajiri Jega ya nuna mishi irin dattijontakan almajiran Arewa, ya kwabe shi, ya yi mishi nasihar da duk duniya sai da a ka jinjinawa wannan salo na Farfesa Attahiru Jega. A cikin ruwan sanyi, ya tsula ma mai kiriniya tsumagiya, ya dawo hayyacinshi.
            Mama ya kamata ki sani har abada mutanen yankin Neja Delta da ‘yan uwan shugaba Goodluck Jonathan, da jikoki da tattaba kunne, har ma da ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP ba za su taba mantawa da wannan mummunan kaye da sakakkun kalamanki su ka janyo musu ba. Yanzu lokaci ne da ya dace ki bi gida gida na ‘yan jam’iyyar PDP masu mafarkin shekara 60 su na mulki, ki basu hakurin harzuka almajirai da ki ka yi su ka kifar da jam’iyyar da ruwan kuri’u. WAHIDI IYA! Mu hadu mako mai zuwa